2025-11-04@12:30:48 GMT
				 
				 إجمالي نتائج البحث: 135
				 
                «a zaɓen fid da gwani»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
	Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa zaɓen 2027 zai kasance ne kai tsaye tsakanin Shugaba Bola Tinubu da ’yan Najeriya da gwamnatinsa ta jefa su cikin mawuyacin yanayin rayuwa. Shugaban riƙo na PDP, Umar Damagum, ya jaddada cewa zaɓen “Tsakanin Jam’iyyar APC ne da ’yan Najeriya,” yana mai nuni da wahalar da talakawa ke fuskanta a ƙarƙashin mulkin APC. Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai don magance abin da ya kira “wahalar da aka kawo mana da gangan.” Damagum ya kuma yi tsokaci kan sauya sheƙar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon Gwamna, Ifeanyi Okowa, tare da mambobin majalisar zartarwarsu, zuwa jam’iyyar APC mai mulki. ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa NAJERIYA...
	A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi. HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa fastocin masu ɗauke da saƙon “Kaura for President” an manna su a wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da kuma Ƙofar Dumi. Ɗaya daga cikin matasan da ke aikin manna fastocin, Aminu Auwal, ya shaida wa Aminiya cewa wasu...
	Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf. NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa. “Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa...
	Da alama tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, yana nema karbe kambun ɗaukaka da ’yan siyasa a baya suka riƙa bai wa tsofaffin shugabannin ƙasar nan biyu, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Cif Olusegun Obansanjo, wajen neman tabarrakinsu musamman a lokacin da zabe ya karato a kasar nan. Buharin wanda ya mulki kasar nan a tafarkin soja da kuma na farin hula daga bayabayan nan, a yanzu haka tauraronsa na haskawa, kuma yana ƙamshin turaren Ɗan goma, inda jiga-jigan ’yan siyasa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP da SDP da kuma jam’iyyarsa mai mulki ta APC, suke nikar gari takanas zuwa gidansa da ke birnin Kaduna, tare da nuna irin kyakkyawan kusancinsa da su. Hakan dai na zuwa ne...
	Jam’iyyar adawa ta SDP buƙaci Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin siyasa a Najeriya su dai shagala da batun zaɓen 2027, su mayar da hankalinsu wajen magance matsalar tsaro da ke ƙara mayar da ƙasar tamkar filin kisa. SDP ta bayyana cewa kashe-kashe ɗaruruwan mutane da ke faruwa a faɗin ƙasar nan – Arewa da Kudu – musamman a makonnin da suka gabata, na da matuƙar tayar da hankali. Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na SDP, Araba Rufus Aiyenigba, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a, cewa abubuwan takaicin sun hada da da kisan mafarautan Jihar Kano a jihar Delta, baya ga ayyukan ’yan ta’adda da hare-haren da a ka yi wa mutane sama da 100...
	Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba ta da wani kyakkyawan tsari da za ta iya kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027. Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai kai tsaye a Abuja ranar Juma’a. Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno Daily Trust ta ruwaito cewa, shugabannin adawa a faɗin ƙasar nan na ƙara zage damtse wajen ganin sun ƙulla alaƙa da nufin kawar da Jam’iyyar APC. Sai dai kuma, mabambantan buƙatu tsakanin manyan masu ruwa da tsaki na ci gaba da kawo cikas ga ci gaban tattaunawar ƙawancen da...
	Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi. Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023. A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi. “Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa. Ɗan Atiku Abubakar ya yi...
	A gefe guda kuma, Ganduje ya kafa kwamiti sulhu guda uku don sulhunta rikicin APC a Anambra kafin zaɓen gwamna da za a yi ranar 8 ga watan Nuwamba. Kowanne yankin sanatan jihar — Arewa, Kudu da Tsakiya — yana da mambobi shida da za su yi aiki don haɗa kan ’yan jam’iyyar domin samun nasara a zaɓen.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Wata kotu a Amurka ta umurci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta ƙasar (FBI) da ta fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken badaƙalar miyagun ƙwayoyi da gwamnatin ƙasar ta yi a shekarun 1990. Jaridar Premium Times ta ruwaito Alƙalin kotun, Beryl Howell wanda ya ba da umarnin a ranar Talata, yana mai cewa babu ma’ana a rufe bayanan ba tare da an bayyana wa jama’a ba. ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar A watan Yunin 2023 ce wani Ba’Amurke, Aaron Greenspan, a ƙarƙashin dokar ’yancin fitar da bayanai (FOAI) ya miƙa buƙatar a ofishin zartarwa...
	“Abin da ke da tabbas shi ne cewa ‘yan Nijeriya ba za su iya yin rufa-rufa ba ta kowace hanya don boye gazawarka da wahalar da suke ciki har su sake jefa maka kuri’unsu a babban birnin tarayya Abuja da kuma zaben 2027,” in ji shi.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Jam’iyyar APC, ta musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na shirin sauya Mataimakinsa, Kashim Shettima, kafin zaɓen 2027. Jam’iyyar ta ce babu wata matsala tsakaninsu kuma maganar sauya Shettima ba ta da tushe. Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Bala Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa wasu ne ke yaɗa wannan jita-jitar don tayar da ƙura. “Wannan jita-jita ce kawai marar tushe. Maganganu ne da bai kamata a ɗauke su da muhimmanci ba,” in ji shi. Ya ƙara da cewa, “Ko da a ce akwai wani dalili da zai sa shugaban ƙasa ya sauya mataimakinsa, ba zai iya yin hakan...
	Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe wa’adi na biyu a zaɓen 2027. Ya yi wannan jawabi ne domin mayar da martani ga sabuwar haɗakar ’yan adawa da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da wasu shugabanni suka kafa. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas A yayin taron manema labarai da Atiku ya gudanar a Abuja a ranar Alhamis, ya soki yadda Tinubu ke tafiyar da mulki, musamman batun ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas. Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka...
	Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya yi ganawar sirri da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. Taron ya gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, sai dai ba a bayyana manufar taron ba. Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja Obi ya isa Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tarbe shi. Rahotanni sun nuna cewa Obi da Gwamna Mohammed sun tattauna wasu batutuwa da suka shafi babban zaɓen 2027 da kuma makomar siyasarsu. Wannan ganawa ta wakana ne a daidai lokacin da ’yan siyasa...
	Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, na ganawar sirri da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi. Taron na gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, amma ba a bayyana manufarsa ba tukuna. Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja Obi ya isa Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tarbe shi. Rahotanni sun nuna cewa Obi da Gwamna Mohammed za su yi magana da ’yan jarida bayan kammala ganawar tasu. Wannan ganawa na faruwa ne a daidai lokacin da ’yan siyasa ke shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027....
	Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi. “Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha. Tun...
	Iyalan marigayi Janar Sani Abacha, sun gargaɗi Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, da ya daina faɗin maganganun da ka iya ɓata sunan mahaifinsu. A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha, ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi, sun musanta iƙirarin da Babangida ya yi a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’. Ramadan: Ali JC ya bai wa jama’a tallafin kayan abinci a Gombe An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba Ya ce Janar Abacha ne, ya ke da alhakin soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga wata Yunin 1993. “Duk wani yunƙuri na ɗora wa Janar Sani Abacha laifin soke zaɓen, wanda a lokacin ya kasance babban jami’in soja a mulkin...
	Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Neja ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi. Shugaban Hukumar Zaɓen, Mohammed Jibrin Iman ne ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da jadawalin ayyukan gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2025 a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban birnin jihar. Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 Gwamnatin Ogun ta rufe kamfanoni saboda mutuwar ma’aikata Imam ya ce an fara shirye-shiryen zaɓen ne daga ranar 6 ga watan Maris, 2025, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu ne tsakanin ranakun 15 zuwa 24 ga Maris, 2025, yayin da za a tattara fom da kuma jerin...
	Hukumar zaɓen ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su shirya don shiga zaɓen da ke tafe, tare da tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin zaɓe. Haka kuma, hukumar ta yi alƙawarin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa an zaɓi shugabannin da suka cancanta a matakin ƙananan hukumomi.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Ƙaramin Ministan Gidaje da Tsara Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa ɗan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a Zaɓen 2023 Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara. Sai dai Ministan ya ce ƙaddarar hukunci daga Allah ne ya sanya a yanzu haka ba shi ke riƙe da madafan iko a Jihar Kanon ba. Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Ata ya faɗi hakan ne yayin da yake barazanar ficewa daga jam’iyyar APC muddin ake sake naɗa Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano. Ministan ya ce kalaman da shugaban jam’iyyar ya riƙa furtawa su ne dalilin da Allah Ya ƙwace mulkin jihar...
	Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa. Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar, ya samu fitowar masu zaɓe sosai tare da ingantaccen tsaro. Gwamna Adeleke ya yaba da yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko matsin lamba ba. Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke An Yanke Wa Mutane 5 Hukuncin Kisa Bayan Sun Kashe Wani Bafullatani A Jihar Osun Da yake jawabi...
	Sadiq S. Abacha, ɗan Tsohon Shugaban Mulkin Soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana mahaifinsa s matsayin mutum mai nagarta duk da sukar da ake yi masa har yanzu. A wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Sadiq, ya ce an jima ana cin amanar mahaifinsa, amma tarihi zai yanke masa hukunci ta hanyar yin adalci. Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa “Mutumin nan Abacha—kullum sukarsa da cin amanarsa kuke yi a asirce. Tarihi zai tuna ka a matsayin shugaba nagari, ko da kuwa sun ci gaba da ƙoƙarin rage maka ƙima. “A matsayina na ɗanka, yau na fi alfahari da kai. Lallai kai...
	Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya ce ya sha alwashin cewa zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar a gobe Asabar zai gudana kamar yadda aka tsara. Gwamnan ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan shawarar da ministan shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi, wanda ya buƙaci gwamnatin jihar ta dakatar da yunƙurin yin sabon zaɓen ƙananan hukumomi. Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, Ministan ya ce kotu ta dawo da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin da aka zaɓa a ƙarƙashin tsohon Gwamna Gboyega Oyetola, amma ta tsige su ta hanyar umarnin zartarwa da gwamnan...
	Tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce ya yi nadamar soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993. Ya ce da zai samu wata dama da zai yanke wani hukunci daban. Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Majalisa ta fara bincike kan zargin USAID na tallafa wa Boko Haram Babangida ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Service’. Yayin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ke nazarin littafin, Babangida ya amsa alhakin soke zaɓen da aka gudanar tsakanin Moshood Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Bashir Tofa na jam’iyyar...
	Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin zaɓe da ya binciki Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC dangane da jinkirin da take yi na gudanar da zaɓen cike giɓin wasu kujerun ’yan majalisar tarayya da na jihohi. Majalisar a wannan Talatar ta kuma bayyana cewa jazaman ne kwamitin ya gayyaci Hukumar INEC domin ta bayar da dalilai kan tsaikon da aka samu da kuma yadda take ƙoƙarin yi wa tufkar hanci. Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara Da wahala City ta yi nasara a gidan Madrid — Guardiola Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar ta buƙaci kwamitin ya sauke wannan nauyi tare da miƙa mata rahoton bincikensa nan da makonni huɗu. Wannan dai na zuwa ne bayan ƙorafin da wani...
	Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, ya zargi malaman addini da neman ƙwace lamurran siyasar Najeriya daga hannun ’yan siyasa. Sule Lamiɗo ya nuna damuwa bisa yadda malaman addini ke ƙara shiga harkokin siyasa, inda ya ce, a halin yanzu malaman suna yin tasiri sosai a yanayin tafiyar siyasa da kuma jefa ƙuri’a. Ya bayyana haka ne a yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum, bisa rasuwar babban ɗansa a Jihar Kaduna. A cikin bidiyon ta’aziyyar, an ji Sule Lamiɗo, yana cewa, malaman addini sun yi wa ’yan siyasa ƙwace, inda suke fitowa fili suna yi wa ’yan takara yaƙin neman zaɓe, tare da kiran mabiyansu su zaɓi wanda su suke goyon baya....
	Hukumar Zaɓe Mai ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda  gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki. Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula da ofishin...
	Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda  gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki. Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula...
	Kamar yadda doka ta tanada cewar duk wata ƙaramar hukumar a tabbatar da cewa zaɓaɓɓun shugabanni ne ke jagorancin ta. Wannan ya sa Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Raɗɗa ta shirya aiwatar da zaɓen ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jahar wanda hakan zai ƙara ba su damar cin gashin kan su kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Shugaban Ƙungiyar Afenifere, Adebanjo ya rasu Kamar yadda shugaban Hukumar zaɓen mai zaman kanta ta Jihar Alhaji Lawal Alhassan Faskari ya shaidawa manema labarai a lokacin da ake rarraba kayan zaɓen zuwa ƙananan hukumomin jihar ya ce, tuni hukumar zaɓen ta kammala duk wasu shirye-shirye don...
	Alhaji Ahmad Haruna Zago da aka fi sani da Ɗan zago, gogaggen ɗan siyasa ne da ya fara siyasa tun a Jamhuriya ta biyu.  Bayan dawowar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999, ya shiga Jam’iyyar APP, inda ya kasance na gaba-gaba a tafiyar siyasar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki ɗaya. Yana daga cikin waɗanda suka jawo Muhammadu Buhari shiga cikin harkokin siyasa. 2003. Gabanin zaɓen 2003, Alhaji Ahmadu Haruna zago ya taka rawa a tunja-tunjar da ta biyo bayan zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APP, da ta kai ga karɓe takarar gwamna daga hannun tsohon shugaban jam’iyyar, Ibrahim Al’amin Little, aka bai wa Malam Ibrahim Shekarau. 2007 Sai dai tun ba a je ko’ina ba,...
	Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas.  Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya. Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke kira ga haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027. A watan Oktoban 2024, jam’iyyar APC a Jihar Osun ya dakatar da Aregbesola bisa zargin cin amanar jam’iyya da sukar shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan...
	Tsohon Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Ari, ya ce bai damu da korar da aka yi masa ba, amma yana nan a kan bakansa cewa Aisha Binani ta jam’iyyar APC ce, ta lashe zaɓen gwamna na 2023. An dakatar da Hudu Ari bayan da ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun kafin a kammala tattara sakamakon ƙuri’u. Gobara ta ƙone motoci da shaguna a wajen sayar da gas a Neja Taron Qur’ani: Tsakanin magoya baya da masu kushe Sai dai ya ce yana da hujjojin da ke nuna cewa Binani ta doke Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP. Da yake magana da manema labarai a Bauchi, Ari ya rantse da Alƙur’ani mai girma cewa manyan jami’an...
	LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu.   Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen.   Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da...
	Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
	Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun ce sun ƙwato tarin makamai a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda na Jihar Zamfara. Dakarun tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (DSS), sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya. Tankar mai ta sake fashewa a Neja Jadawalin Gasar AFCON 2025 da za a fafata a Morocco Wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce sun ƙaddamar da farmaki ranar 27 ga watan Janairun 2025, abin da ya kai ga ƙwato makaman kan hanyar Namoda zuwa Zurmi. Ya ce waɗanda ake zargin sun tsere zuwa cikin daji tare da barin motarsu bayan artabu da sojoji. Kanal Abubakar ya...
