Ambaliyar ruwa ta tsayar da ababen hawa cak a tsakiyar birnin Abuja
Published: 12th, September 2025 GMT
An samu ambaliyar ruwa a tituna da dama na tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja sakamakon mamakon ruwan saman da aka tafka da safiyar Alhamis.
Yankunan da ambaliya ta fi shafa sun hada da Asokoro, Guzape, Jabi, Kado da kuma Wuse.
Wasu direbobi da suka zanta da Aminiya sun ce sun sha wahala wajen samun hanyar wucewa a unguwannin Asokoro da Guzape yayin ruwan saman.
A wani bidiyo da wani mai suna Prince Adebisi Adetunji ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga yadda ruwan ya mamaye titin Asokoro, inda direbobi da mazauna yankin suka yi ta kokarin yadda za su tsallake ruwan.
Ambaliyar dai ta kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa, inda aka ga motoci na ta kokarin ketare ruwan da ya mamaye titunan.
Mazauna yankin sun ce rashin ingantaccen tsarin magudanun ruwa ne ya kara dagula lamarin.
Wani direba mai suna Musa Ibrahim, ya shaida wa wakilinmu cewa tituna da dama a Asokoro da Guzape sun ki biyuwa, lamarin da ya haddasa cunkoso.
Shi ma wani direban, Emmanuel Peter, ya ce shi da wasu direbobin sai da suka jira na wani lokaci kafin daga bisani su samu wata hanyar da ba ta da hatsari su bi.
“Ya kamata hukumar birnin ta nemo mafita kan matsalar magudanun ruwa a birnin tarayya,” in ji Peter.
A cewarsa, matsalar ba ta tsaya ga Asokoro da Guzape kadai ba, domin tana faruwa a kusan dukkan unguwanni idan aka yi ruwan sama mai yawa.
“Hakan na faruwa a Jabi, Wuse, har ma da yankin Central Area a duk shekara. Dole ne masu kula da birnin su dauki mataki kan wannan matsala,” in ji shi.
Wani bangare na titin Obafemi Awolowo da ke Jabi ma ya cika da ruwa yayin ambaliyar.
An ga direbobi da dama suna kokarin ketare ruwan da ya mamaye titin.
Alhaji Nuhu Ademola ya ce motarsa ta makale a cikin ruwan a kusa da tashar motar Jabi.
A cewarsa, ya dauki kusan minti 30 kafin ruwan ya ragu sannan ya samu damar fita da motarsa.
Alhaji Ademola ya bukaci hukumar birnin da ta nemo mafita mai dorewa kan matsalar ambaliyar ruwa a birnin na Abuja.
“Ai ba sai mun fada musu ba, su ma suna gani. Yaya za a gina birnin tarayya ba tare da tsarin magudanar ruwa mai kyau da tsari ba?” in ji shi.
Wakilinmu ya rawaito cewa an kuma samu irin wannan ambaliya a yankin Life Camp da kuma Wuse.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya
এছাড়াও পড়ুন:
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp