Seaman Abbas da Hussaina: An dakatar da shirin Brekete Family Hausa
Published: 31st, January 2025 GMT
Rikici ya ɓarke tsakanin Seaman Abbas da matarsa Hussaina, da kuma mai gabatar da shirin nan na Brekete Family, Ahmad Isa da aka fi sani da Ordinary President.
Rikicin ya fara ne bayan Hussaina ta fitar da wani bidiyo tana cewa mijinta na yi mata duka, saboda zargin ta da yake da sama da faɗi da wasu kuɗaɗe da mota da aka ba su a matsayin tallafi.
A bidiyon ta kuma bayyana cewa tsangwamar ba ga iya shi ta tsaya ba, har na danginsa, abin da ta ce ya yi sanadiyar komawarta gidan iyayenta.
To sai dai mijin nata ya fito ya musanta zarge-zargen, inda ya ce suna zaune lafiya, hasali ma ta je ganin gida ne bayan rashin lafiyar da ta yi.
An ɗaure zawarawa a gidan yari kan aikata zina Tubabbun ’yan Boko Haram 5,000 sun koma cikin jama’aShi ma dai Ordinary President da ake zargin ya hana su Seaman ɗin tallafin Naira Miliyan 20 da Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya ba su, ya ce zance ne mara tushe balle makama.
Ya bayyana cewa a sakamakon waɗannan rikice-rikicen da suke ɓullowa a lamarin Usaina, ya daina gabatar da shirin Brekete Family da harshen Hausa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar nuna goyan baya ga wani kudiri da ya jaddada cewa shirin da Morocco ta gabatar kan Yammacin Sahara shi ne mafita ‘’mafi dacewa” ga yankin da ake takaddama a kai.
Kudirin ya nuna goyan bayan kasashe mambobin kwammitin ga shirin na Morocco, tare da bayyana cewa ikon masarautar kan yankin zai iya kasancewa mafita mafi dacewa.
Kan hakan ne kwamitin yaya kira ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da wakilinsa na musamman kan wannan batu, Staffan de Mistura, da su gudanar da tattaunawa “bisa ga” wannan shirin don cimma yarjejeniya da kowa zai aminta da ita.
Aljeriya wacce ta ke kaddama da Morocco kan yankin ta kaurace kada kuri’an kan batun inda ta bayyana matukar adawarta da kudirin.
Jakadan Aljeriya, Amar Benjama, ya ce kudirin bai dace da burin mutanen Yammacin Sahara, wadanda kungiyar Polisario ke wakilta ba.
Kudurin da aka amince da shi a ranar Juma’a ya kuma tsawaita aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Yammacin Sahara (MINURSO) na tsawon shekara guda.
Shirin wanda Rabat ta gabatar a ranar 11 ga Afrilu, 2007, don mayar da martani ga kiran da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi na samar da mafita ta siyasa game da yankin na yammacin Sahara.
Kudirin na yanzu ya tanadi samar da gwamnati da shugaban yankin, da majalisar dokoki wadda ta kunshi wakilan kabilun Sahrawi daban-daban da membobi da aka zaba ta hanyar zaben gama gari kai tsaye.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci