2025-07-03@13:08:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 276
«Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello»:
Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu. Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI. Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin...
Tsangayar Kwalejin koyar da aikin Jinya ta Jihar Jigawa dake garin Birnin kudu ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin dalibai 116 da za su yi karatun difloma ta kasa da babbar difloma ta kasa karon farko na shekarar karatu ta 2024 zuwa 2025. A jawabinsa wajen taron kaddamar da daliban, kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar Jigawa Dr. Muhammad Abdullahi Kainuwa, ya ce aikin sa na farko daga samun wannan mukami shi ne batun kafa hukumar Gudanarwar Kwalejin da sake fasalin Kwalejin, wanda hakan ya bada damar tantancewa da kuma samun amincewar Cibiyar kula da makarantun aikin Jinya ta Najeriya. Yana mai cewar, daukar wannan mataki ya bada damar kara yawan dalibai da Kwalejin take dauka daga 120 zuwa 240,...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 30 da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa a Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa. Kakakin ’yan sandan Jigawa, SP Lawan Shi’isu, ya ce matashin mai suna Hussaini Abubakar ana zargin ya kashe mahaifiyarsa, Dahara Mu’azu mai shekaru 75 da misalin karfe 8 na yammacin ranar 29 ga watan Yunin 2025. Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina SP Shiisu ya ce matashin ya jikkata mahaifiyarsa da bulon ƙasa, kuma bayan an garzaya da ita asibiti ta mutu washegari. Ya ce wannan lamari ya sanya rundunar ta gaggauta tura tawagar jami’ai kuma aka cafke matashi da a...
Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bukaci a sake komawa teburin tattauna shirin nukiliyar Iran cikin gaggawa, inda take neman hadin kai a tsakanin Tehran da kuma Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya IAEA. Babbar jami’ar diflomasiyyar EU Kaja Kallas ta shaida wa Ministan Harkokin Kasashen Ketare na Iran, Abbas Aragchi cewar Brussels a shirye take ta shige gaba don ganin an koma teburin tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran bayan hare-haren Amurka a tashoshin makamashinsu. HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza Bayan wata doguwar tattaunawa ta wayar tarho da jami’ar ta yi da Mista Argchi, ta wallafa a shafinta na X cewar ya kamata a koma tattaunawa...
Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana. Lardin Guizhou da wasu larduna masu iyaka da shi da ke kudu maso yammacin kasar Sin sun fuskanci mamakon ruwan sama tun daga ranar 18 ga watan Yuni, lamarin da ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa, inda lamarin ya fi muni a yankin Rongjiang. Mahukuntan yankin sun raba yankin zuwa kashi bakwai a matsayin wadanda ambaliyar ta fi shafa tare da kwashe mazauna zuwa wasu manyan wurare masu...
Kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce kasarsa na adawa da duk wata yarjejeniyar yafe haraji da Amurka za ta kulla da wata kasa, wadda ka iya illata moriyar Sin, tare da baiwa kasar da aka kulla yarjejeniyar damar samun yafiyar haraji daga Amurka. Kakakin wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar, lokacin da yake amsa tambayar da manema labarai suka yi masa, dangane da tattaunawar cinikayya da Amurka ta yi tare da wasu kasashe, ya ce, idan an samu aukuwar irin wannan yanayi, kasar Sin ba za nade hannu ba, za ta dauki matakai na martani domin kare halastattun hakkoki da moriyarta. Jami’in ya kara da cewa, tun watan Afrilun da ya gabata, Amurka ke ta ingiza matakan...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Hizbullah ta mika makamanta a cikin wannan lokacin da yaki bai kare ba, kuma HKI tana cigaba da keta tsagaita wutar yaki. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya bayyana masu tunani irin wannan da rashin Sanya hankali a cikinsa. A jawabinsa na dararen Muharram a jiya Asabar, babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Nauyi ne da ya rataya a wuya gwamantin kasar ta takawa HKI birki akan keta tsagaita da take yi wanda take kai wa fararen hula hare-hare.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Babu yadda za a yi Hizbullah ta ci gaba da Sanya idanu ba tare da iyaka ba, domin...
Yau Asabar, kwamitin kula da raya kasa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC), ta ce ta ware yuan miliyan 100, kwatankwacin dala miliyan 13.95, kari kan yuan miliyan 100 da ta ware a ranar Larabar da ta gabata, domin taimaka wa ayyukan agaji a kudu maso yammacin Sin. Mummunar ambaliyar ruwa ta sake dawowa a gundumar Rongjiang ta lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, lamarin da ya sanya hukumomin wurin sake ayyana matakin koli na tunkarar ambaliya, daga karfe 12:30 na rana a yau. Hukumomi a yankin na kwashe mazauna daga wuraren da lamarin ya shafa. Zuwa karfe 6 na yamma, gundumar ta tsara aikin gaggawa na kwashewa tare da tsugunar da iyalai 11,992 da daidaikun...
Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya sa ake samun jituwa a tsakanin al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Saboda haka, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi, a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai-daya, inda za a dinga rage gibin dake tsakanin kasashe, da na zaman rayuwar al’ummu daban daban, ta yadda za a iya daidaita matsalolin da dan Adam ke...
Dan wasan mai shekaru 40 ya zura kwallaye 93 sannan ya taimaka wajen zura 19 a wasanni 105 da ya buga a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar ta Saudiyya, amma har yanzu bai samu nasarar lashe kofi a gasar ba, a kakar wasan da aka kammala kwanan nan, Al Nassr ta kare a matsayi na uku a teburin, inda ta rasa gurbi a gasar cin kofin zakarun yankin Asia na shekara mai zuwa kuma a maimakon haka za ta buga gasar AFC Champions League 2. Bugu da kari, Al Nassr a halin yanzu ba ta da koci tun bayan da ta raba gari da babban kocinta Stefano Pioli a ranar Laraba, wanda ya zama koci na uku...

Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Rumbun Sauki Don Sayar Wa Ma’aikata Kayayyakin Abinci A Farashi Mai Rahusa A Sakkwato
Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wakilan ƙasarsa za su gana da na Iran domin ci gaba da tattaunawa kan makaman nukiliyarta a mako mai zuwa. “Za mu tattauna da Iran a mako mai zuwa, ƙila mu ƙulla yarjejeniya ko kuma akasin haka, ba na ce ba,” in ji shi yayin jawabinsa a taron ƙasashe na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO da ake yi a ƙasar Netherlands. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 2, sun kama wasu a Kaduna An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano “Ba su daɗe da gama yaƙi ba, yanzu za su ci gaba da harkokinsu. Ban damu dole sai na ƙulla wata yarjejeniya da su ba,” a cewarsa. A jiya Talata...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron koli na kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu. A cikin jawabinsa, Xi ya ce, yayin da kasar Sin da kasashe biyar na yankin tsakiyar Asiya ke tafiya kan hanyar samun ci gaba a cikin dogon lokaci, sun kafa “Ruhin Sin da kasashen tsakiyar Asiya” na “Mutunta juna, da amincewa da juna, da moriyar juna, da taimakon juna, da inganta zamanantarwa tare ta hanyar samun ci gaba mai inganci”. Yayin da ya ambaci yanayin rashin kwanciyar hankali da duniya ke fama da shi, ya ce ta hanyar tabbatar da adalci ne za a iya cimma burin kare zaman lafiya, da samun ci...
Iran ta zartar da hukuncin kisa kan jami’an leken asirin Hukumar leken asirin yahudawan sahayoniyya “Mossad” a safiyar yau Litinin A wani gagarumin farmaki da aka kai kan cibiyar leken asirin yahudawan sahayoniyya a cikin kasar Iran, an kama wani mutum tare da yi masa shari’a bisa zargin hadin kai da hukumar leken asirin ‘yan sahayoniyya, bisa tuhumarsa a matsayin maci amana da gudanar da barna a kan doron kasa. An zartar da hukuncin ne bayan kammala shari’ar laifuka da kuma tabbatar da hukuncin da kotun koli ta yanke. A cikin wani hadadden aikin fasaha da leken asiri a cikin kasar, an kama Isma’il Fakri a watan Disamban shekara ta 2023 yayin da yake da alaka da hukumar leken asiri...
Ba tare da saninmu ba, yawancin al’ummar Afirka musamman ma naYammacin Afirka suna fama da abinda ake kira da suna irin hali ko yanayin da aka shiga sanadiyar lamarin cinikin Bayi.Bayan shekara 100 da aka yi daga shekarar 1801 zuwa 1901, an yi wani kokarin da ake yi ma kallon tamkar wani takune na yadda za’a kubuta daga irin cin fuskar da ake yi kowace rana. Kafin dai a tsunduma sosai cikin lamarin cinikin Bayi, yana da matukar kyau a fara yin bayani kan yadda abin ya fara:Lamarin cinikin Bayi ba manufa bace ta Yammacin Turai.Duk lamarin ya zarce wani hasashen da za’a iya yi ko wani rubutun,da aka yi aka aje.Idan kuma aka duba ta bangaren nahiyar Afirka ita...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bude kofofin wuta a kan haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar mayar da martani kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasarta Iran ta bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya a matsayin mayar da martani ga mummunan zaluncin da suka kaddamar kan lardunan Iran da dama, wanda ya yi sanadiyyar shahadan mutane da dama da jikkata. Bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Wajibi ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta jira mummunan hukunci mai tsanani da kuma makoma mai daci kan abin da aikata, kuma bayan da sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Muhammad Pakpour ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran za su bude kofofin...
Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kakkausan martanin da Iran ta mayar ya tabbatar da cewa babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani ba Izzat al-Rishq mamba na ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa: Kakkausan martanin da Iraniyawa suka mayar ya tabbatar da cewa; babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani kan zaluncinsa ba, kuma babu wuce gona da iri ba tare da hukunci ba. Izzat al-Rishq ya yi nuni da cewa: Tabbas makamai masu linzami da jiragen saman yaki marasa matuka ciki na Iran sun yi nasarar kai wa cikin tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila, duk kuwa da kace-nacen da ake yi na girke na’urorin kakkabo makamai...
Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa. Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium da ɗage takunkumai na iya sa tattaunawar ta yi amfani Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta cewa: A bayyane yake cewa cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya na dindindin na shirin makamashin nukiliyar Iran abu ne mai yiyuwa, kuma ana iya cimma shi cikin sauri. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta a shafinsa na Twitter game da sabon zagayen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka da kuma matsayin Iran a kansu yana mai cewa: Shugaba Trump ya bayyana a lokacin da ya shiga fadar White House cewa ba lallai ne Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, wannan matsayi ya yi daidai da akidar Iran...

He Lifeng Ya Bukaci Amurka Da Ta Warware Takaddamar Cinikayya Da Sin Ta Hanyar Tattaunawa Da Hadin Gwiwa
Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya bukaci Amurka da ta warware takaddamar cinikayya da Sin ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa da zai iya haifar da moriyar bai daya. He, ya ce Sin na jaddada burin ganin Amurka ta yi aiki da bangaren Sin, ta yadda za a martaba alkawura da matakai da aka amince, da nuna sahihanci wajen yin aiki tukuru, da aiwatar da gaskiya da kwazo wajen aiwatar da matsayar da aka cimma, ta yadda za a kai ga kare nasarorin da aka cimma ta hanyar shawarwari. He, ya yi tsokacin ne yayin taron farko na shawarwari game da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda ya gudana a ranakun Litinin da Talata a birnin...
Iran ta ce za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a Muscat, babban birnin kasar Oman. Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai a wata sanarwa da ya fitar ya ce “An shirya zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a birnin Muscat.” Tun a watan Afrilu, Tehran da Washington ke gudanar da shawarwarin kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. An yi shawarwari guda uku a tsakanin kasashen biyu a birnin Muscat, yayin da sauran biyun suka gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya. Tehran da Washington sun gudanar da wadannan zagaye biyar na shawarwarin a shiga tsakanin kasar Oman, kan batun maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar...

Jami’in Makamashin Nukiyar Iran Ya Ce; Zarge-Zargen Da Ake Yi Kan Shirin Makmashin Nukiliyar Iran Siyasa Ce Kawai
Jami’in makamashin nukiliyar Iran ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi wa Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, siyasa ne tsantsa Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: Zargin da ake yi wa Iran game da batun Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya, tsagwaron siyasa ne, ba bisa ka’ida ko na fasaha ba. Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya kara da cewa: Kudurorin da suka biyo baya da kuma kara matsin lamba a kan Iran suna share fagen fuskantar al’amura a nan gaba. Yayin da yake ishara da cikas iri-iri da ke kawo sarkakiya ga ci gaban shirin makamashin nukiliyar Iran, Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa: Wadannan kalubalen da suka kara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun...
Tare da cewa giwaye suna cikin dabbobin da masu yawon bude ido suke son gani, said ai gwamantin kasar Zimbabwe ta yanke hukunci yanka 50 daga cikinsu domin rabawa mutanen karkara namansu. Wannan matakin na gwamnatin Zimbabwe ya zo ne saboda yadda giwayen suke kara yawa sosai a cikin shekarun bayannan. Haka nan kuma wuraren da ake killace su, sun yi kadan. Majiyar dake kula da gandun dajin kasar ta ce; adadin giwayen ya rubanya har sau uku, wannan ne ya sa mahukuntar kasar su ka yanke shawarar yanka 50 daga cikinsu saboda a rabawa mutanen karkara. A baya gwamnatin na Zimbabwe ya yi kokarin warware matsalar karuwar dabbobin ta hanyar sauya musu gandun daji da wuraren da aka killace...
Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa ya yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI suka kai kan zirin gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Asa’d Abu Sharia shi ne baban sakataren kungiyar ‘Dakarun Palastinewa”. Wacce aka kafa a shekara ta 2001 M. Kungiyar kanta ta tabbatar da wannan labarin ta kuma bayyana cewa ya dade yana shugabantar wannan kungiyar sannan a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya shiga cikin yakin da aka fara kan HKI kuma dakarunsa sun kama yahudawa da dama suka shigo da su su gaza. Banda haka shi ne yake jagorantar bangaren soje na kungiyarsa. Sau da dama ya jagoranci Falasdinawa a yaki da yahudawan a Gaza. Sannan kungiyar tana...
Kasar Ghana ta kawo karshen goyon bayan da take bawa kungiyar Polisario, sannan ta dawo tana goyon bayan kasar Morocco a kan wannan rikicin. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa, an kafa kungiyar Polisario ne a shekara 1979. Sannan rikicin Polisario yana komawa zuwa shekara 1975 a lokacinda turawan Espania yan mulkin mallaka suka fice daga yankin sai suka hadda fada tsakanin Polisario da kasashen Morocco da kuma Mauritania. Kungiyar dai tana samun goyon bayan kasashe kimani 80 a duniya, amma kuma a hankali-a hankali tana rasa goyon bayan da take da samu a duniya, na karshensu it ace kasar Ghana.

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
CGTN ta wallafa nazarin ne a dandamalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci. Kuma mutane 5610 ne suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 12. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Abu Ubaida kakakn dakarun Ezzuddeen Al-Qassam reshen soje na kungiyar Hamasa ya bayyana cewa dakarunsa zasu ci gaba da Yakar sojojin yahudawa har zuwa korarsu daga yankin zirin Gaza. Abu Ubaida ya kara nda cewa, dakarun Hamas suna a madaka ga sojojin HKI babu jada baya babu janyewa daga matsayinsu. Kafin haka dai a jiya Jumma’a dakarun na Hamas tare da hadin guiwa da na Saraya Qudus sun aiwatar da wani shiri ko tarko kan sojojin yahudawan wanda ya sami nasara halaka sojojin yahudawa da dam. Majiyar yahudawan sun tabbatar da aukuwar hare-haren na Khan Yunus dake kudancin Gaza, wanda kuma ya halaka yahufawa da dama., Abu ubaida ya kammala da cewa aikin soje da suka yi a Khan Yunus...
Shugabannin nahiyar Afirka sun tattauna hanyoyin samar da maganin kwalara a cikin nahiyar. An tattauna wannan batun ne dai a yayin taron da aka yi ta hanyar bidiyo daga nesa akan hanyoyin magance cutuka mabanbanta da su ka hada da riga-kafi. Wadanda su ka halarci tattaunawar ta bidiyo sun hada shugabannin kasashen Angola, Namibia, Malawi da kuma DRC. Shugaban kasar Zambia Hakayinde Hichilema ya bayyana cewa; Da akwai bukatar nahiyar Afirka ta fara samar da magunguna cikin gaggawa tare da dogaro da nahiyar wajen samar da kudaden da ake bukata domin yin hakan, saboda kaucewa dogaro da waje.” Haka nan kuma shugaban kasar ta Zambia ya ce: Saboda kwalara idan ta barke ba ta san iyakar kasashe ba, ya kamata...
Gidauniyar ta kuma kai ziyara fadar Hakimin Mokwa, Alhaji Muhammed Aliyu Shaaba, inda wakilan fadar suka yi maraba da tawagar wakilan gidauniyar tare da jinjina taimako da goyon bayan da aka nuna musu a wannan hali da suke ciki na ibtila’i. Kamar yadda Babban daraktan yankin, Musa Aliyu ya bayyana, gidauniyar Dr. Abubakar Bukola Saraki ta kai taimakon kuɗi domin tallafawa waɗanda suka tsira da masu taimaka musu. Sannan ya yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da ɗaiɗaikun mutane da su taimakawa al’ummar garin Mokwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake tabbatar da cewa Iran ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba kan ‘yancinta na tace Uranium, yana mai cewa ci gaban da kasar ta samu a fannin makamashin nukiliya ya samo asali ne sakamakon sadaukarwa da kuma saka hannun jari na kasa. A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya ce, ba batun inganta makamashin Uranium a duk wata yarjejeniyar nukiliya da za a yi nan gaba. “Iran ta saka kudi da yawa domin kai wag a wannan mataki, sannan kuma ba zai sa mu yi watsi da sadaukarwar da ‘yan kishin kasa sukayi don tabbatar da burinmu. Araghchi ya bayyana tace...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama daya daga cikin masu kamfanin Microsoft, Bill Gates, da lambar girmamawa ta kasa — Commander of the Order of the Federal Republic (CFR), inda ya jaddada cewa Gates ya kasance abin koyi ga shugabanni a fadin duniya saboda yadda yake taimaka wa talakawa da masu bukata ta musamman. Shugaban ya kuma bayyana cewa Mista Gates, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Melinda da Gates, ya bada gudummawa a fannonin kiwon lafiyar mata, noma da bincike kan cututtuka masu yaduwa. Ya gode wa Bill Gates bisa gudummawar da yake bayarwa a duniya, musamman wajen saukaka rayuwa da kare lafiyar masu rauni da wadanda ke cikin bukata. Ministan Lafiya da Ci gaban Jama’a, Farfesa Ali Pate,...

Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Na Da’awar Mallakar Wasu Yankunan Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Tsibiran guda uku na Tunb Babba da Tunb Karami da Abu Musa yankuna ne Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirari da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGCC) ta yi dangane da tsibiran Iran guda uku, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da muradun kasar a cikin tsibiran guda uku. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da yin watsi da ikirarin da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron ministocin harkokin wajen kasashen yankin tekun Fasha karo na...
Rikici tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar yana ci gaba da habaka a wurare da dama na kasar Kasar Sudan dai na fuskantar tabarbarewar harkokin tsaro cikin hanzari, a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF), a cikin sarkakkiyar yanayin jin kai da na siyasa da kuma fadadan rikici a jihohi daban-daban. Fadace-fadace a Sudan suna ci gaba da karuwa, inda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan kungiyar Rapid Support Forces, inda sojojin saman Sudan suka zafafa kai hare-hare ta sama ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki, kuma suka yi luguden wuta kan wasu muhimman...
Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta bayyana ambaliyar ruwa mai tsanani da ta faru a Mokwa, Jihar Neja, a matsayin babbar ibtila’i, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa don tallafi da hana sake faruwar hakan. Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana haka a yayin mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja kan ambaliyar da ta faru a ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2025, sakamakon ruwan sama mai kamar da bakin ƙwarya da ya yi sanadin rasa rayuka, bacewar mutane, da lalacewar gidaje, gonaki, da kayan more rayuwa. Ya yaba da agajin gaggawa daga Gwamnatin Jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago da kuma kokarin hukumomin agaji wajen aikin ceto da tallafa wa...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza ta bukaci masu shiga tsakanin Amurkawa su ngamtar da ita kan cewa HKI zata dakatar da yaki ta kuma fice daga zirin gaza. Amma shawarar da Steve Witkoff ya gabatar bata kunshi wani abu wanda zaia gamsar da kungiyar ta amince da wani sulhu ba. Jihad Taha kakakin kungiyar ya bayyana cewa Hamas tana nazarin shawarar da Witskoff ya gabatar da tsagaita wuta a gaza wanda ya amince da dakatar da wuta na wucin gadi sannan a sake komawa yaki da kuma shigo a kayakin agaji. Y ace shawarar bata ambaci ficewar sojojin HKI daga yankin ba. Taha ya bayyana cewa shawarar bata da wani abin dogaro wanda Hamas da kungiyoyin masu...
Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen. Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen cewa: Kariyar tsaron sararin samaniyar sojojin Yemen za ta mayar da jirgin saman makiya ‘yan sahayoniyya abin izgili a cikin kwanaki masu zuwa. Al-Mashat ya jaddada cewa: Sojojin kasar Yemen za su iya tunkarar jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya ba tare da haifar da wata illa ga...
Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga barazanar shugaban kasar Amurka kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran Ali Shamkhani mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci a fagen siyasa ya jaddada cewa: Iran kasa ce mai cin gashin kanta mai tsayayyen tsarin tsaro, al’umma masu tsayin daka, da jajayen layi. Ya jaddada cewa, “tattaunawa hanya ce ta ci gaba da kuma kiyaye moriyar kasa da mutunci, ba kayan aiki na tilastawa ko mika wuya ba.” Shamkhani ya rubuta a shafinsa na dandalin X cewa: “Burin isa ga cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma ‘tarwatsa su’ ba komai ba ne illa mafarki da shugabannin Amurka da suka gabata sun kasance sun yi has ashen hakan. Ya...
Shugaban kwamitin kungiyar Tarayyar Afrika (AU) Mahmoud Ali Youssouf, ya nanata godiyar kungiyar bisa irin goyon bayan da kasar Sin ke ba ta da ma kasashen Afrika a muhimman bangarori kamar na cinikayya da raya ababen more rayuwa da aikin gona da kiwon lafiya da bunkasa kwarewar jami’ai. Wata sanarwa da aka fitar jiya Laraba, ta ruwaito Mahmoud Ali Youssouf na bayyana haka ne yayin da yake bankwana da Hu Changchun, shugaban tawagar kasar Sin a AU. Shugaban na kwamitin AU ya kuma yaba wa jajircewar Hu tare da gode wa kasar Sin dangane da gudunmuwar da ta bayar na gina Cibiyar Kandagarki da Dakile Yaduwar Cututtuka ta Afrika, da taimakonta ga aikin wanzar da zaman lafiya da sauran taimakon...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa; Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai yi tasiri akan matsayarmu ta taimakawa Gaza ba,sannan kuma ya kara da cewa; Abinda Isra’ila makiya ke son yi, shi ne a kyale ta yi yadda take so da Falasdinawa ba tare da an mayar mata da martani ba daga kowace kasa ta musulmi.” Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Matsayar da kasar Yemen take dauka na taimakawa Falasdinawa, matsaya ce ta addini.” Haka...
Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin cika shekara 71 da aka gudanar a filin faretin RSM Zakari Kumasi dake harabar makarantar a zaria. Shugaban rundunar mayakan saman ya bayyana cewa makarantar ta NMS ta yi fice wajen baiwa yara horo a fannonin karatu da kuma ilimin aikin soja wanda hakan ya sa ta samar da manyan sojoji da dama har ma da shi a ciki. Air Marshal Abubakar ya ce bukin...
A cikin wani mataki na ci gaba da sauya fasalin bangarorin noma da kiwo, Gwamnatin Jihar Jigawa na shirin kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da daya daga cikin manyan kamfanonin kiwon kaji na kasar Indiya, wato Srinivasa Farms. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar. Ya ce a wani bangare na ziyarar zuba jari a fannin noma da gwamnatin jihar ke gudanarwa zuwa kasar Indiya, tawagar jihar karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi ta kai ziyara ofishin babban kamfanin Srinivasa Farms dake birnin Hyderabad domin tattauna damar hadin gwiwa da nufin farfado da harkar kiwon kaji a Jigawa. Hamisu Mohammed Gumel ya kara da cewa...
Falasdinawa da dama ne suka ji rauni a jiya Talata a lokacinda yahudawan Sahyoniyya suka bude rumbunajiyar kayakin abinda ga Falasdinawa a garin Rafah na kudancin gaza. Shafin yanar gizo na Afirka News ya bayyana cewa dubban Falasdinawa wadanda suka yi kwanaki 90 basu sami abinci ba saboda rufe kofar shiar da abinci zuwa gaza. Wannan dai yana daga cikin walakanci mafi girma wanda sojojin HKI suka yiwa Falasdinawa a Gaza, tun bayan fara yakin. An kiyasta cewa falasdinawa kimani dubu 180 ne suka fito don karban agajin HKI da Amurka. Sannan jiragen yakin HKI sun yi barin wuta a sama don tsorata falasdinawa masu neman agaji. A yayinda sojojin yahudawa suna harbi a sama don tsoratar da su. Duk...
Duk tare da yakin da suke fafatawa a Gaza, dimbin yahudawan sahyoniyya masu bauta sun kutsa cikin masallacin Al-aksa da ke birnin Qudus inda suka gudanar da bukukuwan addinu a jiya Litinin. Shafin yanar Gizo na labarai ‘Arab News’ ya bayyana cewa, bakin na addini, farin ciki ne da kwace gabacin birnin Qudus daga hannun falasdinawa a yakin shekara 1967 tsakanin yahudawan da kuma larabawa. Birnin Qudus ta gabas dai nan ne masallacin Al-aksa yake, kuma nan ne Falasdinawa suke da dama. Yahudawan dai su na ganin dukkan birnin Qudus wanda ya hada har da inda masallacin Al-aksa yake mallakinsu ne kuma su na da shirin rusa masallacin don gina wurin bautansu a inda masallacin yake.
Kasar Spain ta bukaci kasashen duniya dasu kakabawa Isra’ila taklunkumi saboda ci gaba da yin fatali da kiraye-kirayen da ake matana tadakatar da yakin da take a Gaza. Ministan harkokin wajen Spain José Manuel Albares ya ce kamata ya yi kasashen duniya su kakabawa Isra’ila takunkumi domin kawo karshen munanan hare-haren soji a zirin Gaza da aka yi wa kawanya. Shugaban diflomasiyyar Spain yana magana ne gabanin wani babban taron kasashen Turai da na Larabawa da za a yi ranar Lahadi a Madrid. “Dole ne mu komai, don kawo karshen wannan yakin,” in ji shi. M.Albares ya bukaci a shigar da agajin jin kai, ba tare da wani sharadi ba, ba tare da tsangwama ba, ta yadda Isra’ila ba ta...
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda hakan ya sa Zamfara ta kasance a baya a fannin ilimi a faɗin Nijeriya. “Da sanin matsalolin da ke tattare da harkar ilimi, Gwamna Lawal ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a watan Nuwamba 2023, matakin da ya samar da sakamako mai kyau ga bangaren ilimi a jihar Zamfara. “Sama da makarantu 500 ne aka gyara tare da samar da kayan aiki tun bayan...
Ofishin yada labaran Gaza ya bayar da rahoton mutuwar Falastinawa 299 da suka fada cikin mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki, da karancin kayan masarufi da magunguna. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera na cewa, taimakon jin kai na cikin hadarin rubewa saboda haramcin da gwamnatin sahyoniyawan ta kakabawa na shiga Gaza a yayin da al’ummar zirin ke fama da yunwa. Ofishin yada labarai na Gaza ya kara da cewa: Gwamnatin Sahayoniya ta yi ikirarin cewa ta ba da izinin shigar da ayarin motocin agaji yayin da manyan motoci 300 ne kawai suka shiga zirin Gaza. Gwamnatin mamayar ta tilasta wa ayarin motocin agaji bin hanyoyin da ke da hatsarin gaske. Har ila...
An gudanar da taron dandalin tattaunawa na masanan Sin da Afirka karo na 14 a birnin Kunming dake lardin Yunnan na kasar Sin a yau Talata, 20 ga wata, inda wakilai kimanin 100 daga Sin da kasashen Afirka fiye da 50 suka halarci taron tare da tattauna fasahohin mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa na kasar Sin da kasashen Afirka da kuma zamanintarwa irin ta kasar Sin. Da yake tsokaci, Elia Kaiyamo, jakadan Namibia dake kasar Sin ya bayyana cewa, aikin zamanintar da kasa na da sarkakiya, domin kowace kasa tana da bambancin tarihi da al’adu da zamantakewar al’umma da tattalin arziki, don haka ya kamata a bi hanyoyi daban daban na zamanintarwa da suka dace da yanayin kasa,...

Babban Muftin Oman Ya Yi Suka Kan Taron Kungiyar Larabawa Saboda Rashin Saboda Rashin Ba Wa Gaza Muhimmanci
Babban Mufti na kasar Oman ya bayyana cewa: Matakin taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya fi kankara sanyi da rashin muhimmanci Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya jaddada yabonsa ga fitaccen matsayi na kasar Yemen da kuma matsin lamba da dakarun kasar Yemen suke yi na kai kayan agaji a zirin Gaza. A gefe guda kuma, ya nuna rashin jin dadinsa da raunin kudirin taron kasashen Larabawa kan daukan matakan matsin lamba kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da take aiwatar da kashe-kashen gilla kan al’ummar Falasdinu. A wani rubutu da ya yi a dandalin X, Al-Khalili ya bayyana godiyarsa ga jaruman kasar Yemen da kuma kasashen da suka bayar da gudumawa wajen matsin lamba...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati dake Dutse. Ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen siyan motoci Sharon guda goma sha shida da kuma motoci Golf Volkswagen guda ashirin domin raba wa mambobin ƙungiyar guda talatin da shida a matsayin tallafin dogaro da kai. Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma yanke shawarar fitar da...
Tshouwar Mawakiyar Hausa Hip-Hop, Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar 25 ga watan Mayu, 2025. ’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Rahotanni sun nuna cewar a ranar Laraba za a fara bidirin bikin har zuwa ranar Asabar. An shirya gudanar da walima, ƙwallon ƙafa, saukar karatun Alƙur’ani da sauransu har zuwa ranar ɗaurin aure. A shekarun baya, Queen...

Kungiyar Hizbullah Ta ce Marigayi Shahid Ra’isi Ya Kasance Mai Taimakawa Kasar Lebanon Da Kuma Falasdinawa Ne
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Na’im Kasim a wani jawabinda da ya gabatar don tunawa da cika shekara guda da shahadar shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyarsa, ya bayyana cewa shugaban ya kasance mai kaunar falasdinawa ne har cikin zuciyarsa. Sheikh Qasim ya kara da cewa, shugaba Ra’isi ya rike makamai da dama a rayuwarsa a JMI amma wannan bai canza shi ba, ya kasance yana tambaya ta dangane da gwagwarmaya da HKI a yankin Hizbullah da kuma sauran mujahidai a yankin. A lokacin shugabancinsa ya taimakawa kungiyar Hizbullah, sosai kamar yanda wadanda suka gabaceshi suka yi. A ranar 20 ga watan Mayun shekarar da ta gabata ce. Sayyid Ibrahim Ra’isi shugaban kasar Iran yayi...
“Mutanen Zamfara ba wawaye ba ne. Gwamnan ya kamata ya daina waɗannan maganganun ƙarya, ya daina farfaganda, ya kuma haɗa kai da masu ruwa da tsaki na gaskiya don magance matsalar tsaro,” in ji Gummi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Iran ta yi watsi da zarge-zargen taron kasashen Larabawa game da tsibirai uku na Tekun Fasha Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da zarge-zargen da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron kasashen Larabawa a Bagadaza dangane da tsibiran Iran guda uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa. Isma’il Baqa’i ya tabbatar a jiya Litinin 19 ga watan Mayu cewa: Tsibiran nan uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa wasu bangarori ne na kasar Iran, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ganin duk wani da’awar a wannan fanni ya sabawa ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, da kuma keta mutuncin yankunan kasa da ka’idojin...
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce ta samu gagarumar nasara wajen shiga sahun kasashen duniya a ranar cutar hawan jini ta duniya. Kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron tunawa da ranar hawan jini ta duniya, wanda aka gudanar a Kano. A taron tunawa da ranar, ma’aikatar ta shirya wani tattaki da taron manema labarai da nufin wayar da kan jama’a game da cutar hawan jini da inganta rigakafinta, ganowa da sarrafa shi. An fara tattakin ne a ma’aikatar lafiya ta hanyar gidan waya da karfe 8:30 na safe kuma aka kammala a cibiyar bayar da agajin gaggawa (EOC) da ke cikin asibitin...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta ceto wata tsohuwa mai shekaru 80 da aka sace a Jihar Kano, bayan wani samame da suka kai Ƙaramar Hukumar Garki. A yayin samamen, sun kashe mutane biyar da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sannan sun kama wasu biyar. Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso Rahoton ya ce samamen ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar 16 ga watan Mayu, 2025 bayan samun sahihan bayanan sirri. Waɗanda suka sace tsohuwar, Hajiya Hajara daga Ƙaramar Hukumar Minjibir, a Jihar Kano, su 12 ne ɗauke da bindigogi, kuma sun zo ne a kan babura. Rundunar ta haɗa...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga shugaban Iraqi Abdul Latif Rashid, wanda kuma shi ne shugaban karba-karba na majalisar shugabannin kasashen kungiyar Larabawa, tare da taya murnar kaddamar da babban taron kungiyar na 34, a birnin Baghdad na Iraqi. Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru sama da 80 da kafata, kungiyar kasashen Larabawa ta kasance mai mayar da hankali kan inganta hadin kai da karfafa yankin Larabawa da furta matsalolin kasashen da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya. Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen Larabawa wajen zurfafa aminci da ingiza hadin gwiwar moriyar juna da kara musayar...

Jagora: Jawaban Trump A Ziyar Da Ya Kai Wasu Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Abin Kunya Ne Gare Shi Ga Kuma Amurkawa
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara da cewa da dama daga cikin maganganunsa basu cancanci maida martani ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Asabar, a lokacinda yake ganawa da wasu malaman makaransu daga larduna daban daban na kasar, a Husainiyyar Imam Khonaini (q) a nan Tehran. Jagoran ya kara da cewa : Trump yace yana son amfani da karfin da Amurka...
Wani babban jami’in kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza ya bada sanarwan cewa an fara tattaunawa da HKI ta kawo karshen wannan yakin a birnin doha ba tare da shimfida wasu sharudda ba. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto Taher Annunu daga daga cikin manya-manyan jami’an kungiyar ta Hamas yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa tattaunawar zata hada dukkan matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu. Annunu ya ce kungiyarsa zata gabatar da dukkan abubuwan da yakamata a tattaunawa a kansu kama daga tsagaita wuta, musayar fursinoni da kuma ficewar sojojin HKI daga Gaza. Majiyar HKI ta nakalto firai ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa ya aika tawagar tattaunawarsa zuwa birnin Doha na kasar Qatar.
A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa. Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama abin tsoro kuma ya nuna akwai jan-aiki. “Alal misali, a jihar da ke da mutane kusan miliyan 6 tare da tarin ƙalubale, na’urar duban ɗan tayi ɗaya ce kawai a cikin dukkan cibiyoyin da gwamnati ta mallaka, kuma shi ma duk faci ne a jikinsa da salataf ko’ina! Nan take na ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya don dawo da ababen more rayuwa, samar...
HKI tana ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi a Gaza wanda ya ci rayukan Falasdiniwa kusan 300 da su ka hada kananan yara da mata. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambaci cewa;Tun da asubahin yau ne dai sojojin mamayar su ka fara kai wadannan munanan hare-haren wanda ba komai ba ne, sai kisan kiyashi akan Falasdinawada suke fama da matsananciyar yunwa saboda rashin abinci. Bugu da kari, mafi yawancin Falasdinawan da HKI take kai wa hare-haren suna rayuwa ne a cikin hemomi bayan da ta rushe musu gidajensu. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta sanar a cewa; A cikin sa’oi 24 da su ka gabata, adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 109, kuma tuni an fito...

Kungiyar Hamas Ta Shirya Zanga-Zangar Goyon Bayan Halaccin Yunkurin ‘Yantar Da Kasarsu Daga Mamayar Yahudawa
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta shirya wata zanga-zanga da Falasdinawa ke jaddada cewa: babu halacci ga ‘yan mamaya kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da gwagwarmaya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da halacci ko kuma wani ikon mallakar wani yanki na Falasdinu da ta mamaye, kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da kare kansu ta hanyar gudanar da gwagwarmaya har sai sun kwato dukkanin Falastinu tare da kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci kai wacce Qudus zata kasance a matsayin babban birninta. A yayin bikin cika shekaru 77 da kafuwar Nakba, -boren Falasdinawa na farko- kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa: “Ba za a yi wani sabon...
Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta ce ta dauki mataki mai muhimmanci wajen tabbatar da kiyaye ka’idojin aikin jarida ta hanyar kafa Kwamitin Ladabtarwa da kuma Kwamitin Ilimi da Horaswa. A cikin wata sanarwa da Sakatariyar kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed ta fitar, ta bayyana cewa Kwamared Sabo Abdullahi Guri ne zai jagoranci Kwamitin Ladabtarwar tare da Kwamared Mati Ali, da Dr. Musa Idris Barnawa da Yusuf Sulaiman a matsayin mambobi, yayin da Muhammad Askira Musa zai kasance Sakataren kwamitin. Sanarwar ta bayyana cewa an dora wa kwamitin alhakin tabbatar da bin ka’idojin aikin jarida, warware matsalolin rashin ladabi ko sabawa doka cikin aikin, da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana a aikin jarida a...
Tashar talabijin din almayadin ta watsa labarin dake cewa, daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 40,mafi yawancinsu daga yankin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare a yankuna mabanbanta na Gaza da su ka hada da Khan-Yunus. ‘Yan sahayoniyar sun yi amfani da manyan bindigogi da kuma jiragen sama na yaki. Adadin wadanda aka tabbatar da sun yi shahada ya zuwa yanzu sun haura 40. Sai dai wasu rahotannin da suke fitowa daga Gaza din sun ce, adadin shahidan ya karu zuwa 82. Jiragen HKI suna kai wa yankin na Gaza hare-hare daga kduancinsa zuwa arewacinsa cikin hauka. A Khan-Yunus ‘yan Sahayoniyar sun...

Iran Da Kasashen Turai uku wato E3 Zasu Bude Tattaunawa A Tsakaninsu A Birnin Istambul A Gobe Jumma’a
Manya-Manyan Jami’an gwamnatin kasar Iran da tokwarorinsu na kasashen turai uku wadanda ake kira, E3 zasu fara tattaunawa a tsakaninsu dangane da tattaunawa dangane da makamashin nukliya tsakanin Iran da Amurka wanda ke ci gaba a halin yanzu. Kasashen E3 dai sun hhada da Faransa, Jamus da kuma Ingila wadanda suke sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu a shekara ta 2015. Manufar taron ko kuma tuntubar juna tsakanin Iran da wadannan kasashe uku itace sanyasu a kan hanya kan yadda tattaunawar take tafiya, da kuma yadda ake son a gabatar da sauye-sauye wa yarjeniyar JCPOA, tunda Amurka ta waresu daga wannan tattaunawar. JMI tana ganin idan har an cimma wata yarjeniya da Amurka kan shirinta na makamashin nukliya ba zai bambanta sosai...
Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Jigawa ta naɗa Kwamared Sani Muhammad Gumel da Kwamared Usman Mohammed Usman a matsayin mambobin majalisar kungiyar na musamman (Ex-Officio). Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar ta kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed, ta sanya wa hannu kuma ta rabawa manema labarai a Dutse. Ta bayyana cewa, an yi waɗannan naɗe-naɗen ne a matsayin girmamawa da yabo ga jajircewarsu, ƙwarewa, da kuma gudummawar da suke bayarwa wajen haɓaka aikin jarida a Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya. Aisha Abba Ahmed ta ƙara da cewa, duka waɗannan mutane biyu sun dade suna nuna ƙwazo da biyayya ga manufofi da burin ƙungiyar. Ta ce, ana sa ran waɗannan mambobin na...
Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa. Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Yarjejeniyar ta samu karɓuwa daga ɓangarorin da dama, inda wasu ke ganin hakan zai ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da bunƙasa fasahar zamani. Sai dai wasu na nuna damuwa kan yawan makaman da Saudiyya ke saye daga Amurka, suna mai cewa hakan na iya ƙara tsananta rikice-rikice a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
An zabi Comrade Isma’il Ibrahim Dutse na ma’aikatar yada labarai a matsayin sabon shugaban kungiyar ‘yan jaridu NUJ ta kasa reshen jihar Jigawa ba tare da hamayya ba. A lokacin da yake sanar da sakamakon zaben, mataimakin shugaban kungiyar na kasa mai kula da shiyya ta daya wato Zone A, Comrade Tukur Umar Muhammad ya ce an kuma zabi Nura Sani Bello da Najib Umar da Aminu Umar Shuwajo ba tare da hamayya ba. Tukur ya ce Aisha Abba Ahmed ta kamfanin dillancin labarai na kasa NAN dake Dutse ta samu nasara da yawan kuri’u 46, shi kuma Abdullahi Mukhtar ya sami kuri’u 34, yayin da Larai Musa na NTA ta sami kuri’u 14. Tukur Umar, ya bayyana...
Kasar Sin ta harba wani rukunin taurarin dan adam daga cibiyar harba tauraron na Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar. An harba taurarin ne jiya Lahadi da misalin karfe 9:27pm agogon Beijing, bisa amfani da samfurin rokar Long March-6 da aka yi wa ‘yan gyare-gyare. A cewar cibiyar ta Taiyuan, rukunin taurarin mai suna Yaogan-40 02, ya shiga da’irarsa cikin nasara. Za a yi amfani da taurarin ne wajen gwaje-gwajen fasahohi da gano yankuna masu tasirin haduwar maganadisu da lantarki. Aikin na jiya shi ne karo na 574 da aka yi amfani da samfurin rokar Long March. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
‘Hudu daga cikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun isa birnin Jakarta na kasar Indonesia domin halartar taron majalisun kungiyar kasashen musulmi. A yau Litinin ne dai aka bude taron majalisun kasashen kungiyar kasashen musulmi a birnin Jakarta na kasar Indonesia wanda shi ne karo na 19. Taken da aka bai wa taron karo na 19 shi ne: “Kafa Gwamnatoci masu hikima a kuma cibiyoyi masu karfi a matsayin ginshikin jajurcewa.” Tawagar ta Iran dai wacce Ruhullah Mutafakkir Azad yake jagoranta, ta kuma kunshi Sara Fallahi, Sayyid Yahya Sulaimani, da Muhammad Mahdi Shahriyari. Taron zai ci gaba har zuwa ranar 15 ga watan nan na Mayu da ake ciki, kuma tawagar ta Iran za ta gabatar da jawabi a...
Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka. A jawabin da ya gabatar akan ranar ma’aikatan jiniya ta duniya, Daraktan riƙo na Hukumar ta WHO a Afirka, Chikwe Ihekweazu, ya ce ficewar tasu za ta nakasa harkokin kiwon lafiyar da ake riritawa a nahiyar. Ihekweazu ya cigaba da cewa wannan ɓangare na masu aikin jinyar na da matuƙar muhimmanci ga ɗaukacin al’umma, don haka bashi kulawa, abu ne da ya dace, domin zai ba da gudunmawa ga cigaban ɓangaren lafiya,...
Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta. Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata. Sanarwar ta PKK ta kuma kunshi cewa;Jam’iyyun siyasa na kurdawa za su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa domin bunkasa tsarin demokradiyya da sake gina al’ummar Kurdawa.” Haka nan kuma PKK ta ce, da akwai alakar a sake Shata salon alakar Kurdawa da Turkiya. A martanin da jam’iyyar dake Mulki a Turkiya ta fitar, ta bayyana cewa; Zartar da matakin da kungiyar...
Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta bada sanarwan cewa a shirye take ta saki fursina mai suna Edan Alexander wanda yake da jinsiyar Amurka da HKI don bude kofa ga tattaunawar tsagaaita wuta a gaza da kuma bude kofar rafa don samar da kayakin abicni a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jami’an kungiyar tana fadar haka a jiya Lahadi. Khalil Al-Hayya shugaban kungiyar ya bayyana cewa Hamas ta amince da hakan ne bayan wata tattaunawa da Amurka kan batun. Ya kuma kara da cewa kungiyar tana son a fara tattaunawa da gaske tsakaninta da HKI ta hanyar masu shiga tsakani, don kawo karshen yakin da kuma ficewar sojojin yahudawa gaba daya daga...
Tsohon jami’in harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Josep Borrell ya yi kakkausar suka ga kungiyar kan rashin daukar mataki game da kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ke yi a zirin Gaza yana mai cewa “rabin bama-baman da aka jefa a zirin Gaza ne muke kawowa.” Da yake jawabi bayan karbar lambar yabo ta Carlos V ta Turai da ke Spain, Josep Borrell ya ce nahiyar Turai na shaida kawar da wata kabila tun bayan karshen yakin duniya na biyu, domin gina wurin yawon bude ido bayan korar da Falasdinawa. Ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin kisan kiyashi, ya kuma ce kungiyar EU, duk da cewa tana da hanyoyin nunna adawa da kuma kawo karshen ayyukan Isra’ila,...
Da safiyar yau Asabar Falasdinawa 7 sun yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai a yankin Gaza. Sojojin HKI sun kai harin ne a kan sansanin ‘yan hijira na unguwar ” al-Sabrah” a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 5 a iyalai daya na Dulaibh. Shahidan su nel Saqar Ahmad Fu’ad dulaibh, da matarsa Hindu, da ‘ya’yansu Ahmad, Hamzah, da Abdulazizi. Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren ta jirgin sama maras matuki a unguwar “Tuffah” dake birnin Gaza, da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. Su ma jiragen ruwan HKI sun kai wasu hare-haren munanan a garin Rafah da ya yi sanadiyyar shahadar Muhammad Sa’id al-Burudawil. A tsakiyar birnin Gaza, ma dai...
Fira ministan kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya kira yi Majalisar kasa wacce take kula da makaman Nukiliyar kasar da su yi taro. Wannan matakin da ake yi wa Kallon mai hatsari yana faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan take yaki da Indiya. Ita dai Majalisar kasar Pakistan dake kula da makaman Nukiliya da kuma manufofin kasa na koli, ta kunshi manyan kwamandojin soja, da fararen hula, aikinta kuma shi ne kula da manyan batutuwa da su ka shafi kasa daga ciki har da siyasar makaman Nukiliya da kuma makamai masu linzami.An kafa wannan majalisar ne dai a 2000. Tashar talabijin din “Sama News” ta bayar da labarin dake cewa; Mahalarta taron za su yi bitar halin da...
A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa tsakanin Tehran da Washington. M. Baghai ya bayyana cewa ziyarce ziyarce da Araghchi zai yi na daga cikin manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da karfafa alakarta da makwabtanta. “Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai fara tafiya birnin Riyadh don ganawa da manyan jami’an Saudiyya, sannan kuma zai tafi Doha don halartar taron tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Larabawa.” Bayanin hakan ya...

An Yi Taron Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasarar Yakin Da Sinawa Suka Yi Kan Zaluncin Japan Da Yakin Ceton Kasa Na Tsohuwar Tarayyar Soviet
An gudanar da taron musayar al’adu da cudanyar al’umma na murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya na jama’ar kasar Sin a kan zaluncin kasar Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kamfanin gidajen talabijin da rediyo na kasar Rasha suka shirya a birnin Moscow. An karanta wasikun taya murna daga shugaban kasar Sin Xi Jinping da na Rasha Vladimir Putin a wajen taron. A jawabinsa, babban darektan CMG, Shen Haixiong, ya bayyana cewa, yayin da bikin shekarar al’adun Sin da Rasha ya kankama, bari mu dauki ruhin sakon wasiku na taya murna a matsayin jagora, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu....
Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani domin kwantar da hankulan al’amura da kuma hana bullar rashin kwanciyar hankali a yankin. Al-Julani ya yi nuni da cewa: “Shisshigin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi ba bisa ka’ida ba ne, kuma sun bayyana cewa: Siriya ta amince da yarjejeniyar kawo karshen rikici ta shekara ta 1974,” yana mai cewa “Tsarin mulkin kasar Siriya zai tantance ‘yancin...

Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kungiyar tarayyar turai wato Kaja Kallas, ya bayyana mata yadda bangarorin Amurka da Iran za su kai ga cimma yarjeniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasarsa. Ministan ya kara da cewa tun kimani shekaru 20 da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bangaren tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar ta zaman lafiya. Kuma batun shirin nukliyar kasar Iran tana daga cikin ayyuka...
Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar . Da yake magana a gidan talabijin na gwamnatin kasa, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim Yassin, ya zargi Abu Dhabi da keta hurumin ‘yancin Sudan ta hanyar mara baya ta fuskar soji ga RSF, ciki har da samar da makamai, da jiragen yaki marasa matuka, da makamai masu linzami wadanda aka kai hari da su a baya-bayan nan a tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da kuma tashoshin...
Gwamnatin Sudan da ke da goyon bayan sojoji ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana bayyana ƙasar a matsayin mai katsalandan, a cewar Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin ranar Talata, Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat ɗinta a ƙasar Gulf ɗin. Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi Inter Milan ta kori Barcelona daga Gasar Zakarun Turai Ya zargi UAE da take hurumin Sudan ta hanyar “ƙawarta”, wato Rundunar RSF, wacce ke yaƙi da sojojin Sudan tun watan Afrilu 2023. “Dukkan duniya ta shaida, fiye da shekaru biyu, laifin kai hari...
Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu. Mohammed Ali al-Houthi mamba a majalisar koli ta siyasa ta kungiyar Ansarullahi ya bayyana cewa: Sanarwar Trump gazawa ce ga Netanyahu, kuma dole ne fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi murabus daga kan mukaminsa. Ya kara da cewa: “Za su fara tantance sanarwar da Trump ya bayar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen,” bisa la’akari...
Shugaban tawagar kasar Yemen, Mohammed Abdul Salam, ya sanar da cewa ayyukan Yemen na tallafawa Gaza ba zai tsayawa ba Shugaban tawagar shiga Tsakani na kasar Yemen Abdul Salam ya bayyana cewa: Yemen ta samu sakon bukatu daga Amurka ta hanyar masarautar Oman, kuma wanda ya sauya matsayinsa Amurka ce, ba Yemen ba. Ya kara da cewa ikirari da Amurka ta yi na mika wuya, yana nuni ne ga gazawa, saboda Amurka ba zata iya kare jiragen ruwan haramtaciyar kasar Isra’ila daga hare-haren Yemen ba. Abdul-Salam ya kara da cewa: Fahimtar farko da aka samu tsakanin Amurka da Yemen ba ta da wata alaka da matsayar Yemen kan goyon bayan Gaza, yana mai nuni da cewa za a samu ci...
Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke huldar diflomasiyya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kiran hanzarta dawowar ma’aikatan ofishin jakadancin Sudan gida daga Abu Dhabi. Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron Sudan ya bayyana cewa: Fiye da shekaru biyu, daukacin duniya take bibiyar laifuffukan wuce gona da iri kan kasar Sudan, da tabbatar da tsaron yankunanta, da tsaron ‘yan kasarta daga hadaddiyar daular Larabawa ta hanyar wakiliyarta na cikin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata ƙungiya mai rajin kare muradun al’ummar Hausawa a Nijeriya mai suna Kungiyar Hausawan Nijeriya ta tsaya kai da fata cewa dole a ƙyale Hausawa su kafa ƙungiyarsu kamar kowacce ƙabila tun da dai doka ba ta hana su ba. Martanin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da masu kiran ke shan sukar cewa suna ƙoƙarin rura wutar ƙabilanci ne a Arewacin Nijeriya Najeriya, musamman a daidai lokacin da yankin ke buƙatar haɗin kai domin magance matsalolinsa. Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus To sai dai ƙungiyar ta ce ba ta ga dalilin da zai sa a ƙalubalanci yunƙurin nasu ba, tun da dai ’yan ƙabilar Yarabawa suna da ƙungiyar Afenifere,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hanyar deblomasiyya ce kadai zata warware matsakar shirin nukliyar kasar iran da kasashen yamma. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawa ta wayar tarho da jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Kaja Kallas. Labarin ya kara da cewa ministan yana ganin matsalolin shirin Nucliya da kuma tsaron kasar ba za’a iya warwaresu ba sai ta wannan hanyar. JMI ta dauki wannan hanya ce don ita ce kadai wacce zata kai da gamsuwar ko wani bangare a cikin al-amuran da suke sabani a cikinsu. Aragchi ya fadawa Kallas kan cewa da wannan dalilin ne JMI ta dauki hanyar...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kaddamar da manyan jami’an likitocin kasa a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan Hukumar Alhaji Umar Ahmed Labbo ne ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da aikin da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, hukumar ta kaddamar da tawagar likitocin guda 10, inda ya bukaci kungiyar da ta yi aiki da gaskiya, hakuri, da jajircewa wajen yi wa alhazan jihar hidima a kasar Saudiyya. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce aikin amana ce da bai kamata kungiyar ta dauka da wasa ba. Ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewa da wannan tawagar, inda ya nuna cewa, wannan shi ne karon farko da jihar...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa tattaunawar sulhu a Gaza ba ta da wani tasiri a wannan mataki. Ofishin kungiyar, ya yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba kan gwamnatin Netanyahu don kawo karshen laifukan yunwa, kishirwa da kisan kai a Gaza, in ji wani babban jami’in kungiyar. Halin da ake ciki a Gaza ya kai intaha inji kungiyoyin kasa da kasa. A wani rahoto data fitar a baya baya nan kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta yi gargadi kan halin da ake ciki a zirin fiye da na watanni 19 da suka gabata.” kungiyar ta jaddada cewa “mafi yawan jama’a na yankin na fuskantar matsananciyar hadarin yunwa.” Sama da mutane miliyan daya...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Cikin Gaggawa Kan Duk Wani Hari Kan Kasarta
Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke yi, ko da kuwa wani mataki ne da ya sabawa ‘yancin kai, ko cikakken amincin Iran ko kuma muhimman muradun kasa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, za a mayar da martani cikin gaggawa, da ya dace kuma halastacce. Wannan dai ya zo ne a cikin wata wasika da Amir Sa’ed Irawani, jakada kuma wakilin din-din-din na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya aikewa babban...
Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawar da cewa ta hada baki da dakarun kai daukin gaggaawa wajen yi wa mutanen yankin Darfur kisan kiyashi. A nata gefen Hadaddiyar Daular Larabawan ta ki amincewa da tuhumar da Sudan ta yi mata tana mai siffata ta da cewa; Farfaganda ce, kuma Sudan din ta yi hakan ne domin kawar da hankulan duniya daga kan laifukan da sojoji suke aikatawa.
Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa. Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta da goyon bayan dakarun (RSF) da suka shafe shekaru biyu suna yaki da sojojin Sudan. Khartoum na zarginsu da kasancewa masu goyan bayan kisan kare dangi” da ake ci gaba da yi wa al’ummar Massalit na Darfur, saboda zarginsu da goyon bayan dakarun gaggawa na Janar Hemedti (RSF). Khartoum na fatan alkalan kotun su umurci Hadaddiyar Daular Larabawa da ta daina goyon bayan kungiyar RSF,...
113-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauransu inda muke masu karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasasnce tare da mu. ///…Madallah, masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da cewa {gwagwarmayar kwace kasar Falasdinu zai fara da tube Mahmood Abbas daga shugabancin kungiyar Kwatar yencin Palasdinawa PLO}. Shugaba Mahmood Abbas, shugaban gwamnatin jeka na yi ka na Palasdinawa ya dade yana hana ruwa guda a gwagwarmayan da Falasdinawa Musamman a Gaza suke yi...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa Iran, ya kara haifar da shakku game da aniyar Washington na neman hanyar diflomasiyya. “Don ci gaba a kan wannan tafarki dole ne dayan bangaren ya nuna kyakkyawar niyya cewa da gaske ya ke,” in ji shi, kafin ya ce: “Iran, a matsayinta na mamba a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), dole ne ta ci moriyar makamashin nukiliya don dalilai na zaman lafiya.” Ministan...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya soki mummunar rawar da Faransa ke takawa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya soki kasar Faransa saboda abin da ya bayyana a matsayin gurgunta rawar da take takawa a kokarin diflomasiyya kan matsayin Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. A wani rubutu da ya yi a dandalin X, kakakin ya yi tsokaci kan zargin na Faransa, yana mai cewa: Ikirarin da ministan harkokin wajen Faransa ya yi na cewa Iran na daf da kera makamin nukiliya, da’awa ce ta karya kuma marar tushe. Ya kara da cewa: Wadannan kalamai na karya, tare da barazanar sake kakabawa Iran takunkumi, suna kara karfafa ra’ayin cewa matsayar Faransa na rikidewa zuwa wani matsayi na...
Gwamnatin jihar Kebbi, ta baiwa ma’aikatan jihar tabbacin ci gaba da jajircewa wajen kyautata jin dadin su da kuma kare hakkokinsu. Gwamna Nasir Idris wanda ya ba da wannan tabbacin a lokacin da yake jawabi ga ma’aikata domin bikin ranar watan Mayu a Birnin Kebbi, ya jaddada cewa ma’aikata aminai ne masu kima wajen ci gaban jihar Kebbi, kuma su kasance masu ruwa da tsaki da ba za a yi watsi da su ba. Gwamna Idris, wanda ya bayyana bikin ranar Mayu a matsayin wani muhimmin lokaci, ya yabawa ma’aikatan bisa jajircewarsu da irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar. “Kwazonku da jajircewarku sune kashin bayan tattalin arzikinmu. Ina yaba muku kan kokarinku na...
Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Suna tsaye kafada da kafada da kungiyar Hizbullah ta Lebanon kan duk wani yunkuri na kokarin tada zaune tsaye daga ‘yan sahayoniyya Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi, ya yi gargadin yadda yunwa ke barazana ga Falasdinawa sama da miliyan biyu a zirin Gaza, wadanda ke fuskantar yunwa a idon dukkanin bil’adama. Yana mai jaddada cewa: Wannan abin kunya ne ga kasashen duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa. A jawabin da ya gabatar na zagayowar ranar shelar Falasdinawa kan neman taimakon Falasdinawa dangane da hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya, Sayyid Al-Houthi ya yi bayani kan sabbin abubuwa da suka shafi wuce gona...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...