Sojojin Faransa Sun Mika Sansanin Soji Mafi Girma Da Suka Mamaye Ga Sojojin Faransa
Published: 22nd, February 2025 GMT
Bayan shekaru 47, Faransa ta janye daga sansanin sojinta mafi girma a kasar Ivory Coast
A hukumance Faransa ta mayarwa kasar Ivory Coast babban sansanin soji da ta mamaye kusan shekaru hamsin a kusa da birnin Abidjan, a wani bangare na yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla.
Filin tashar jiragen ruwa na Port Bouet, wanda ke dauke da bataliyar sojoji na 43 da na ruwa, ya shaida bikin mika ta, inda aka daga tutar Ivory Coast a farfajiyar sansanin, kuma an canza sunan ta da sunan babban hafsan soji na farko a Ivory Coast, Thomas Dakine Ouattara, wanda hakan ya kawo karshen kasancewar Faransa a kasar tun shekarar 1978.
Ministan tsaron kasar Ivory Coast, Tene Berahima Ouattara, ya jaddada cewa: Wannan mataki na wakiltar wani sabon mataki na dangantakar abokantaka da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu. A nasa bangaren, ministan tsaron kasar Faransa Sébastien Lecornu ya bayyana cewa: “Duniya tana canjawa, kuma a fili yake cewa dole ne dangantakar kasashen biyu ta bunkasa,” yana mai nuna alfaharinsa ga “dangantakar da aka gina bisa abota da kwarewa tsakanin Faransa da Ivory Coast.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Ivory Coast
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA