2025-09-17@23:15:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2643
«jiragen Ruwan»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Bayan sama da shekaru biyu a kan mulki, gwamnatin Sakkwato ta fara waiwayar ’yan gudun hijira da hare-haren ’yan bindiga suka raba da muhallansu. A dukkanin ƙananan hukumomi 23 na jihar akwai ’yan gudun hijira da ke buƙatar ɗauki. Tsohon mataimakin Gwamnan Gombe da wasu jiga-jigai sun fice daga PDP zuwa APC Saudiyya ta ƙaƙaba wa masu laifukan rashin ɗa’a sabuwar tara Wasu ma sun tsallaka zuwa Jamhuriyar Nijar, inda suka yada zango a jihohin Dosso, Maradi da Tahoua. Mutane da dama, musamman yara, suna cikin mawuyacin hali. Wasu marayu suna yin sana’o’i kamar tuƙa baro, tara dutse ko yin bara domin samun abin ci, ba tare da wata kulawa daga gwamnati ba. Da yawa daga cikinsu ba sa zuwa...
Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce a yau Juma’a, shugaba Amurka Donal Trump zai rattaba hannu kan wata doka da za ta sauya sunan ma’aikatar tsaron kasar zuwa ma’aikatar yaki. Canjin suna na dindindin na buƙatar Izinin majalisa, to amma umarnin zartarwa da shugaban zai sa wa hannu, zai ba da damar amfani da sunan na wucin gadi. A wata hira da aka yi da shi, sakataren tsaron kasar Pete Hegseth, ya ce hakan zai nuna wani sauyi da ke nufin ma’aikatar tsaron kasar ta Pentagon ta rungumi wani suna na Jarumta. Ya ce ko nasarorin da kasar ta samu a yakin duniya na daya da na biyu ta same su ne da sunan Ma’aikatar Yaki, ba wai...
Rahotanni sun bayyana cewa sanar da sabon kwamandan hedkwatar khatamul ambiya na nuna irin sabbin canje –canje da irin tsari da ta bullo da shi kan abubuwan da ta fi bawa muhimancin, kuma wata babbar cibiya da ake sa ido kan tsaron kasa, canjin jagoranci na iya yin tasiri babba a bangaren soji wajen tunkarar kalubalen da take fuskanta a bangarori daban daban. Major ganaral Ali Abdullahi sabon kwamandan hekdawatar khatamul Ambiya ya jaddada a bayanin da ya fitar cewa sojojin kasar Iran a shirye suke su kare kasar daga duk wata barazana, da kuma kare dukkan ababen girmamawa na kasar, Ya kara da cewa a halin yanzu sojojin kasar sun fi zama cikin shirin ko ta kwana fiye da...
“Jami’an yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), sun gano wadannan kayan laifuka ne, ta hanyar jajircewa da himma da kuma sanin makamar aiki.” Rundunar ta ce, dukkannin abubuwan da aka baje kolin nasu da wadanda ake zargi da aikata laifin, na nan a hannun hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, inda ake ci gaba da bincike a dakin gwaje-gwaje, don tabbatar da kayan laifin da aka kama. Hukumar ta NDLEA, ta bukaci jama’a su kasance cikin taka-tsan-tsan, tare da kai rahoton abubuwan da ake zarginsu da aikatawa ko kuma abubuwan da suka shafi muggan kwayoyi ga ofishinta ko wata hukuma mafi kusa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin jihar Sakkwato ta bayar tallafin motoci 14 kirar Hilux da babura 150 ga dukkan jami’an tsaron jihar don karfafa aikin sintiri. Tallafin kari ne a kan Hilux 170 da babura da gwamnatin ta bayar a baya. Ba abin mamaki ba ne idan na fice daga NNPP – Abdulmumin Kofa ’Yan sandan Kaduna sun gayyaci El-Rufa’i kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye Sakataren Gwamnatin jihar, Muhammad Bello Sifawa ne ya miƙa kayan a madadin Gwamnan jihar, Ahmad Aliyu a wani ƙwarya-ƙwaryar bikin da aka yi a gidan gwamnatin jiha a ranar Alhamis. Bello Sifawa ya ce hukumomin tsaro ne suka roki a ba su ababen hawan a lokacin zaman majalisar tsaro ta jihar, shi kuma Gwamnan ya amince...
Gwamnatin jihar Sakkwato ta bayar tallafin motoci 14 kirar Hilux da babura 150 ga dukkan jami’an tsaron jihar don karfafa aikin sintiri. Tallafin kari ne a kan Hilux 170 da babura da gwamnatin ta bayar a baya. Ba abin mamaki ba ne idan na fice daga NNPP – Abdulmumin Kofa ’Yan sandan Kaduna sun gayyaci El-Rufa’i kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye Sakataren Gwamnatin jihar, Muhammad Bello Sifawa ne ya miƙa kayan a madadin Gwamnan jihar, Ahmad Aliyu a wani ƙwarya-ƙwaryar bikin da aka yi a gidan gwamnatin jiha a ranar Alhamis. Bello Sifawa ya ce hukumomin tsaro ne suka roki a ba su ababen hawan a lokacin zaman majalisar tsaro ta jihar, shi kuma Gwamnan ya amince...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya gana da jami’a mi kula da al-amuran harkokin wajen na tarayyar Turai Kaja Kallas a birnin Doha na kasar Qatar a jiya Alhamis. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, jami’an guda biyu sun tattauna inda aka kwana dangane da shirin nukliyar kasar Iran da kuma samar da hanyoyin diblomasiya don warware matsalar. Sun kuma tattaunawa dangane da SnapBack wanda kasashen turai uku Faransa Jamus da kuma Jamusa da faransa suka yi. Wanda yake nufin sake maida takunkuman MDD kan Iran kafin yarjeniyar JCPOA. Sun kuma yadda Iran zata koma bada hada kai da hukumar IAEA don ci gaba da bincike a cikin ayyukan shirin makamashin Nukliya na kasar....
Kamfanin sadarwa ta Google a halin yanzu tana aiwatar da yakin farfaganda ga Natanyahu a shafukan yanar gizo da kuma dukkan kafafen da kamfanin yake da shi don kyautata fuskar Natanyahu da kuma HKI a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, aikin wanda Natanyahu ya sayeshi da dalar Amurka miliyon 45 zai rage irin kiyayyar da ake masa a duniya da kuma gwamnatinsa. Sannan mai yuwa ya rage irin takurawa da ake masa kan kissan kiyashin da sojojinsa suke aikatawa a gaza da kuma kasar Falasdinu da suka mamaye. Daga karshe dai gwamnatin Natanyahu ya fake da farfaganda ta karya don wanke faska da hannayensa tare da amfani da kamfanin google don boye aiyukan ta’adanci...
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da sanya tarar kuɗi kan masu aikata ayyukan da suka shafi rashin ɗa’a a cikin al’umma, musamman a lokutan salla, domin kare mutunci, tsaro da kuma zaman lafiya. Sabbin matakan, wanda za a fara aiwatarwa nan take, sun shafi masu sanya kaya marasa mutunci a bainar jama’a, da masu kunna kiɗa lokacin salla, da masu bahaya ko zubar da shara a wuraren da doka ta haramta. Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13 a Borno Hisbah ta kama mai safarar mutane da mata 12 A cewar sabuwar doka, duk wanda aka kama da kunna kiɗa a lokacin salla zai biya tara ta Riyal 1,000 (kimanin Naira 390,000) a karon farko, kuma idan aka sake kama shi, tarar...
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa ya bayyana halin da Iran take ciki kan sabon zagayen tattaunawa Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi ya tabbatar da cewa, ana musayar sakonni tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, yana mai cewa maido da zaman tattaunawa da Amurka zai yiwu ne kawai bayan samun tabbacin cewa ba za a kai wa Iran hari makamancin wanda ya faru, kamar yadda ya faru a baya-bayan nan ba. A wata hira da ya yi da kafafen yada labaran Turkiyya, Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Ana gudanar da magana tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani na yanki da na kasa da...

Sakataren Kwamitin Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Tattauna Da Takwaransa Na Birtaniyya Kan Shirin Nukiliyar Iran
Babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran ya tattauna da takwaransa na Birtaniyya kan tattaunawar nukiliya da hanyoyin kawar da sabani tsakanin Iran da tawagar Turai Mai bai wa fira ministan kasar Birtaniya shawara kan harkokin tsaro, Jonathan Powell, ya tattauna kan farfado da shawarwarin makamashin nukiliyar da kuma warware hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen rikicin a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da Ali Larijani, babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran. Bangarorin biyu sun tattauna batun sake farfado da shawarwarin makamashin nukiliyar da kuma neman hanyoyin da za a bi don magance matsalar makamashin nukiliyar Iran ta hanyar tattaunawa. A cikin wannan tattaunawa ta wayar tarho da aka gudanar a yammacin yau Alhamis, bangarorin biyu...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China na Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba gudana, yana mai jaddada cewa: Iran na ba da muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China na Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba gudana, yana mai jaddada cewa: Iran na ba da muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran...
Falasdinawa 79 ne suka yi shahidai sakamakon tashin gobara da farmakin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai zirin Gaza a jiya Laraba Majiyoyin kiwon lafiya sun sanar a cikin dare cewa: An kashe Falasdinawa 79 sakamakon tashin gobara da hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ciki har da mutane 16 da ke jiran agaji. Majiyar ta bayyana cewa, an mayar da shahidai 25 zuwa Asibitin Al-Shifa, 6 zuwa asibitin Sheikh Radwan, 7 zuwa Asibitin Al-Ahli Arab Baptist, 5 zuwa Asibitin Rehabilitation Hamad, 1 Asibitin Al-Awda, 12 zuwa Asibitin Shahidai Al-Aqsa, 23 kuma zuwa Asibitin Nasser. Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun ci gaba da kai farmaki a zirin Gaza, inda...
Adadin mutanen da suka rasu a hatsarin jirgin ruwa da ya auku a yankin Malale, da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja, ya kai 60. Jirgin ruwan, wanda ya ɗauko kusan mutum 90, ya tashi daga Tugan Sule a gundumar Shagunu, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Dugga. ‘Za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 14’ Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda Mutanen da ke cikin sun tafi yin gaisuwar ta’aziyya ne, lokacin da hatsarin ya auku a ranar Talata, 2 ga watan Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 11:30 na safe. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA),...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta yi gargadin cewa sabon salon da ’yan mata suka fito da shi na karbar kudin samarinsu da nufin za su je wajensu amma su ki zuwa laifi ne da za a iya hukunta su da shi. A cikin wani bidiyo da Kakakin rundunar a jihar, Grace Iringe-Koko, ta wallafa ranar Laraba, ta ce yin hakan daidai yake da da damfara, kuma za a iya hukunta duk wacce ta aikata. Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin Kofa NAF ta hallaka ’yan ta’adda 15 a dajin Sambisa A cewar kakakin, “Me ya sa za ki karbi kudi daga wajen mutum kuma ki ki zuwa wajensa, hakan laifi ne da mai aikata shi zai iya fuskantar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wata matashiya mai shekara 20, Maryam Atiku, bisa zargin binne jaririyar da ta haifa da ranta a unguwar Nasarawa da ke Kamba a Karamar Hukumar Dandi. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, CSP Nafi’u Abubakar, ya fitar a wannan Larabar. Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 29 a Neja Dalilin da Najeriya ba ta jin tsoron matakan Trump — Tinubu Ya ce matashiyar bayan ta haifi jaririyar, ta naɗe ta a cikin wasu zannuwan atamfa guda uku, sannan ta kai ta wani daji da ake kira Malam Yaro a yankin Nasarawa, inda ta tono rami ta binne ta da ranta. Sai dai a cewar...

Firaministan Senegal: Yadda Sinawa Ke Girmama Tarihi Da Kiyaye Labarun Abubuwan Da Suka Faru Da Su Na Da Matukar Burgewa
Firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko ya bayyana a wata hira da ya yi da wakilin rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye bayar da labarun abubuwan da suka faru da su ya yi matukar burge shi. Sonko ya ce, duk kasar da ba ta iya tuna abubuwan da suka faru da ita a tarihi za ta yi matukar wahala ta dauki darasi daga abin da ya gabata, kuma tana iya saurin maimaita kura-kurai da kuma shan wuyar tashin hankalin da aka shiga a tarihi. Abin da ya yi matukar ba shi mamaki shi ne yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye labarun abubuwan...

Dakarun “IRGC” Sun Bayyana Cewa: Takunkumin Da Turai Ta Kakaba Kan Iran Daukan Fansa Kan Al’ummar Kasar
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun bayyana cewa: Takunkumin kasashen yammacin Turai kan Iran wani yunkuri ne na daukar fansa kan tsayin dakan al’ummar Iran Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Ali Muhammad Na’eini ya tabbatar da cewa: Amurka da kasashen Turai na neman daukar fansa a yakin kwanaki 12 da suka yi da al’ummar Iran mai girma ta hanyar mayar da takunkumi kanta. Na’eini ya bayyana cewa, dogaron da makiya suke da shi a kan lissafi na son abin duniya kawai ya sanya su jahilci hakikanin bangarori na karfin Iran kamar al’adun tsayin daka, ruhin jihadi da shahada, jagoranci mai hikima, imani na addini, nasarar Ubangiji, da hadin kan kasa. Na’eini ya zayyana misalan wadannan...

Qalibaf: Ya Bukaci Gwamnatocin Kasashen Musulmi Su Fito Su Yi Allah Wadai Da Ayyukan Isra’ila A Gaza
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Dole ne gwamnatocin Musulunci su dauki matakai na zahiri don dakile ayyukan kisan kare dangi ‘yan sahayoniyya a Gaza Muhammad Baqir Qalibaf, Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada bukatar da ke akwai ga al’ummar Musulmi da su yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi a Gaza ba tare da bata lokaci ba. Ya kuma yi kira ga gwamnatocin kasashen musulmi da su yi koyi da al’ummarsu da suka dauki matakai na zahiri don nuna rashin amincewa da duk wata hanyar aiwatar da kashe-kashen yahudawan sahayoniyya. A farkon taron majalisar a ranar Laraba, Qalibaf ya taya al’ummar musulmi murnar shigowar makon hadin kai, inda ya ce: A wadannan...
Wata kotu a Jihar Ekiti, ta tura wani mutum mai suna Ibrahim zuwa gidan yari bisa zargin kashe saurayin ’yarsa. Rahotanni sun ce saurayin ya ziyarci budurwarsa a gidan mahaifinta da ke kusa da Corpers’ Lodge, a kan titin New Iyin, Ado Ekiti. Da ina da iko da cikin mako biyu zan magance matsalar tsaron Zamfara – Gwamna ’Yan daba sun tarwatsa taron neman zaman lafiya na dattawan Katsina Mahaifin, wanda ba ya son dangantakaru, ya kira ’yan uwansa suka tare saurayin, inda suka yi masa dukan da ya yi sanadin mutuwarsa saboda zubar jini. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar da gurfanar da mahaifin yarinyar. Hakazalika, ya ce an gurfanar da wasu mutane biyu, kuma kotu...
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba, kasar Iran zata dauki matakan maida martani ga matakin da kasashen E3 ko Faransa, Jamus da kuma Burtania, suka dauka na maida dukkan takunkuman tattalin arziki n a MDD kafinn yarjeniyar JCPOA. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a cikin Malisar dokokin kasar a nan Tehran. Ya jami’an gwamnatin kasar Iran, da kuma kasashen Rasha da Chin duk sun bayyana cewa maida wadannan takunkuman tattalin arziki kan Iran baya bisa ka’ida kuma zalunci ne. Sannan ba tare da shawara da kowa ba kasashen uku suka dauki matakin aikawa MDD wasika wanda na sake farfado da takunkuman. Share 0 0...
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, biyar ga watan Satumban 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Ana dai yin bikin ranar ce dai da ake kira ta Mauludi a duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal, wat ana uku a shekarar Musulunci. DAGA LARABA: Yadda Mata Dake Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, ranar Laraba a madadin gwamnatin, kamar yadda Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani ta sanar. Ministan ya kuma taya ’yan Najeriya murna, inda ya bukace su da su yi koyi da kyawawan halayen Annabin na zaman lafiya, kaunar jama’a, hakuri, tawali’u...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5 da gwamnatin kasar Habasha, domin gina daya daga cikin manyan masana’antun takin zamani a duniya a garin Gode. An rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin rukunin Dangote da kamfanin zuba jari na Habasha (EIH), wanda zai baiwa rukunin Dangote damar rike hannun jarin kashi 60 cikin dari, yayin da EIH zai rike kashi 40 cikin dari. Ana has ashen cewa idan an kammala aikin, zai kasance cikin manyan masana’antun samar da takin zamani guda biyar na duniya, wanda zai rika samar da takin zamani ton miliyan uku a kowace shekara. A cewar EIH, za a kammala aikin a cikin...
Rundunar sojin Yaman ta sanar da cewa ta kaddamar ad wasu manyan hare-hare a kan wasu mihimamn wurare na tsaro da tattalin arzikin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Tun a ranar Litinin da ta gabata ta sanar da cewa za ta aiwatar da ayyukan soji biyar masu girma a kan wasu muhimman wurare da suka hada da hedikwatar tsaro, tashar wutar lantarki ta Hadera, filin sauka da tashin jiragen sama na Lod da ke Jaffa ko Tel Aviv, da kuma tashar jiragen ruwa ta Ashdod, da kuma tashr jiragen ruwa ta MSC ABY da ke arewacin tekun Bahar Maliya. An gudanar da ayyukan ta hanyar amfani da jirage marasa matuka da dama da kuma makamai masu linzami. Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya...
Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba. Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta. Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga...
A ranar Litinin 8 ga Satumba, 2025 ne gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabuwar majalisar Shurah, karkashin jagorancin gwamna Abba Kabiru Yusuf. Za a gudanar da bikin kaddamarwar ne a gidan gwamnati dake Kano. Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a 2 ga Satumba, 2025. Xi: Alakar Sin Da Rasha Ta Zama Misali Na Kyakkyawar Dangantakar Manyan Kasashe Sabuwar Ajandar Kasar Sin Ta Inganta Magance Gibin Kudi A Duniya Kafa majalisar Shurah na zuwa ne domin karfafa gudanar da mulki cikin hadin kai, da bayyana gaskiya wajen yanke shawara. Ana sa ran majalisar za ta kasance kamar wata kungiya mai ba da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata. Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa A cewarsa, “bayan samun sahihan bayanan sirri, an kama wani Salihu Umar, mai shekaru 42, ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, wanda ya shiga kasuwar shanu ta Bachaka da shanu 10 da ya sace wa wani Usman...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da ajandar mulkin duniya a taron “SCO+” na birnin Tianjin a jiya Litinin. Wannan ajanda, ta nuna hanyar da za a bi, tare da ba da jagoranci ga aiwatar da ayyukan gina tsarin mulkin duniya mai adalci da dacewa, a karkashin yanayin duniya mai fuskantar manyan sauye-sauye, da kuma jagorancin cike gibin kudi na samar da ci gaba da bunkasa. Sabuwar ajandar mulkin duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta yi magana kai tsaye kan wasu muhimman abubuwa guda uku a tsarin jagorancin duniya, wato rashin daidaiton iko, da rarrabuwar ra’ayoyi, da kuma rashin daukar matakai. Ajandar, wadda ta fitar da wasu ka’idoji guda biyar, wato tabbatar da daidaiton ikon mulkin kasa, da...
Majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 na daban suka jikkata a Gaza cikin sa’o’i 24 Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da yi tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ya karu zuwa shahidai 63,633, tare da jikkatan wasu 160,914. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta bayyana a cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullun cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a cewar alkalumman baya-bayan nan da ma’aikatar ta...
Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatu na bana da za a soma a watan Satumbar nan. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da kuma fannin fasaha. Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne da nufin rage nauyin karatu kan ɗaliban da kuma inganta tsarin koyarwa a faɗin ƙasar. Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ce ta bayyana hakan a madadin Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa a ƙarshen...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya. Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030. Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Kemi Badenoch ta shiga tsaka mai wuya kan karatun likitanci Golan zai riƙa amfani da riga mai lamba 99 domin ranar haihuwarsa ta 1999, kamar yadda ƙungiyar ta sanar. A jawabin da ya yi dangane da komawa ƙungiyar, Donnarumma ya ce yana cike da farin ciki da jin daɗi. “Na koma ƙungiya da ke cike da zaratan ’yan wasa, sannan kuma ƙungiya...
Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari. Abba ya yi wannan kira ne ta bakin wani mai fassara a taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen tattaunawa kan kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka shirya don inganta aiki. Ya ce rashin masu fassara a asibitoci alama ce ta rashin kula da kurame a jihar, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum...
An gudanar da janazar manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen 9 da suka yi shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kansu,a lokacin da suke gudanar da wani zama na gwamnati, domin bin kadun ayyukan ma’aikatun da suke jagoranta. Dubban daruruwan mutane ne dai suka halarci janazar wadda ta gudana a birnin San’a fadar mulkin kasar ta Yemen a jiya, inda aka gabatar da jawabai daban-daban, da ke kara tabbatar da aniyar al’ummar kasar Yemen wajen ci gaba da bin tafarkin wadanda suka yi shahada, domin mara baya ga al’ummar Gaza mara kariya. A nasa bangaren Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan wannan hari na wuce gona da...

Araghchi : China da Rasha sun bi sahun Iran wajen kin amincewa da yunkurin E3 na dawo mata da takunkumai
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce shi da takwarorinsa na Rasha da China sun aike da wasika ga Majalisar Dinkin Duniya, inda suka yi watsi da matakin da Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka a baya-bayan nan na yunkurin maido da takunkumin kasa da kasa kan Iran a matsayin mataki marar ma’ana. Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya wallafa a jiya a Shafin X, kwanaki hudu bayan da kasashen Turai wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015 suka sanar da kwamitin sulhu na MDD cewa, sun yi amfani da tsarin dawo da dukkanin takunkumin MDD a kan Iran. Ya ce, a cikin wasikar hadin gwiwa da suka aike wa...
Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe. Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin. An kama ɗan shekara 60 kan yi wa mai shekara 24 fyaɗe Simon Ekpa: An ɗaure ɗan Nijeriya kan laifin ta’addanci a Finland Mai magana da yawun hukumar a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya ce bisa binciken da suka gudanar, uban da ɗan sun aikata laifin ne a lokuta daban-daban. A cewarsa, Ibrahim Haruna wanda tela ne ya yi aika-aika ne a shagonsa na ɗinki, yayin...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba, yana mai jaddada cewa: Iran na daukar muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian za...
A cewar sa, yankin Arewa-maso-yamma ya samu kaso mafi girma na ayyuka da ya kai naira tiriliyan 5.97, Kudu-maso-kudu ya samu naira tiriliyan 2.41, Arewa-ta-tsakiya naira tiriliyan 1.13, Kudu-maso-gabas naira biliyan 407, Arewa-maso-gabas naira biliyan 400, yayin da Kudu-maso-yamma (ban da Legas) ya samu naira biliyan 604. Idris ya ce dukkan waɗannan yankuna suna amfana da manyan hanyoyi, layukan dogo da kuma hukumomin raya yankuna. Ministan ya ce daga cikin muhimman ayyukan da ake aiwatarwa akwai Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, da Babban Titin Sakkwato zuwa Badagiri, da gyaran layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri, da kuma Hanyar Gadar Neja ta 2. Haka kuma, gwamnati ta samar da fiye da naira biliyan 250 don ayyukan...
’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta hada jihohin Sakkwato da Kebbi da Neja. A yayin zanga-zangar a ranar Lahadi, wani daga ƙauyen Rinaye ya shaida wa Aminiya cewa, “Rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalinta da jami’an tsaro gare mu a ɗauki matakin korar mana ’yan bindigar su bar yankinmu. “Yau (Lahadi) sun jera kwana uku kullum sai sun zo sun sace...
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a wanda ya kai ga shahadar firaministan kasar Yemen da wasu jami’an farar hula da dama. A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na jinjinawa shahidai, al-Houthi ya bayyana cewa, “laifi na kai hari kan ministoci da ma’aikatan farar hula ya kara tabbatar da laifukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin,” yana mai jaddada cewa dukkan wadanda suka yi shahada suna gudanar da ayyukansu ne a fagagen da ba na soja ba. Da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalan shahidai, abokan aikinsu, da al’ummar kasar Yemen, ya tabbatar da cewa wuce gona da...
Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC). Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki a Gombe Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata Babban Daraktan Kamfanin Media Trust, Malam Ahmed I. Shekarau ne, ya bayyana wannan ci gaba. Ya bayyana hakan a matsayin abin alfahari, inda ya ce Trust Radio za ta mayar da hankali kan yaɗa shirye-shirye na gaskiya, adalci da kuma abin da ya shafi jama’a. Za a riƙa watsa shirye-shirye daga Abuja...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Muhimmancin Aiwatar Da Yarjejeniyar Da Iran Ta Cimma Da China
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya wallafa wani bangare na jawabinsa cikin harshen chinanci kan muhimmancin dangantakar Iran da China. Kididdigar ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan jagoran juyin juya halin Musulunci ya wallafa bayanansa kan kasar Iran da kuma damar da kasar China ke da ita ta taka rawa a fagen duniya da kuma wajibcin aiwatar da yarjejeniyar tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, wanda ya zo daidai da ziyarar...
Mataimakin babban kwamandan “IRGC” ya bayyana cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna yakar Iran Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Fadavi ya tabbatar da cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Iran. Duk da tsare-tsare masu yawa da kuma sanar da manufofinsu a baya, makiya sun kasa cimma wata manufa da suka ayyana a cikin yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan Iran, lamarin da ya tilasta musu amincewa da shan kashi ta hanyar amincewa da tsagaita bude wuta cikin hanzari. Fadavi ya kara da...
Ya tabbatar da cewa, an kwashe dukkan fasinjoji 618 da ke cikin jirgin cikin koshin lafiya. 20 sun samu kananan raunuka, yayin da bakwai ke kwance a asibiti amma tuni an sallame su, kuma NRC ce ta dauki nauyin biyan kudaden kiwon lafiyarsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
135-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka yi yaki kan ruwan furat, bayanda sojojin mu’awiya ya hana sojojin...
Ƙungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar Mohammed Sinwar, wanda aka daɗe ana ɗauka a matsayin jagoranta a Gaza. Wannan tabbaci ta Hamas ta bayar na zuwa ne fiye da watanni uku bayan Isra’ila ta ce ta kashe shi a wani harin sama. Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara Xi na karɓar baƙuncin taron SCO a China Hotunan da Hamas ta fitar ranar Asabar sun nuna Sinwar tare da wasu manyan shugabannin siyasa da na soji, waɗanda aka bayyana a matsayin “shahidan kwamitin soji.” Mohammed Sinwar, shi ne ƙanen Yahya Sinwar wanda Isra’ila ke zargi da jagorantar harin ranar 7 ga Oktoban 2023 a Isra’ila, rikicin da har yanzu wutarsa ke ƙara ruruwa. Kamfanin Dillancin Labaran...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa wasu daga cikin manyan jami’an kasar Yemen, tare da yin kira ga al’ummar duniya da su tinkari irin wadannan munanan ayyuka na rashin bin doka da oda. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta yi tir da wadannan ayyuka na ta’addanci, tare da jaddada bukatar daukar matakin gaggawa daga kasashen duniya don dakile aniyar yahudawan sahyuniya ta kawo hargiti a gabas ta tsakiya, wanda kai tsaye yake shafar tsaro na kasashen duniya. Ta bayyana wannan munanan aiki da cewa, ba wai kawai laifukan yaki da laifin cin zarafin bil’adama ba ne, har ma yana a matsayin ramuwar gayya...
Fadar shugaban kasar Yemen a Sana’a ta sanar da shahadar firayim minista Ahmed Ghaleb al-Rahwi tare da wasu ministocin kasar, sakamakon harin da Isra’ila ta kai a ranar Alhamis din da ta gabata. Fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta kara da cewa, wasu ministoci da dama sun samu raunuka sakamakon wannan ta’asa, kuma a halin yanzu suna samun kulawar lafiya. Duk da haka, fadar shugaban kasar ta ba da tabbacin cewa cibiyoyi za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ga jama’a ba tare da wani tsaiko ba, duk kuwa da girman Rashin da aka yi. Dangane da matsayar kasar Yemen kan batun yakin Gaza, fadar shugaban kasar da ke birnin San’a ta jaddada wa...
Shugaban mayakan RSF a Sudan Mohammed Hamdan Dagalo ya yi rantsuwar shugabatar gwamnati mai kishintar gwamnatin kasar. Sanarwar ta ce Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, wanda kuma ba kasafai ake ganinsa a kasar Sudan ba tun bayan barkewar rikici na tsawon watanni 28 tsakaninsa da sojojin kasar, an rantsar da shi ne a yayin wani biki a birnin Nyala na kasar Sudan, ko da yake kamfanin dillancin labaran Reuters ya kasa tabbatar da inda yake. Nyala, daya daga cikin manyan biranen kasar Sudan dake yankin Darfur, wanda kuma shi ne babbar tungar mayakan kungiyar RSF, kungiyar da ta nada nata firaminista da majalisar shugabancin karkashin jagorancin Dagalo. A ranar 16 ga watan Afrilu, Dagalo, kwamandan rundunar RSF ya...
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe, kayan tallafi. Darakta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta amince da fara wannan tallafi a Potiskum, inda ta samu wakilcin Abdullahi Garba, ko’odinetan ofishin NEMA na Maiduguri. An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara A cewarta, wannan mataki ya biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku a ranar 15 ga qatan Agusta, 2025. Ambaliyar ta shafi dubban jama’a kuma ta lalata gidaje da dama. Binciken da NEMA tare da wasu ƙungiyoyin agaji suka gudanar ya nuna cewa gidaje 2,557 ne abin ya...
Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya fada a ranar Asabar cewa: Kasarsa tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila da nufin kawo karshen yakin Gaza. Ya kara da cewa: Abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza ya wuce kare kai, don haka dole ne a matsa lamba kanta don kawo karshen yakin da kuma bala’in jin kai. Ya ci gaba da cewa gwamnatin mamayar Isra’ila na ruguza tsarin samar da kasashe biyu. A nata bangaren, jami’ar kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai, Kaja Kallas ta bayyana cewa: Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun dauki...
Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, yayin da sama da 20 suka ɓace a Jihar Zamfara, bayan jirgin ruwan da suka hau domin tsere wa ’yan bindiga ya nutse. Mazauna yankin da wasu jami’ai sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar. Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Wike Harin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Birnin Magaji, inda ’yan bindiga suka kai wa ƙauyuka biyu hari. Mutane da dama ne suka tsere zuwa bakin kogi, inda suka riski jirgin ruwa guda ɗaya kacal. Hakan ya sa aka jirgin da mutane sosai, lamarin da ya sa ya nutse a cikin ruwa. “Babban yayana...
Shi yasa ta ce duk kowa daga ciki al’umma yana da irin gudunmawar da zai bada wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar da zai tafi makaranta, ta kuma kara jaddada tsarin nastressing TaRL yana bada dama ga Jihohi su samu kira da sa duk masu ruwa da tsaki. A tasu gabatarwar ta hadin gwiwa, Dakta Goni Shetima,wanda shi horarwa ne ta bangaren tsarin TaRL,da Malam Abdulrahman Ibrahim Ado, kwararre jami’in ilimi na UNICEF, sun bayyana cewa tsarin an fara gudanar da shi a karamar hukumar Alkaleri. Kamar yadda suka ce, an fara tsarin ne da makarantu 190, ‘yan makaranta 10,865, sai kuma Malaman makarantar gwamnati 290. Shi ma darektan shiyya na hukumar (UBEC), wanda Abdulsalam Abubakar ya...
Jihar Legas, mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta samu ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira Turkiya 3.9 a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa. Ayyukan da gwamnatin ta ba wa Jihar Legas ya zarce jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas baki ɗaya, waɗanda suka haɗa da jihohi 18. Rahoton binciken da wakilanmu suka gudanar ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da suka gabata, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 3.9 a jihar Legas. A cewar rahoton, cikin lokaci guda, FEC, wadda Shugaban Ƙasar ke jagoranta, ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 5.97 ga Kudu maso Yamma,...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin kama ma’aikatan Mosad na HKI a lardin Khorasan Razavi da ke arewa maso gabacin kasar, wadanda suka taimakawa HKI a kan hare-haren da ta kaiwa kasar na kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto sanarwan da dakarun suka bayar a jiya Jumma;a na cewa, bangaren leken asiri na su ya sami nasarar kama wasu mutane 8 a cikin lardin wadanda suke da hannu dumu-dumi a cikin yakin kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata. Kuma suna aiki kai tsaye da HKI a cikin yakin. Labarin ya kara da cewa gungun mutanen guda 8 suna aiki...
A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa da kwarewa wajen gano yadda aka boye kwayoyin. “Wannan lamari ya nuna jajircewar hukumar wajen katse hanyar rarraba miyagun kwayoyi da tabbatar da tsaron al’umma.” Ya rawaito kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Malam Abubakar Idris-Ahmad, yana yaba wa jami’an hukumar bisa jajircewa da himma wajen gudanar da aikin. Idris-Ahmad ya kuma yaba wa shugaban hukumar NDLEA na kasa, Tsohon Birgediya-Janar mai ritaya, Mohamed Buba-Marwa, bisa goyon baya da jagoranci da yake bayarwa. “NDLEA a Jihar Kano ta dage wajen aiwatar da manufarta ta kawar da miyagun kwayoyi a jihar, tare da gode wa hadin kai da goyon bayan jama’a wajen cimma wannan buri,” in ji shi. A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu. Shugaban ya kuma koka kan yadda aka shafe wadannan shekarun masu yawan gaske, ba tare da an yi masu wani gyara ba. Ya buga misali da kananan Tashoshin Jiragen Ruwa na kasasehe kamar na Togo, Côte d’Iboire da Ghana, wanda suka kasance, Tashoshin Jiragen Ruwa da manyan Jiragen Ruwa ke sauka. A cewar Shugaban irin lalacewar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar suka yi, abu ne, da ya...
Jack Neriya, tsohon shugaban hukumar leken asirin Isra’ila a Syria da Lebanon, ya yi gargadi game da masu tunann cewa ta yi rauni, yana mai jaddada cewa “kungiyar ta sake gina karfin soji kuma ba ta da niyyar yin watsi da makamanta.” A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin, Neriya ya ce, “Tun daga watan Nuwamba, Hezbollah ta sake tsara sahunta, ta dawo kera jiragen sama marasa matuka da sauran makamanta, tare da jaddada kudurin ta na ci gaba da yin amfani da makamanta.” Ya kara da cewa, bayyanar babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem a bainar jama’a a cikin kayan soji na nuni da daukar matakin da ya dace, musamman ma a lokacin...
Shaidu sun ce jirgin cike yake da mata, maza, da yara, kafin ya kife a tsakiyar ruwa. Wasu daga cikin fasinjojin sun yi nasarar yin iyo inda suka tsira, amma har yanzu ba a gano da dama ba. Al’umma sun daɗe suna zargin irin waɗannan hatsari na faruwa ne saboda ɗauke fasinjoji fiye da ƙima, rashin saka rigar iyo, amfani da jiragen ruwa marasa inganci, da kuma rashin bin ƙa’idojin tsaro. Duk da wannan, gwamnati ba ta ɗauki matakan tsaro ba. A halin yanzu, magidanta a Shagari da ƙauyuka maƙwabta na cikin tashin hankali suna jiran labari game da ‘yan uwansu da suka ɓace, yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Jibrin Ado bisa laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita a unguwar Gerawa da ke jihar. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne a ranar Alhamis daga wata sanarwa ta manhajar X ta wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan jihar An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa A cewarsa, Ado ya aikata wannan aika-aika ne tare da wasu masu laifin a ranar Talata. Waɗanda suka haɗa da: Musa Kwalle da Dan Abba da Sule Musa da wani Arrow dukkansu daga ƙauyen Gerawa. Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 26 ga watan Agusta da misalin ƙarfe...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙara kuɗin fasfo. Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta ƙara kuɗin fasfo mai shafi 32 zuwa Naira 100,000, yayin da mai shafi 64 ya koma Naira 200,000. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan jihar An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa Obi, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, inda ya ce wannan ƙarin ba adalci ba ne duba da halin matsin tattalin arziƙi da ake fuskanta. “Wannan gwamnati kullum na ƙara jefa mutane cikin wahala a maimakon ta sauƙaƙa musu rayuwa,” in ji shi. “An ƙara kuɗin fasfo sau uku cikin shekaru biyu...
Ambaliyar ruwar da ta biyo bayan mamakon ruwan saman da aka tafka ta raba kauyuka shida da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato da saurann yankunan jihar. Kauyukkan da ambaliyar ta shafa su ne Makuwana da Dangawo da Faru da Gumbula da ’Yan Faruna da kuma Magajin Dawaki, sannan ta lalata hanyar da ta hada kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni. An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ Tuni dai Majalisar Dokokin Jihar ta yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da ke kula da harkokin ruwa da su dauki matakin da ya dace kan wadanda lamarin ya shafa. Hakan...
Bayan sanarwar da E3 (Faransa, Jamus, da Burtaniya) suka yi na haifar da hanyar da za ta kai ga dawo da takunkumin da aka kakaba wa Tehran kan shirinta ma nukiliya, Majalisar Dokokin Iran ta tsara tare da gabatar da wani kudirin doka na gaggawa da ke ba da shawarar ficewa gaba daya daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Hossein-Ali Haji-Deligani, Mataimakin Shugaban Kwamitin Mataki na 90 na Majalisar Dokokin Iran, ya tabbatar da cewa za a shigar da kudirin zuwa tsarin majalisar a rana mai zuwa sannan a sake duba shi a wani budadden zama. “Kamar yadda muka fada a baya, wadannan kasashe sun riga sun fara aiwatar da takunkumin da aka kakaba mana. Babu wani sabon abu...
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham, ’yan mintoci kalilan bayan fara tafiyar. Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” Injin jirgin da kuma tarago biyu da ke biye masa sun samu mummunar illa, a yayin da ragowar taragu shida...
Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar. Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki. Masu shirya taron sun kara da cewa dalilin da ya sa suka zabi masarautar Daura domin shirya wannan taron shine saboda kasancewar Daura tushen Hausa da al’adu hausawa. Haka kuma an shirya wani tattaki daga Katsina domin zuwa Daura karkashin hukumar raya al’adu ta jihar Katsina inda aka shafe kwana biyu ana tafiya akan dawakai zuwa garin na Daura duk a cikin shirye-shiryen bikin ranar Hausa ta...
Annabi (SAW), shi ne farkon wanda kasa za ta tsage wa ya tashi a ranar Alkiyama, shi ne farkon wanda zai shiga Aljannah, shi ne wanda Allah ya kebanta da tsani da wasilah, shi kuma ya kebanci muminai masoyansa da ita. Allah ya girmama Manzon Allah (SAW) da abin da bai girmama wani dan Adam da shi ba. Ya daukaka ambatonsa, ta inda ya hada sunansa da sunan Annabi (SAW). Indai an kira sunan Allah, sai an kira sunan Annabinsa. Allah ya yi masa budi (Fatahi) na Zahiri – Sulhu a Hudaibiyya, Fat’hu Khaibara, da Fat’hu Makkah; da Badini – Fatahi a Sifa, Fatahi a Suna da Fatahi a Zati. Allah ya gafarta wa Manzon Allah (SAW), ya tafiyar da...
Daraktan Tsara Tafiye-tafiye na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya maka jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar a gaban kotu, bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar kiransa da ɓarawo. A kwanakin baya ne dai jaridar ta zargi Daraktan da karkatar da kudade har sama da Naira biliyan shida da rabi zuwa asusunshi, kodayake daga bisani Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya wanke shi daga zargi, inda ya ce ba satar kudaden aka yi ba, na aiki ne. Magauta sun sa NNPCL a gaba – Ojulari Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso To sai dai jaridar ta sake yin labari mai taken “Gwamnan Kano ya kare hadiminsa barawo, ya ce gwamnatin Ganduje ma ta...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dangantaka tsakanin Iran da China na dauke da dabarun manufofi masu kyau Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Kasar Iran na da sha’awar gudanar da hadin gwiwa mai ma’ana da kasar China, musamman a fannin raya dabarun kiyaye hanya, yana mai bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin kyaukyawar dabara. Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Alhamis don daidaita yin nazari kan fannoni daban-daban na dangantaka da hadin gwiwa, da kuma bayyana ajandar ziyarar shugaban kasar China. Taron ya samu halartar manyan jami’ai da shugabannin hukumomin zartarwa da abin ya shafa. A yayin wannan taro, an tattauna muhimman batutuwan da suka shafi...
Jami’in kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: A shirye suke su ci gaba da yaki na dogon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila Jami’in kungiyar Ansarullah ta Mabiya Huthi ta kasar Yemen Mohammed al-Bukhaiti ya bayyana cewa: A shirye al’ummar Yemen su ci gaba da yaki na tsawon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila, kuma suna farin ciki da arangama kai tsaye da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa, za a ci gaba da daukar matakan soji na goyon bayan Gaza muddin gwamnatin ta ci gaba da yakin da take yi a Gaza. Ya yi nuni da cewa harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan birnin Sana’a ba zai shafi goyon bayan da al’ummar Yemen ke yi ga...
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan mummunan sakamakon Shirin Isra’ila na fadada ayyukanta a birnin Gaza Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi gargadi kan mummunan sakamakon matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila zata dauka na fadada ayyukan soji a birnin Gaza, yana mai yin Allah wadai da manufofin fadada gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan mamaya a yankunan gabar yammacin kogin Jordan. A jawabin da ya yi wa manema labarai a jiya Alhamis, gabanin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a hedkwatar Majalisar dake birnin New York, Guterres ya bayyana cewa, matakin farko da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka na kwace birnin Gaza ya sanar da wani sabon yanayi mai hadari. Ya kara da cewa “fadada...

Baki Kusan 50 Daga Kasashe 30 Na Turai Za Su Halarci Bikin Tunawa Da Nasarar Yakin Turjiyar Sinawa Kan Zaluncin Japanawa
A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika shekaru 80 da samun nasara a yaki da kutsen Japan da yaki da mulkin danniya a duniya. Wannan ya nuna niyyarsu ta hada hannu wajen tunawa da tarihi da kiyaye zaman lafiya da adalci. Guo ya jaddada cewa, kasar Sin ta shirya bikin ne da nufin tunawa da tarihi da magabata, da kiyaye zaman lafiya da ma tabbatar da makoma mai kyau ga bil...
Nafisa wacce ta wakilci Nijeriya a karkashin Kwalejin Tulip International ta Nijeriya, ta buge abokan karawarta fiye da 20,000 daga kasashe 69, ciki har da kasashen Turanci. Gasar ‘TeenEagle’ babbar gasa ce ta duniya wacce ke bibiyar ƙwarewar ɗalibai cikin harshen Turanci, kaifin basira, da ƙwarewa a salon magana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanadiyyar ambaliyar ruwa a gonaki amfanin gona na miliyoyin Naira ne suka salwanta inda ɗaruruwan filayen noma suka shefe da ruwa a Jihar Taraba. Kodayake, ba a bayyana ko an sako ruwa daga Logdo Dam ba ne daga jamhuriyar Kamaru ba, amma kogin Benuwe da ke Taraba ya yi ta malala daga gaɓarsa wanda ya yi sanadin ambaliya da lalata ɗaruruwan filayen noma. ACF ta yi Allah-wadai da rushe kasuwar Alaba Rago Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara Daily Trust ta gano cewa ruwan ya fara ƙaruwa a kogi a ’yan kwanakin da suka gabata, kuma a yanzu kogin ya yi ta malala a gefan koguna inda ya haddasa ambaliya a faɗin jihar. Ambaliyar...
Gwamnatin Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary International sun ƙaddamar da shirin aikin jinya domin rage mace-macen mata da yara a faɗin jihar. Shirin da aka gudanar a Ƙananan hukumomi uku da suka haɗa: Gombe da Kaltungo da Yamaltu-Deba, inda aka yi wa jama’a gwaje-gwaje, jinya da wayar da kai a unguwannin Yelenguruza da Kagarawal. An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000 Shugaban Rotary Reproductive, Maternal and Child Health a Nijeriya, Farfesa Emmanuel Adedolapo Lufadeju, ya bayyana cewa fiye da mutum 120 aka duba a unguwar Kagarawal kaɗai, inda aka samu kashi 70 cikin 100 sun kamu da zazzaɓin cizon sauro. Ya ce, tun daga...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya bayyana cewa: Shirin dawo da takunkumi kan Iran za shafi mu’amalar Iran da IAEA Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazim Gharib-Abod yayin da ya dawo daga shawarwarin karshe na shawarwarin da aka yi tsakanin Iran da tawagar kasashen Turai uku a birnin Geneva, ya bayyana cewa: A cikin wannan zagaye na shawarwarin, Iran ta bayyana a fili ga kasashen Turai cewa, ba su da hurumin aiwatar da doka ta yadda za a iya sake dawo da takunkumi da wa’adinsa ya kare kan kasar Iran, kuma babu wata hujja ta shari’a kan matakin...
Rahoton yahudawan sahayoniyya ya tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa dakile hare-haren dakarun Yemen Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Jerusalem Post ta bayyana a cikin wani rahoto na baya-bayan nan cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fama da babbar matsala ta soji da tsaro, bayan da ta kasa dakatar da hare-haren da Yemen ke kai mata hari da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki tun daga ranar 19 ga Oktoban shekara ta 2023. Jami’an gwamnatin mamayar Isra’ila sun bayyana bangaren Yemen a matsayin “wanda ya fi kowa hauka a yankin,” suna masu gargadin cewa shiga fafatawar da suke yi da su zai haifar da mummunan sakamako ga haramtacciyar kasar Isra’ila, ganin yadda suke ganin dakarun Yemen...
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa Birtaniya, Faransa da Jamus suna shirye-shiryen mayar da takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran a shekarun baya. Kasashe uku na Turai, da aka fi sani da E3, sun gana da jami’an Iran a ranar Talata a wani abin da aka bayyana a matsayin dama ta karshe na ceto huldar da ke gabansu na yin amfani da batun yarjejeniyar nukiliyar 2015, wanda wa’adinsa zai kare a tsakiyar watan Oktoba. Duk da cewa jami’an diflomasiyyar Turai sun yi iƙirarin cewa tattaunawar ba ta samar da hanyoyin warware batun kamar yadda suke bukata ba, amma Tehran ta nanata cewa tana nan a shirye don tattaunawa mai ma’ana, muddin aka mutunta haƙƙinta da...
A lokacin ziyarar, ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da sauran manyan jami’an ƙasar. Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda biyar da suka shafi sufurin jiragen sama, harkokin waje, kimiyya da fasaha, da kuma noma, da wasu muhimman fannoni a ci gaban Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindigar da suka sace wani mutum, matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa. Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda. Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi An sace su ne a gidajensu da ke Filin Canada Quarters a Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina da safiyar ranar Talata. A yayin kai harin, wani ɗan sa-kai mai shekara 25 mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ceto su. Wani ɗan uwan ma’auratan ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar...
Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci tare a tsakanin Sinawa da kuma kwarya-kwaryan harkokin da ake yi a gefen wasu tituna bisa tsari. Baya ga bunkasa tattalin arziki, wannan dabara tana samar da yanayi mai dadi da faranta ran jama’a. Shi ma birnin Shanghai ba a bar shi a baya ba a kan wannan sabga, inda shi kuma ya mayar da hankali a kan nishadantarwa ta fuskar al’adu. Birnin ya...
Shugaban hukumar kula da jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya ce ya ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da ya auku a ranar Talata. Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na safe bayan jirgin ya taso daga Abuja zuwa Kaduna. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno ASUU: Malaman Jami’ar FUK sun yi zanga-Zanga kan rashin cika musu alƙawura Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels a yau Laraba, Opeifa ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen binciken abin da ya haddasa lamarin. “Bayan neman gafarar ’yan Najeriya, a matsayina na shugaban hukumar, na ɗauki alhakin duk abin da ya faru,” in ji shi. “Ba...
Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin hanzarta aiwatar da ci gaban Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar kere-kere da tattalin abinci don samun nasarori irin na sauran ƙasashe masu tasowa kamar Brazil. A yayin da yake jawabi a ranar Talata a lokacin da ya gana da wasu ‘yan Nijeriya mazauna kasar Brazil, shugaba Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kawo sauyi ta hanyar kere-kere, gyare-gyare, da kuma samar da ci gaba mai dorewa. Sin Da Kasashen Afirka Za Su Rubuta Sabon Babin Hakkin Dan Adam Bisa Ci Gabansu NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi “Dole ne mu sanya Nijeriya a gaba wajen ci gaban Afirka, ta hanyar amfani da fasahar kere-kere, tattalin abinci,...
Ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya bayyana jin dadinsa ga hadin kai da goyon bayan Iran ga kasarsa A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Iran, ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya yabawa irin hadin kai da goyon bayan Iran ga ‘yancin kai, yana mai jaddada aniyar Iran na kare ta daga barazanar Amurka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna da takwaransa na kasar Venezuela Ivan Gil Pinto ta wayar tarho game da alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaban da ake samu a yankin Caribbean. A cikin wannan kiran, Ministan Harkokin Wajen Venezuela ya ba da rahoto kan abubuwan da ke faruwa a yankin Caribbean bayan karuwar barazanar Amurka da...
Rasha ta ba da shawarar tsawaita kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran Mataimakin wakilin dindindin na kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Dmitry Polyansky ya sanar da cewa, Rasha ta gabatar da shawarwarin a Majalisar Dinkin Duniya na tsawaita sahihancin kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran. Tashar talabijin ta Russian Today ta ruwaito cewa: Polyansky ya shaida wa manema labarai cewa: “Wannan ba batun sassauta takunkumi ba ne na tsawon watanni shida, amma a maimakon haka, a tsawaita kuduri mai lamba 2231. A gaskiya ma, Rasha da Chana, a matsayin masu kula da shirin hadin gwiwa na shirin (JCPOA), suna son ba da karin sarari ga diflomasiyya da...
Uzodimma ya ce ƙarin albashi zai inganta rayuwar ma’aikata, sannan ya bunƙasa tattalin arziƙin jihar. Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida sun ƙaru daga Naira miliyan zuwa sama da Naira biliyan uku a kowane wata, yayin da bashin jihar ya ragu daga sama da Naira biliyan 280 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 100. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa cire tallafin mai, yana cewa duk da ya jawo tsadar rayuwa, amma ya ƙara yawan kuɗin da ake raba wa jihohi kuma ya bai wa gwamnati damar yin sauye-sauye. Gwamnan ya ƙara da cewa daga ranar 27 ga watan Agusta, gwamnati za ta fara biyan kashin ƙarshe na kuɗaɗen fansho da ake bai wa tsoffin ma’aikata,...
Haka kuma, a wani samame daban da rundunar ta kai a ranar 15 ga watan Agusta, 2025, ‘yansanda a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu sun yi artabu da ‘yan bindiga a kusa da garin Dankade. Sun ceto mutum biyu da aka sace; Tukur Bello da Isyaka Abubakar, waɗanda aka sace a dajin Gairi na Jihar Zamfara a ranar 9 ga watan Agusta yayin da suke kiwon shanu. ‘Yansanda sun ce sun ƙwato makamai da harsasai daga hannun ‘yan bindigar, tare da alƙawarin ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Opeifa ya kara da cewa, tuni tawagar kwararru daga Hukumar, jami’an Hukumar Binciken Tsaro ta Nijeriya (NSIB) da sauran hukumomin da abin ya shafa suka isa wurin domin gano musabbabin wannan matsala da kuma tabbatar da daukar matakan kariya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi. Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi. Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya yi hastari a hanyar Kaduna-Abuja Ya ce an haramta gudanar da al’adun gargajiya irin su Shadi, Sharo, Garaya da kuma shagulgulan wannan zamani kamar Kauyawa Day, Gala, DJ, Aloba da sauransu a bukukuwan aure. Isah ya ce an ɗauki waɗannan matakan ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda abubuwa na rashin tarbiyya da tayar da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarihi ba zai yafe jinkirin yin Allah wadai da bala’in Gaza ba Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: “Al’umma ta tuna cewa bala’in Gaza bai shafi musulmi kadai ba, wannan lamari ne na gwaji na lamiri na dukkanin bil’adama, don haka suna kira ga dukkanin al’umma ba tare da la’akari da addini ko yanayin kasa ba, da su tsaya a bangaren bil’adama, adalci da mutunci, wato a bangaren dama na tarihi.” Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen taron baje kolin na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, inda ya yi jawabi ga...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tun Bayan Barkewar Yaki Da Iran Babu Wata Hulda Tsakaninta Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tun bayan barkewar yakin da Iran, babu wata hulda da ta hada ta da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya jaddada cewa: “Turawa za su iya taka muhimmiyar rawa a shawarwari,” yana mai bayanin cewa: “Tun bayan barkewar yaki da Iran, kasar Iran ta daina yin mu’amala da Amurkawa, amma tana ci gaba da hulda da Turawa ko da a lokacin da ake tsaka da yakin.” A wata hira da jaridar Süddeutsche Zeitung ta Jamus dangane da shawarar da Turai ta gabatar na tsawaita wa’adin aiki da hanyar da za a bi wajen ganin an dawo da takunkumin majalisar dinkin duniya kan Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen...
Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina. An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa, shekaru arau-aru. Mahaya dawaki da sauran mahalarta bikin daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje da mazauna garin Daura sun fara tururuwa zuwa filin bikin, wanda zai samu. An kuma shirya gudanar da gagarumin hawan daba a Fadar Sarkin Daura, albarkacin zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 10. A wannan ranar ake cika shekara 10 da fara wannan gagarumin biki,...
Mataimakin Ministan harkokin wajen Iran da takwarorinsa na Faransa, Jamus, da Birtaniyya za su gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawa a birnin Geneva na kasar Switzerland, a daidai lokacin da kasashen uku ke barazanar aiwatar da abin da ake kira tsarin dawo da takunkumin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya fada a ranar Litinin cewa, za a koma yin shawarwari tsakanin wakilan Iran da E3 a ranar Talata. Ya ce za a gudanar da taron ne a matakin mataimakan ministocin harkokin waje da daraktocin siyasa. Hakan na zuwa ne bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da babban wakilin kungiyar EU mai...