MDD ta yi maraba da yarjejeniyar Iran da IAEA dangane da komawa bincike
Published: 11th, September 2025 GMT
Stéphane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana a jiya Laraba cewa, MDD ta yi maraba da yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA, kan “tsarin da zai ba da damar komawa bincike a Iran”.
A yayin taron manema labarai a wannan rana, Dujarric ya ce wannan yarjejeniya wani mataki ne mai kyau da Iran da IAEA suka dauka don komawa cikakkiyar hadin gwiwa.
Dujarric ya kuma jaddada muhimmancin cikakkiyar hadin gwiwar Iran da IAEA. Yana mai cewa, hakan yana da muhimmanci wajen kafa wani tsari na dogon lokaci, wanda zai “tabbatar da shirin nukiliyar Iran gaba daya don zaman lafiya”.
A ranar Larabar, yayin ziyararsa a Alkahira, babban birnin kasar Masar, ministan harkokin wajen Iran Abass Araghchi, ya sanar da cewa, Iran ta kulla yarjejeniya da IAEA don sake yin hadin gwiwa tsakaninsu kan batun nukiliyar Iran.
Iran ta dakatar da hadin gwiwa da IAEA, bayan harin da Isra’ila da Amurka suka kaddamar kanta a watan Yunin bana.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sauyin Yanayi : Shugabannin Afirka sun bukaci a yi adalci September 11, 2025 Sheikh Qasim: Hare-Haren HKI Kan Qatar Sashe Ne NA Shirinta Na “Isra’ila Babba” September 10, 2025 Majiyar Gwamnatin Yamen Ta Ce HKI Ta Kai Wasu Sabbin Hare-Hare Kan Kasar September 10, 2025 Aragchi: Yarjeniya Da IAEA Ya Nuna Hakurin Iran Bayan Hare-Hare Kan Cibiyoyin Nukliyarta September 10, 2025 Iran Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Guda kan HKI bayan Harin Qatar September 10, 2025 Sojojin HKI Sun Ragargaza Hasumiyyar Tayyib II A Kokarin Korar Falasdinawa Daga Birnin Gaza September 10, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Al-Mujtaba (a) 138 September 10, 2025 Araqchi Ya Isa Kasar Tunisiya A Wata Ziyarar Aiki Da Ya Kai. September 10, 2025 Babu Gaggawa Na Fara cire Haraji Kashi 5 Na Man Fetur A Nijeriya September 10, 2025 Da Alama Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya September 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin isra’ila na fuskantar suka game da matakin da ta dauka na kai hari kan kungiyar unicef ta majalisar dinkin duniya a gaza, matakin da falasdinawa da masu sa ido ke gani a matsayin wata dabara ta murukushe kungiyoyin agaji da kuma fitar da kungiyoyin majalisar dinkin duniya daga yankin gaza
Rahoton da wani jami’in majalisar dinkin duniya ya fitar a jiya jumaa ya nuna cewa sojojin isra’ila sun kama wani ma’aikacin UNICEF mai suna Raed Afif mai shekaru 45 da haihuwa a kerem shalom alokacin da yake gudanar da ayyukansa.
Yazu wa yanzu isra’ila bata bayyana dalilan da suka sanya ta kama shi ba kuma take ci gaba da tsare shi.
Kwana daya kafin tayi kamun isra’ila ta bukaci kungiyar ta Unicef da ta kwashe dukkan kayayyakin agajinta daga yankin , kawai sai ta rufe dukkan kofofin shiga da magunguna zuwa asibitocin dake arewacin yankin Gaza. Kungiyoyin bada agaji na duniya sun yi gargadin cewa wannan matakin an dauke shi ne domin yanke duk wasu ayyukan jinkai da ake yi da kuma korar dukkan kungiyoyin agaji da hakan zai kara sanyawa yanayi ya kara tazzar a yankin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci Daga Yanzu November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci