HOTUNA: Yadda ake shirye-shiryen gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya
Published: 26th, August 2025 GMT
Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya.
A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina.
An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa, shekaru arau-aru.
Mahaya dawaki da sauran mahalarta bikin daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje da mazauna garin Daura sun fara tururuwa zuwa filin bikin, wanda zai samu.
An kuma shirya gudanar da gagarumin hawan daba a Fadar Sarkin Daura, albarkacin zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 10.
A wannan ranar ake cika shekara 10 da fara wannan gagarumin biki, wanda a bana zai gudana a kasashe 26.
Makada da mahaya saura masu sana’o’in gargajiyar Hausawa sun fara kayatar da ’yan kallo da kade-kade da bushe-bushe da sauransu, a wannan kasaitaccen biki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Daura Ranar Hausa Ranar Hausa ta Duniya bikin Ranar Hausa ta Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai October 30, 2025
Manyan Labarai Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar October 30, 2025
Manyan Labarai Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15 October 30, 2025