Wata babbar tawagar jami’an tsaron Sudan ta ziyarci Somaliya
Published: 28th, August 2025 GMT
Tawagar Sudan karkashin jagorancin babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa (NISS) Manjo Janar Ahmed Mufadal ta isa Mogadishu babban birnin kasar Somalia a wata ziyarar aiki da ta kai kasar, inda ta gana da shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud a fadar shugaban kasa dake Mogadishu.
Jagoran tawagar ta Sudan Mufadal Sheikh Mohamud ya aike da sako daga shugaban kwamitin rikon kwarya na kasar Sudan, Laftanar Janar Abdel Fattah Al-Burhan.
Sakon ya hada da jaddada aniyar Khartoum na karfafa hadin gwiwa da Somaliya, musamman a fannin tsaro da leken asiri.
Taron ya samu halartar babban daraktan hukumar leken asiri ta kasar Somalia (NISS), Mahad Mohamed Salad, wanda ya tattauna da Mufadal hanyoyin inganta hadin gwiwa domin tunkarar kalubalen da yankin nasu ke fuskanta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka E3 za su gabatar da bukatar dawo da takunkuman MDD a kan Iran: Reuters August 28, 2025 Shugaban Rwanda ya musunta zargin sojojin kasarsa da hannu a rikicin Congo August 28, 2025 ASUU: Gwamnatin Najeriya ba ta aiwatar da ko daya daga cikin bukatunmu ba August 28, 2025 Iran da Rasha Sun Zasu Hadakai A fagen Watsa Labarai August 27, 2025 IRGC Sun Halaka Yan Ta’adda 13 A Yankin Sistan Baluchestan August 27, 2025 Zanga-Zanga Ta hana Wakilin Amurka Ziyara A Kudancin Lebanon August 27, 2025 Hamas: Isra’ila Tana Rike Da Gawawwakin Falasdinawa 726 August 27, 2025 Isra’ila Ta kashe Falasdinawa Fiye da 1000 A Yamma Da Kogin Jordan August 27, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za Su Iya Komawa Zaman Tattaunawa Da Amurka A Kan Wasu Sharudda August 27, 2025 Masu Binciken Hukumar IAEA Ba Za Su Shiga Wajen Da Amurka Ta Kai Hari Ba A Cibiyoyin Nukiliyar Iran August 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan
Isra’ila ta amince da gina sabbin gidaje 1,300 a yankin Gush Etzion, kudu da Gabashin Urushalima da ta Mallake, wanda hakan ke nuna wani sabon ci gaba da fadada matsugunai ba bisa ka’ida ba a fadin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.
A cewar tashar talabijin ta Isra’ila Channel 14, Kwamitin tsare-tsare da Gine-gine na musamman da ke kula da matsugunan da ke Gush Etzion ya amince da wannan shawara a farkon wannan makon, inda ya shafi unguwar Har HaRusim, wadda ke kusa da matsugunan Alon Shvut, kudu maso yammacin Gabashin Urushalima da aka Mallake.
Shirin bai shafi gidaje ba kawai, har ma da gina makarantu, wuraren jama’a, wuraren shakatawa, da kuma babbar cibiyar kasuwanci da aka yi niyya don yi wa al’ummomin da ke makwabtaka hidima.
Majalisar Yankin Gush Etzion ta yi maraba da wannan mataki, tana mai ganin hakan a matsayin martani ga karuwar bukatar mazauna yankin.
Wannan sanarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da damuwar da ake da ita game da ayyukan Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan.
Jawabin Trump ya zo ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta amince da wasu kudirori biyu da nufin hade Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma yankin Ma’ale Adumim.
Irin wadannan matakai za su ware Gabashin Kudus daga yankunan Falasdinawa da kuma raba Yammacin Kogin Jordan zuwa yankuna biyu daban-daban, don haka za su kawo cikas ga yiwuwar hadewar kasar Falasdinu.
Majalisar Dinkin Duniya da yarjejeniya kasa da kasa sun sha nanata cewa matsugunan Isra’ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye haramtattu ne a karkashin dokokin kasa da kasa, gami da Yarjejeniyar Geneva ta Hudu.
Bugu da kari, kungiyar kare hakkin dan adam ta Peace Now ta bayyana shirin E1 a matsayin “mummunan rauni” ga samar da Falasdinu, tana mai jaddada cewa aiwatar da shi zai kawo cikas ga yunkurin kafa kasar Falasdinawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci