Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Ta Fara Tattaunawa, Marhala Ta Biyu Na Tsagaita Wuta A Gaza
Published: 4th, February 2025 GMT
Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna AbdulRazaq Ya Amince Da Naira Biliyan 20 Don Gyaran Gine-ginen Makarantu A Kwara
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati.
Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin.
Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko.
Ta kara da cewa gwamnatin ta gyara sama da ajujuwa 1,254 banda wasu muhimman ayyukan gyara da aka gudanar a wurare daban-daban.
Gwamnatin ta bayyana jin dadinta kan aiwatar da ayyukan gyaran makarantu na SUBEB-UBEC tun daga shekarar 2014.
Sanarwar ta ce wannan sabuwar gudummawar za ta hada da dakunan gwaje-gwaje da wuraren tsafta a makarantun da ke sassa daban-daban na jihar, domin cike gibi tare da kara karfafa ayyukan da SUBEB ke yi.
“Duk da irin manyan ayyukan da muka gudanar, muna sane da cewa har yanzu akwai gibin da ake bukatar cikewa, kuma wannan ne dalilin da ya sa Mai Girma Gwamna ya amince da wannan sabon matakin na musamman don rage gibin da ke cikin gine-ginen makarantu,” In ji sanarwar.
Ali Muhammad Rabi’u