2025-07-09@10:05:29 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1343

«Wannan saboda»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    An watsa shirin talibijin mai taken “Yawon bude ido a Tuscany” a Florence na Italiya, da babban rukunin gidan radiyo da talibijin kasar Sin CMG da hukumar yawon bude ido ta yankin Tuscany na Italiya suka tsara da kuma gabatar cikin hadin gwiwa. Shugaban CMG Shen Haixiong da babban jami’in hukumar sun shaida bikin gabatarwar, kuma sun yi musanyar ra’ayi mai zurfi game da daukar shirye-shirye cikin hadin gwiwa da gabatar da albarkatun yawon bude ido da kiyaye al’adu da sauransu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
    Ofishin kula da aikin harba kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ba da labari cewa, jiya Alhamis da karfe 9 da mintuna 29 na dare agogon Beijing, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20, wato Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie sun cimma nasarar fitowa daga akwatin gwaji na Wentian, yin tattaki a waje na tsawon sa’o’i 6.5, da kuma komawa akwatin, bisa taimakon na’urori masu hannun injin dake tashar sararin samaniya da jagorancin masu nazarin kimiyya da fasaha dake doron kasa. Yayin da suke aiki a waje, Chen Dong da Chen Zhongrui sun cimma nasarar hada na’urorin kiyaye tashar sararin samaniya daga sassan wasu na’urorin da aka daddasa a sararin samaniya, da binciken na’urorin dake waje...
    Ya kara da cewa, babban makasudin kafa cibiyoyin da kudaden jama’a shi ne bunkasa masana’antu, da rage bukatar musayar kudaden waje, da samar da fa’idoji masu yawa ga kasar nan. Idu ya ce IDCs, musamman Cibiyoyin shiyyoyi hudu, sun cika da manyan injina don yada ilimin fasahar masana’antu da fasahar da za su yi tasiri matuka kan yunkurin kasar na samar da masana’antu. Ya bayyana damuwarsa cewa, “A tsawon shekaru, kusan dukkanin IDCs, ma’aikata da kayan aiki a yi asarar su kuma wasu kayan aikin sun daina aiki. “Duk da cewa gwamnatin tarayya ta mika wadannan cibiyoyi ga hukumar kula da masu kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN) tsawon wasu shekaru a yanzu, babu wani abin da aka yi gaba daya...
    Haka shi ma, shugaban ADC, Cif Ralph Okey Nwosu, ya karyata amincewa da ADA, yana mai cewa batun zama jam’iyya kawance lokaci ya riga ya shude. Ya ce sake bijiro da kawance a hukumance ya faru ne wannan makon, bisa ga shawarar daga dukkan masu ruwa da tsaki. A cewar wani rahoto, NNCG ta yi rajistar ADA a hukumance ga INEC. Wasikar neman rajistar ADA daga INEC an sanya hannu a kai daga shugaban kungiyar na wucin gadi, Cif Akin A. Rickets, da sakataren kungiyar na wucin gadi, Abdullahi Elayo. Hadakar ta kuma gabatar da takardu masu muhimmanci, daga cikin su akwai kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka bayar da manufifinra da tambari da kuma bayanan taron kafa ta. Wasikar...
    Ya kuma yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa ‘yansanda na taimakawa wajen magudin zabe, yana mai bayyana irin wadannan zarge-zarge a matsayin mara tushe, tare da cewa aikin ‘yansanda a lokacin zabe ya takaita ne kawai wajen samar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya. “Mu ba ’yan bangar siyasa ba ne, mu kamar alkalan wasa ne, aikin ‘yansanda ya takaita ne kuma ya ta’allaka ga samar da tsaro a lokacin zabe, gwargwadon yadda ya kamata, ba za mu yi zabe ba, jama’a ne za su kada kuri’a, INEC ta kidaya, muna sa ido. “Kuma wannan ita ce matsayarmu, sannan kuma hanyar da za a bi domin cimma nasara ita ce, sake sabunta hadin gwiwa tsakanin hukumomi,...
    Misali, a lokutan hare-haren, an kone gidaje da dama, inda wasu ahali ma, wanda yawansu ya kai, har zuwa 15, aka shafe su, daga doron kasa, a lokacin da suke kan bacci, a gidansu. Wasu daga cikin wadanda suka tsallake Rijiya da baya daga hare-haren na ‘yan ta’addar, sun bayyna yadda ‘yan ta’addar, suka cinnawa wasu shaguna da ke a wata kasuwa, da ka mayar a matsayin wajen kwanan, ‘yan gudun hijira, wuta. Duk da kokarin da wasu matasa da kuma kokrin jami’an tsaro na dakile maharani, hakan ya faskare su, hatta wani daya daga cikin jami’in tsaro da aka tura wanzar da tsaro, ya rasa ransa. Duk a 2025, a watan Afiiru an kai hare-hare a Logo da Ukum,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun. Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?...
    Albarkacin cika shekaru 55 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Italiya, an shirya bikin kaddamar da shirin talibijin mai taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” da CMG ya gabatar, a jiya Laraba a birnin Rome, hedkwatar kasar Italiya. Za a fara watsa wannan shiri a kafofin yada labarai na kasar fiye da 30.   An dauki da kuma tsara wannan shiri ne a garin Zhengding na lardin Hebei da Xiamen na lardin Fujian da Hangzhou na lardin Zhejiang da kuma Dunhuang na lardin Gansu da sauran wuraren da Xi Jinping ya taba kai rangadi ko aiki a can, don yin karin haske kan kokarin da Sin take yi wajen zakulo mafarin al’adun Sinawa, da kiyaye kayayyakin al’adu da sauran...
    Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya sa ake samun jituwa a tsakanin al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Saboda haka, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi, a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai-daya, inda za a dinga rage gibin dake tsakanin kasashe, da na zaman rayuwar al’ummu daban daban, ta yadda za a iya daidaita matsalolin da dan Adam ke...
      Bello, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muawiyah Yusuf, ya bayyana matukar bacin ransa da alhininsa kan wannan mummunan harin.   Sanata Bello wanda kuma tsohon gwamnan jihar Neja ne, ya yi jinjina ga sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, inda ya bayyana su a matsayin jarumai na kasa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare zaman lafiya da ‘yancin Nijeriya.   Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasu, yana mai addu’ar Allah ya kara musu lafiya, ya basu hakurin juriya da irin wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Ɗaya daga cikin baƙin da suka tafi ɗaurin aure daga Zariya, Abbas Rufa’i, ya bayyana yadda ya kuɓuta daga harin da wasu matasa suka kai musu a Ƙaramar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato. A cewarsa, “Da muka tsaya a hanya domin yin tambaya, na fito daga motar domin neman hanya. Amma sai na ga yadda mutanen da ke wajen suka fara mana wani irin kallo. Gwamnatin Gombe za ta sayi takin N8.8bn don tallafa wa manoma 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi “Na ji ɗaya daga cikinsu yana cewa, ‘a kashe su gaba ɗaya, a ƙone motar.’” Rufa’i ya ƙara da cewa, “Na cire rigata, na shiga cikin daji har na sai da na samu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Borno (PPRO), Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, ta ce an kwashe gawarwakin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na jihar da ke Maiduguri. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto.   Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara wajen yaɗa labaran ƙarya domin tayar da ƙura a intanet.   “A yayin tattaunawa da manema labarai kai tsaye a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ƙudirinsa na ɗaukar nauyin kasafin kuɗi, inda ya tabbatar da cewa bai karbi lamuni na cikin gida ko na ƙasashen waje ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana mulki.   “Amma abin ya ba mu...
    Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar, Abdullahi ya nuna matukar damuwarsa kan kisan da aka yi wa matafiyan a ranar Juma’a, a lokacin da suka bata kan hanyarsu a yayin da suke tafiya don halartar wani daurin aure a karamar hukumar Mangu.   Ya ce, wadanda aka kashen, ba su dauke da wani makami, kawai suna kan hanyarsu ne ta zuwa daurin aure, wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai musu hari tare da kashe su, lamarin da ya jefa ‘yan uwan matafiyan cikin jimami. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Jibrin Barau, ne ya sanar da kudirin bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan samar da kayayyaki.   Adeola ya ce, karin wa’adin ya zama dole domin baiwa gwamnatin tarayya damar kammala wasu manyan ayyuka da suka samu jinkiri sakamakon karancin kudaden shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar 23 ga wata, Kirsty Coventry, wacce ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics ta kasa da kasa kwanan nan, ta yi hira ta musamman da wani shirin gidan talabijin na CCTV mai lakabin “High-End Interview” a birnin Lausanne na kasar Switzerland. Wannan ita ce hira ta farko da ta yi da kafar yada labarai tun bayan da ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics na duniya. Coventry ta ce ya zama wajibi a kiyaye kima da kuzarin wasannin motsa jiki na Olympics, tare da kara kiyaye su da kuma karfafa su. Ta ce, tana fatan yin mu’amala mai zurfi da dukkan masu ruwa da tsaki a watanni masu zuwa, tare da haduwa tare wajen tsara fasalin aiki na...
    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da gidauniyar Milano Cortina 2026, wanda aka dorawa alhakin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina ta shekarar 2026 dake tafe. Yayin sanya hannu kan yarjejeniyar, sassan biyu sun amince su zurfafa hadin gwiwa a sassan yayatawa, da tsara ayyukan watsa gasar ta Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina, tare da aiwatar da musayar jami’ai. Sakamakon wannan hadin-gwiwa, CMG ya samu ikon watsa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina dake tafe a shekara mai zuwa a hukumance. An kafa gidauniyar Milano Cortina 2026 a watan Disamban shekarar 2019, domin ya tsara, da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Batun sauya sheka da ke faruwa a cikin tsarin siyasar Nijeriya, Jega ya kira a hana sauya sheka ga wadanda aka zaba a bangaren zantarwa da kuma ‘yan majalisa. Ya kuma yi kira ga jami’an INEC a matakin tarayya, da na jihohi su shirya gudanar da zaben cike gurbi da zarar an samu labari game da sauya sheka. Ya ba da shawarar cewa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje su dunga kada kuri’a a zaben shugaban kasa, kuma ya yi kira a tsaurara dokoki kan kudaden kamfen ciki har samar da hukumar da za ta sa ido kan aiwatar da hukunci. Jega ya yi nadama da cewa daya daga cikin manyan kalubalen da Nijeriya take fuskanta shi ne,...
    Wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Alƙalin Babbar Kotun Jihar Bayelsa, Ebiyerin Omukoro. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Asabar a unguwar Ekeki, kusa da babban titin Melford Okilo a Yenagoa, babban birnin jihar. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar ’yan ɗaurin auren da aka kashe a Filato Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen sun isa a cikin mota ƙirar Hilux, sanye da baƙaƙen kaya. Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, maharsn sun kutsa kai gidan cin abincin da alƙalin ke ciki kuma suka tilasta masa shiga motarsu. Har zuwa yanzu, ba a san inda suka kai shi ba, kuma babu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce Sin ta yi matukar Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kasar Iran, tare da jefa bama-bamai kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar kasar, dake karkashin kulawar hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA a takaice. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan ne a Lahadin nan, lokacin da yake tsokaci kan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare kan cibiyoyi uku na nukiliyar kasar Iran. Jami’in ya ce matakin Amurka ya yi matukar keta makasudi, da ka’idojin MDD da dokokin kasa da kasa, ya kuma ruruta yanayin rashin tabbas da ake ciki a yankin Gabas ta...
    Trump ya ce hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lallai zai kara rura wutar rikici a ci gaba da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila.   Sai dai ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai da cewa “abin takaici ne” sannan ya ce Iran ta tanadi “dukkan zabin kare ‘yancinta”, yana mai jaddada cewa Amurka za ta fuskanci “tsauraran sakamako”.   Araghchi ya kara da cewa, Amurka ta keta kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.   Bugu da kari, wani dan Majalisar kasar Iran, ya kara da cewa, “babu wani mummunan lahani...
    Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya. “Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi. Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya...
     Juma’a, 15 ga Agusta  Liberpool bs Bournemouth   Asabar, 16 ga Agusta  Aston Billa bs Newcastle   Brighton Bs Fulham   Nottingham Forest bs Brentford  Sunderland bs West Ham   Tottenham Bs Burnley   Wolberhampton Wanderers bs Manchester City   Lahadi, 17 ga Agusta  Chelsea bs Crystal Palace   Manchester United bs Arsenal  Litinin, 18 ga Agusta  Leeds Bs Eberton    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bayan karar, lauyan masu shigar da kara, Abdulhamid L. Tukur, ya kira Nnadikwu Izuchukwu Collins, wani jami’in binciken EFCC, domin ya gabatar da gaskiyar lamarin. Collins ya shaida wa kotun cewa wasu gungun masu zuba jari sun mika koke ga hukumar EFCC a ranar 21 ga Oktoba, 2022, kan FARM360 da MCBHADMOS Trans-Atlantic Trade Limited, bisa zargin cewa kamfanonin sun yaudare su wajen saka hannun jari a harkar noma da kasuwanci tare da “alkwarin mayar da hannun jari.” Ya bayyana cewa kungiyar ta hada baki ta zuba jarin Naira miliyan 93 tare da kamfanonin. “A yayin gudanar da bincike, an aika da wasikun ayyukan bincike zuwa Hukumar Kula da Canje-canje (SEC), Bankuna, Babban Bankin Nijeriya (CBN), da Hukumar Kula da...
    Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai Tottenham Hotspur da West Ham United na fafatawa wajen ganin sun dauki tauraron dan wasan Nijeriya dake buga kwallo a Club Brugge, Raphael Onyedika, ana alakanta Onyedika da barin kungiyar Club Brugge sakamakon rawar gani da ya taka a bana. Dan wasan na Nijeriya ya samu dimbin masu sha’awar raba shi da Brugge saboda bajintar da ya nuna a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta bara, a cewar Transferfeed, kungiyoyin biyu na son siyan dan wasan tsakiyar a wannan bazarar, West Ham na son ya maye gurbin Tomas Soucek dan kasar Czech, wanda ke kan hanyarsa ta barin kungiyar. Nico Williams Ya Amince Da Komawa Barcelona Akan Kwantiragin Shekaru 6 Diaz Ba Na...
    Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD ya yi kiran hada karfi da karfe a bangaren kasa da kasa don karfafa tattaunawa domin ganin an yayyafa ruwa ga rikicin Isra’ila da Iran. Wakilin, Fu Cong ya ce, yayin da rikicin yake-yaken sojoji na Isra’ila da Iran ya shiga kwana na takwas, abin bakin ciki ne ganin yadda lamarin yake janyo asarar rayukan fararen hula da dama tare da lalata kayayyakin aiki a dukkan bangarorin biyu. Ya kara da cewa, idan har wutar rikicin ta ci gaba da ruruwa, ba kawai bangarorin biyu ne za su tafka babbar asara ba, hatta sauran kasashen yankin lamarin zai yi musu mummunar illa. Fu Cong, ya fada wa wani taron gaggawa na kwamitin sulhun...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wakilin ƙasar Iran ya isa birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya domin halartar taron Ƙungiyar Haɗin kan Kasashen Musulmi (OIC) a ranar Asabar. Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa, a yayin taron Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, zai gana da jami’an diflomasiyya na ƙasashen Larabawa don tattauna batun rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin ƙasarsa da Isra’ila. Kimanin jami’an diflomasiyya 40 ne ake sa ran za su halarci taron a daidai lokacin da Isra’ila da Iran ke ci gaba da musayar hare-haren makamai masu linzami. “Ministan harkokin wajen ya isa Istanbul a safiyar yau domin halartar taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan Musulunci,” in ji Tasnim. Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila Najeriya...
    Idris, wanda shi ne ya jagoranci zaman, ya bayyana irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro da sauran Hafsoshin Sojin a matsayin mai tabbataccen tasiri da gamsasshen sakamako.   Ya ce: “Abin da muka gani ba wai kawai daƙile waɗannan barazanar ba ne, sai dai ma sake karɓe sararin ƙasar mu, da tunanin jama’a, da kuma a matakin aiki. Yanzu ‘yan Nijeriya za su iya tabbatar da cewa manyan hanyoyin mu sun fi samun tsaro ƙwarai idan aka kwatanta da ‘yan shekarun baya.”   Ya lissafa nasarorin da rundunonin sojin Nijeriya suka samu a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da yankin Arewa-maso-gabas da gaɓar teku. “Daga nasarar ragargaza sansanonin Boko Haram da ISWAP...
    Aminu Boyi ya kara da cewa ido ba mudu ya san kima, idan dai batun nagarta da kwarewa da jajircewa, lallai Shettima ya yi zarra, wannan tasa ba za su laminci wani ya sauya sunansa ba a takatar 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙasar Iran ta bayyana shirinta na shiga tattaunawar sasantawa “idan aka tsagaita hare-hare”, kamar yadda ministan harkokin wajen ƙasar ya bayyana bayan ganawa da takwarorinsa daga Faransa, Burtaniya da Jamus.   Yayin da ministocin Turai suka nuna sha’awar ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna shakku kan yiwuwar nasara, yana mai cewa Iran tana son magana kai tsaye da Amurka. Hakan ya faru ne a lokacin da rikici tsakanin Iran da Isra’ila ke ci gaba, inda Isra’ila ta kai hari kan wasu wurare a Tehran, kuma Iran ta mayar da martani da harin makamai. Fadar White House ta bayyana cewa Trump zai yanke shawara cikin makonni biyu kan ko Amurka za ta ɗauki mataki...
    A yau Juma’a, mai magana da yawun rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta kasar Sin reshen gabashi Liu Runke, ya soki lamirin kasar Birtaniya, bisa yadda ta zuzuta abun da ya wakana yayin wucewar jirgin ruwan sintirinta ta zirin Taiwan a ranar Laraba. Liu Runke, ya ce rundunar ta PLA reshen gabashi ta girke dakaru domin sanya ido ga yadda daukacin lamarin ya faru, tare da tabbatar da kasancewa cikin matakin koli na ko-ta-kwana, tare da aiwatar da matakai yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    A cikin takardar, ƙungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar kafa sabuwar jam’iyya maimakon haɗaka da wasu. Sun bayyana cewa sun zaɓi suna All Democratic Alliance (ADA) kuma taken jam’iyyar shi ne “Justice for All” wato “Adalci ga Kowa.” Sun kuma haɗa da adireshin babban ofishin jam’iyyar a cikin takardar. Sun gabatar da wasu muhimman takardu da suka haɗa da tambarin jam’iyya, tsarin kundin mulki, tutar jam’iyyar, da manufofinta. Tambarin jam’iyyar ya ƙunshi kayan hatsi irin su masara da launuka masu ma’ana. Kundin tsarin mulki kuma ya ƙunshi manufofi, tsari da dokokin jam’iyyar, bisa ga tsarin dokokin Najeriya da ƙa’idar dimokuraɗiyya ta duniya. Takardar ta ƙare da girmamawa, inda ta ke roƙon INEC da ta ɗauki mataki na gaba wajen...
    Kazalika, a cewar jami’in, Sin na kara bude kofarta ga ketare bisa matsayin koli, da shigo da jari cikin kasar a bangaren sana’o’in samar da kayayyaki, kana da yafe dukkannin harajin kwastam ga kasashen Afirka mafiya fama da karancin ci gaba da suka kulla dangantakar diplomasiyya da ita. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta kama wani mutum mai suna Alexander Peter bisa zarginsa da kashe mahaifiyarsa mai suna Madam Atiny Peter mai shekara 71 da adda. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ikot Inyang da ke ƙaramar hukumar Oruk Anam a Jihar Akwa Ibom. Yin sulhu da ’yan bindiga dabara ce ba gazawa ba — Gwamnatin Sakkwato Katolika ta horar da shugabannin al’umma da na addini kan zaman lafiya Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Baba Mohammed Azare ne ya tabbatar da kamen a yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, a hedikwatar ’yan sanda da ke Ikot Akpan Abia, a Uyo. Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin Alexander ne a ranar...
    A yau Jumma’a, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2025, an kafa sabbin kamfanoni na kasashen waje guda 24,018 a babban yankin kasar Sin, wanda ya nuna an samu karuwarsu da kashi 10.4 bisa dari a mizanin shekara-shekara. Daga watan Janairu zuwa Mayu, ainihin jimillar jarin waje na kai-tsaye, watau FDI da aka yi amfani da shi a masana’antun fasahohin kasar Sin ta kai yuan biliyan 109.04, inda jarin na FDI ya karu da kashi 146 cikin 100 a fannin hada-hadar kasuwanci ta shafin intanet, da kashi 74.9 cikin 100 a fannin kera kayayayakin jiragen sama, da kashi 59.2 bisa 100 a fannin samar da sinadaran harhada magunguna, da kuma karin...
    Alhaji Hassan ya ce duk da matsalolin tsaro da aka samu a kananan hukumomin, Jihar Kaduna ce kan gaba a noman shinkafa a daukacin jihohin da suke Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar tantance fina-finai ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta ce za ta ci gaba da sa ido tare da ɗaukar matakin shari’a kan duk wani da ya yi amfani da sunan barkwanci don yada abin da ya kira da “nishadi mai tada zaune tsaye.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dangane da sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar na cewa za ta maido da yin tambayoyi ga dalibai kafin a ba su biza kuwa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin ta lura da batun, kuma tana fatan Amurka za ta aiwatar da kalaman shugaba Trump na maraba da daliban kasar Sin da su zo Amurka don yin karatu. Dangane da wani rahoto da wata cibiyar bincike ta kasar Switzerland ta fitar, inda ta bayyana cewa, matsayin karfin yin takara na yankin Hong Kong na Sin ya karu zuwa matsayi na uku a duk fadin duniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan na nuni da matsayin Hong Kong na musamman da kuma alfanun da ake da shi, da kuma...
    Kafin wannan, yana riƙe da sarautar Walin Gaya, wanda aka ba shi lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiri sabbin masarautu. Masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da ƙimar sarautun gargajiya bisa tsarin da aka gada. Sai dai matakin ya zo ne mako guda bayan Alhaji Usman ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kan zarginta da karɓar bashi na dala miliyan 6.6. Gwamnatin Kano ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa ba gaskiya ba ne face tsantsar siyasa. Ko da yake masarautar ba ta danganta ƙwace sarautar da wannan suka da Alhaji Usman ya yi ba, lokacin da aka ɗauki matakin ya haifar da zargi da cece-kuce a tsakanin jama’a. Daga kanmu, magana...
    Da take aiwatar da rahotannin sirri cikin gaggawa, rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an ‘yansandan Nijeriya, Sojoji, jami’an kula da jama’a na jihar, da ’yan banga na yankin sun bi sawun barayin da suka tsere zuwa Dutsen Falale da ke yankin Kurfi-Safana inda aka yi musayar wuta mai tsanani, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindigar 12.   Sai dai kuma, yayin da yake yabawa wannan bajinta da jajircewa da jami’an tsaron suka yi, Dakta Mua’zu ya bayyana matukar alhininsa game da rasuwar wani dan banga mai suna Alhaji Danmalam wanda ya rasa ransa a fafatawar.   Bugu da kari, soja guda ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana samun kulawa a Asibiti.   Alhaji Danmalam ya rasu...
    Idan dai za a iya tunawa, a baya an kai hari gidan dangin Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 15 ga Afrilu, 2025, ba tare da an kama ko daya daga cikin maharan ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Murdyk ya halarci wasan karshe na gasar cin kofin Uefa Conference League da Chelsea ta doke Real Betis a watan da ya gabata, amma kuma ba a cikin tawagar Chelsea ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, FA ta ce “Za mu iya tabbatar da cewa an tuhumi Mykhailo Mudryk da laifin keta dokar hana kara kuzari, ta hanyar amfani da wani abu da aka haramta, wanda kuma ya sabawa doka ta 3 da 4 a kundin dokokin FA na hana kara kuzari.   Zuwa yanzu Chelsea ba ta ce komai ba dangane da tuhumar da akeyiwa Murdyk amma a watan Disamba ta ce, ta na fatan dan wasan nata yayi nasara duba da cewa “Mykhailo ya...
    Aiki ceton, ya samu hadin gwiwar kungiyoyin ceto da suka hada da Red Cross da Hukumar Kula da Ruwan Kogin (NIWA) da jama’ar garin Yauri.   A ranar Laraba, an yi jana’izar Mutane uku, a garin Hikiya da ke karamar hukumar Rohiya a jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An cimma jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a taron koli na biyu na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar 17 ga watan nan agogon kasar. Shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya sun yaba wa kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa kuma kawa ta gaskiya da kasashen yankin tsakiyar Asiya za su iya amincewa da ita har abada. Ana iya sa ran cewa, hadin gwiwar da Sin za ta yi da tsakiyar Asiya ba wai kawai za ta inganta manyan ayyukan hadin gwiwa ba ne, har ma za ta kara karfafa kokarin “neman sabbin abubuwa masu dadi” da “sabbin kirkire-kirkire”, da sa kaimi ga kasashen shida wajen cimma zamanantarwa tare...
    Sauran sun hada da: Danjuma Azi, Fwangje Bala Ndat, Salome Tanimu Wanglet, Namba Rimuyat, Nimchak Rims, Ishaku Maren da Paul Datugun.   Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce bincike ya nuna cewa tsaffin ‘yan majalisar sun shafe watanni shida ne kawai a kan karagar mulki, sannan gwamnatin jihar ta siya musu motocin alfarma.     Bincike ya kuma nuna cewa, motocin da aka ce kudinsu ya kai Naira biliyan 2.5. Bayan sun sauka akan mukaminsu, sun tafi da motocin kuma duk kokarin da aka yi na su dawo da su, lamarin ya ci tura.   Sai da gwamnatin jihar ta sake sayo wa ‘yan majalisar na yanzu motocin da kudinsu ya kai kimanin...
    An gayyaci shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa kasar Kazakhstan, daga ranar 16 zuwa 18 ga watan Yunin shekarar 2025, don halartar taron koli karo na biyu na Sin da tsakiyar Asiya. A karshen ziyarar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi wa manema labarai karin haske game da lamarin. Wang Yi ya ce, babban abin da ya fi daukar hankali a wannan taro shi ne sanarwar da shugaba Xi Jinping ya yi ta “Ruhin Sin da Tsakiyar Asiya”. Inda shugabannin kasashen yankin tsakiyar Asiya suka amince baki daya kan kiyaye wannan ruhi, da inganta tsarin kasar Sin da tsakiyar Asiya don samun sabon babban ci gaba. Bugu da kari, dangane da halin da ake ciki a yankin...
    Don girmama ziyarar shugaban ƙasa, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu domin bai wa mazauna yankunan damar halarta taron da kuma bin diddigin abubuwan da suka shafi ziyarar. Wannan ita ce ziyarar farko da Tinubu ya kai Jihar Benuwe tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta. Jama’a da dama na kallon wannan ziyara a matsayin gwada gwamnati kan yadda za ta shawo kan matsalolin tsaro, musamman a jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, rikicin makiyaya da na ƙabilanci. Kisan da aka yi a Yelwata, wanda shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren, ya janyo suka damuwa a faɗin ƙasar tare da ƙara matsin lamba ga shugaban ƙasa da ya ɗauki matakin gaggawa don tabbatar...
    A yayin shari’ar, jami’in ‘yansanda ASP Luka Sadau, ya bayyana cewa wasu daga cikin kwamitin Masallacin ne suka kama Usman a ranar 13 ga watan Yuni, sannan suka kai shi ofishin ‘yansanda. Ya ce bayan sallar Juma’a, Usman ya sace takalma da kuɗinsu ya kai Naira 100,000. Usman ya kuma amsa cewa yana yawan zuwa Masallaci a ranakun Juma’a domin satar takalma, sannan ya sayar da su a kasuwannin Monday Market da Maraban Rido. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Da farko mun ɗauka yana wasa ne, amma kafin wani ya kai ɗauki, ya riga ya kunna wa kansa wuta.” Wata mazauniyar yankin, Aisha Salisu, ta ce yana matashin yana shaye-shaye. “Ba ya cikin hayyacinsa. Ana jin warin wani abu mai ƙarfi a jikinsa, kuma yana karkarwa da ihu,” in ji ta. Mutane sun yi ƙoƙarin taimaka masa. Wasu sun ja shi zuwa cikin ruwan da ke wata magudanar ruwa a gefen hanya, amma wutar ta riga ta yi masa ƙone sa. “Abun ya zama kamar fim kuma mai ban tsoro,” in ji wani direban adaidaita sahu mai suna Ibrahim Jafar. “Ko bayan da suka jefa shi cikin ruwan, wutar ba ta daina ci nan take ba. Fatar jikinsa duk...
    Kasar Sin ta cimma nasarar aikin gwajin tserewa lokacin da ake gamu da matsala a matakin farko na harbar kumbo mai dauke da mutane na “Mengzhou” a yau Talata, a cibiyar harbar taurori dan Adam dake birnin Jiuqiu, abin da ya alamanta cewa, Sin ta cimma sabuwar nasara a aikin binciken duniyar wata tare da kumbo mai daukar mutane. Wannan ita ce nasara irinta ta biyu da Sin ta samu a wannan bangare, bayan shekaru 27 da suka gabata, da samun nasara ta farko a aikin gwajin da ta gudanar a shekarar 1998. Aikin gwajin tserewar da aka gudanar ya kasance muhimmin mataki na ba da tabbaci ga rayukan ’yan saman jannati, wato idan an gamu da hadari ko matsala...
    Kwamitin Majalisar wakilai mai kula da samar da abinci mai gina jiki da tattalinsa ya fara bincike kan yadda aka kashe Naira Tiriliyan 1.12 na shirin Ba da Lamuni na Anchors. Har ila yau, binciken ya shafi yadda cibiyar NIRSAL’s ta raba Naira biliyan 215 na ayyukan noma da kuma yadda Bankin Masana’antu (BOI) shi ma ya raba Naira biliyan 3 ga kananan manoma 22, 120 ta shirin AVCF. An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana Sin Ta Fara Aiwatar Da Matakin Soke Haraji Kan Kayayyakin Kasashen Afirka 53 Da yake jawabi a zaman binciken, shugaban kwamitin Hon. Chike Okafor, ya bayyana damuwarsa cewa, a cikin cibiyoyin hada-hadar kudi 24 da...
    “Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma gode wa Tinubu bisa yadda ya bai wa ‘yan Arewa maso Gabas muƙamai masu gwaɓi kafin na nemi a mara masa baya,” in ji Salihu. A lokacin taron, wasu matasa sun kusan kai masa hari, amma ya ce hakan ya faru ne saboda wasu ba su fahimci abin da ya yi ba. Ya kuma jaddada cewa a tsarin jam’iyya, mutum ɗaya ne kawai ake zaɓa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a lokacin zaɓen fidda gwani, kuma shi ne ke da ‘yancin zaɓar mataimakinsa. “Ba a daidaita tikitin shugaba da mataimaki a zaɓen fidda gwani. Ɗan takara kawai ake zaɓa, kuma yana da ‘yancin zaɓar wanda zai mara...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karancin kayan ganyayyaki na cigaba da barazana ga lafiyar ‘yan Najeriya.   Masana sun bayyana cewa akwai gibi mai girma na rashin kayan ganyayyaki da ya kamata cike. Sai dai hakan na fuskantar tasgaro sakamakon wasu dalilai. NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan matsala da zummar nemo hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa, kwakkwaran zumunci da ake sadawa a aikace a tsakanin Rwanda da kasar Sin na yin tasiri mai kyau ga al’ummar Rwanda. A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu (CAETE) da aka gudanar daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, Nduhungirehe ya kara da cewa, “Muna da kyakkyawar alaka da kasar Sin.” Ya yi karin haske game da hadin gwiwa mai fadin gaske a tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, fasaha da makamashi. Yana mai cewar, “Muna...
    Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin. Ya kuma ce Kwamishinan ‘yansandan jihar ya tura rundunar ta musamman don taimakawa wajen gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka sace. Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Kwara, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ƙona Gidaje Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Ponyan, Hon. Banjo Fabola, ya tabbatar da cewa an...
    Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....
    Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan ya nuna ragin hauhawar farashi a faɗin ƙasar nan. Masana na ganin wannan ragi a matsayin alamar ci gaba ga tattalin arziƙi, sai dai har yanzu ‘yan Nijeriya da dama na fama da tsadar rayuwa, musamman wajen samun kayan abinci da wasu muhimman abubuwan buƙara na yau da kullum. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi  Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin wani sako da Ismail Baqa’i ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe adadi mai yawa na yara Iraniyawa tare da kai hari kan asibitin yara a tsawon kwanaki uku na hare-haren soji kan Iran. Kamar yadda Ya’ir Golan, tsohon mataimakin hafsan hafsoshin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da cewa: Kashe...
    A cikin wata wasika mai kwanan wata 23 ga Mayu, 2025, mai lamba CR/3000/IGP-SEC/MU/ADM/14/ABJ/VOL 118/57, wacce aka aike wa sakataren gwamnatin jihar Kano, na cewa, IGP ya bukaci a mika Bature zuwa gaban wani jami’i, SP Mojirode B. Obisiji a ranar Alhamis 29 ga Mayu, 2025, domin amsa tambayoyi.   In ba a manta ba, IGP a watan Disamba, 2024 ya ba da irin wannan umarni tare da tura jami’an sa ido na IGP domin su kamo mai magana da yawun Gwamnan Kano tare da kai shi hedikwatar rundunar da ke Abuja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Garkuwan sararin samnaiyar kasar Iran a lardin Zanjan ya bada labarin kakkabo jiragen yakin na HKI guda biyi wadanda ake sarrafasu daga nesa a sararin samaniyar. Kamfanin dillancin lbaran Tasnim na sojojin kasar Iran ya nakalto majiyar dakarunn juyin juya halin musulunci na kasar Iran tana fadar haka. Labarin ya kara da cewa rubuce rubucen da aka rubuta a jikin jiragen da aka tarwatsa sun bayyan cewa kirar kasar Amurka ce. Wannan yake tabbatar da irin hannun da Amurka take da shi a cikin yakin da Iran take fafatawa da HKI. A wani labarin kuma yansandar yanar gizo sun kama mutane biyu wadanda suke yada labaran karya dangane da yaki da kuma shuwagabannin kasar. Har’ila yau an kama wasu wadanda...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyaana cewa kasarsa bata rufe kofar diblomasiyya dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, matukar HKI zata dakatar da hare-haren da take kaiwa kasar. Kamfanin dillancin  labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Lahadi a taron yan jaridun da ya kira a birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa Iran tana son ta ci gaba da shirinta na makamashin Nukliya ta zaman lafiya ta hanyar diblomasiyya idan an bata damar yin haka. Ministan ya ce ikidar JMI ne warware dukkan matsaloli da farko ta hanyar Diblomasiyya, da kuma tattaunawa amma ba zamu taba amincewa  wani ya hanamu hakkimu na mallakar makamashi nukliya ta zaman lafiya ba....
    Bisa la’akari da haka, a fili kasar Sin tana adawa da matakin da Isra’ila ta dauka na keta dokokin kasa da kasa, inda ta kai wa kasar Iran hari, lamarin da ba za a amince da shi ba, musamman ma ta la’akari da yadda kasashe daban daban ke ci gaba da neman hanyar daidaita batun nukiliyar kasar ta Iran ta hanyar siyasa. Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci Isra’ila da Iran da su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, da lalubo bakin zaren kasancewa tare cikin kwanciyar hankali da lumana. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Jam’iyyar APC a Yankin Sanatan Kaduna ta Arewa (Zone 1) ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, don sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu. An yanke wannan shawara ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jami’ar Tarayya ta Ilimi da ke Zaria, inda tsoffin gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa, da kwamishinoni da shugabannin hukumomi na tarayya da jiha suka halarta. EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna An Karrama Dalibar Kaduna Da Ta Zo Ta Biyu A Gasar Karatun Alkur’ani Ta Duniya Masu ruwa da tsakin sun jero nasarorin da gwamnati mai ci ƙarƙashin APC...
    Wani jami’in ɗan sanda, SP Mustapha Garba Gumau, ya yi gamo ajalinsa a wani hatsarin mota yayin da ya rage aƙalla sa’a ɗaya a ɗaura masa aure. Aminiya ta ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin jami’in ne a kan hanyar Gumau zuwa Magaman-Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi, inda za a ɗaura masa aure. Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina SP Gumau wanda hatsarin ya rutsa da shi da abokansa ya rasu ne da misalin ƙarfe 9 yayin da ake shirin ɗaura masa aure da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Asabar. Wata sanarwa da mai magana da yawun...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Babu wata tattaunawa da zata yi da Amurka a halin da take ciki na kare kanta A yayin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasar Iran, a hukumance Iran ta bayyana rashin yiwuwar ci gaba da zaman tattaunawa da Amurka kan batun shirinta na makamshin nukuliya, tare da dora wa Amurka alhakin abin da ke faruwa kai tsaye. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Akwai hadin kai tsakanin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka wajen kai hare-hare kan kasar Iran domin rusa zaman tattaunawar nukiliya da haka ke bayyana kawar da duk wata magana ta hakikanin aniyar Amurka na samar da hanyar warware takaddamar Shirin Iran...
    Kungiyar ‘Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya’ ta yi Allah wadai da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan Iran Kasashe mambobin kungiyar aminan yarjejeniyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun fitar da wata sanarwa ta musamman inda suka yi kakkausar suka kan wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Sanarwar ta yi la’akari da harin hadin gwiwa ta sama da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar a ranar 13 ga watan Yuni a kan wasu wurare da dama a Iran, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da jikkata wasu daruruwa da suka hada da mata da kananan yara da masana kimiyya, matakin da ya saba wa Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da muhimman ka’idojin dokokin...
    Sannan shi ne ya fi kowanne danwasa yunkurin cin kwallo a gasar, inda ya kai hari (attempt) sau 64, 23 daga cikinsu akwai munana (on target) 23. Ya yi nasarar yanka abokan hamayyarsa har sau 62, sannan ya yi bugun kwana 45.   Rapinha Zakakurin danwasan gaba na Barcelona da Brazil, Rapinha, na cikin ‘yanwasan da suka fi bai wa mabiya harkokin wasa mamaki a kakar wasa ta bana baki daya – ba a Champions League ba kawai. Tare da dan wasan kungiyar Borussia Dortmund, Serhou Guirassy, su ne kan gaba a cin mafi yawan kwallaye da 13 kowannensu. Sai dai Rapinha ya zarta shi da yawan bayar da kwallo a zira a raga, inda yake da guda 9, Guirassy...
    Wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ko IAEA Li Song, ya ce kasarsa na matukar Allah wadai da harin Isra’ila kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran da ake amfani da su domin ayyukan zaman lafiya. Li Song, ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin taron manyan jami’an majalisar gudanarwar hukumar ta IAEA, game da batun hare-haren da Isra’ila ta kaddamar kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran. Ya ce, har kullum Sin na mayar da hankali ga zakulo matakan wanzar da zaman lafiya, dangane da batun nukiliyar Iran ta hanyoyin siyasa da diflomasiyya, tana kuma adawa da kakaba takunkumai ba bisa ka’ida ba daga bangare guda. Har ila yau, Sin za ta ci gaba da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Semenyo ma ya taka rawar gani saboda kwallo biyun da ya ci a wasan karshe sun sa ya ci wa kungiyarsa Bournemouth kwallo 11 kenan a karonfarko. Danwasan Najeriya Aled Iwobi ya fi abokan wasansa kokari a Fulham da kwallayensa tara da ya ci da kuma taimakawa wajen cin shida, sannan ya dan dara Amad Diallo na Manchester United (wanda ya ci takwas kuma ya bayar aka ci shida). Amma Iwobi ya fi shi buga wasanni saboda Diallo ya yi jinyar wajan watanni uku a kakar da ta gabata. Iwobi ne dai kan gaba wajen kirkirar damarmaki (59) da kuma bayar da cikakken fasin (508) a cikin bangaren abokan hamayya, inda shi kuma. Thomas Partey na Ghana ya fi yawan...
    Kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, ta gudanar da taron shekara-shekara na biyu, na hukumar zartaswar cinikayyar hidimomi a birnin Geneva dake kasar Switzerland a jiya Juma’a, inda bangaren Sin ya yi nuni da cewa, matakin Amurka game da harajin kwastam na tattare da rashin fahimta da rashin gaskiya a wasu fannoni, don haka ya bukaci bangaren Amurka da ta bi ka’idojin kungiyar WTO, da daidaita matsaloli ta hanyar yin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban, da dakatar da daukar matakai daga bangare daya, don tabbatar da tsarin ciniki na duniya tare da bangarori daban daban. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta yi tir da harin na Isra’ila akan Iran tare da bayyana cewa, ya haifar da rikici a tsakanin bangarorin biyu da kuma musayar harba makamai masu linzami. Gwamnatin ta Najeriya ta nuna bakin cikinta akan abinda ya faru, tare da kuma da yin kiran a tsagaita wutar yaki da gaggawa, da kai zuciya nesa. Har ila yau, sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Nigeria wacce kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya rattabawa hannu a yau Asabar,14 ga watan Yuni 2025, ta jaddada cewa; yaki ba zai maye gurbin tattaunawa ba, kuma hanyar diplomasiyya ce za ta kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa, girmama juna da aiki da dokokin kasa...
    Mai magana da yawun hukumar da take kula da filin saukar jiragen sama ta Ben Gorion ta sanar a yau Asabar cewa an rufe filin saukar jiragen saman har zuwa wani lokaci a nan gaba, bayan da aka dauke dukkanin jiragen sama zuwa kasashen Cyprus, Greece da kuma Amurka. Mai Magana da yawun hukumar filin saukar jiragen saman na Ben Gorion  Lisa Daiper ta bayyana ce; Babu wani lokaci takamaimai da aka tsayar domin sake bude filin saukar jiragen saman na Ben Gorion.”  A gefe daya jaridar “Maariv’ ta bayyana cewa; An dauke dukkanin jiragen sama zuwa filayen  jiragen saman a kasashen turai. Haka nan kuma ta kara da cewa; An dauki 14 daga cikin jiragen saman na HKI zuwa...
    Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda ya tattauna ta wayar tarho da jami’ar harkokin waje ta tarayyar turai ya bayyana cewa, ci gaba da tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ba shi da wata ma’ana, kamata ya yi jami’an tarayyar turai din su yi Allawadai da wuce gona da irin HKI akan Iran. Da safiyar yau Asabar ne dai jami’ar diplomasiyyar ta turai Kaja Kallas ta kira yi minsitan harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci inda su ka tattauna halin da ake ciki a yammacin Asiya da ya hada da harin da HKI ta kawo wa Iran. Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana harin na HKI da cewa, wuce gona da iri ne da...
    Na’urorin kakkabo jiragen sama na Iran sun kakkabo jirgin sama na HKI samfurin F-35  a yammacin kasar, wanda shi ne karo na uku a cikin sa’oi 24. Kamfanin dillancin labarun Tasnim ya nakalto majiyar tsaro na cewa; dakarun kare samaniyar jamhuriyar musulunci sun harbo jirgin sama samfurin F-35,kuma matukinsa ya fito ta hanyar amfani da lemar ceto.  Bayan wani lokaci daga faduwar jrigin da kuma fitowar matukinsa daga ciki, sojojin kasa na jamhuriyar musulunci ta Iran sun kama shi. A jiya Juma’a ma dai daakrun kare sararin samaniyar jamhuriyar musulunci ta Iran, sun kakkabo jiragen saman na ‘yan sahayoniya wadanda kirar Amurka ne, kuma daya daga cikin jiragen yakin da take alfahari da su. Shi dai jirgin yakin na Amurka...
    Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta ƙasa ta dakatar da shirinta na gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku, bayan martani mai zafi daga jama’a. Tun da farko, an tsara addu’ar ne domin neman taimakon Ubangiji wajen tabbatar da tsaron (wadataccen) abinci a Nijeriya. Wata takarda da ta bayyana ga jama’a, wadda Daraktar Gudanarwa ta Ma’aikatar, Mrs. Adedayo Modupe O., ta sanya wa hannu, ta gayyaci daraktoci da sauran manyan ma’aikata domin halartar wannan taron addu’a a shalƙwatar ma’aikatar a Abuja, a ranakun 16, 23 da 30 ga Yuni, 2025. Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025...
    Bugu da kari, akwai kuma masu kiwon Tarwada a gonar da sama da su 600, wadanda aka rage yawan adadinsu daga 1,327 zuwa 600, bayan bullar cutar annobar Korona, saboda kalubalen ci gaba da gudanar da sauran ayyukan gonar. A shekarar 2024, masu kiwon Tarwadar a gonar; sun samar da Tarwadar da yawanta ya kai kimanin tan 1,700, wadda kuma aka kiyasata cewa; kudinta ya kai na Naira biliyan 4.5. Wannan ba karamin ci gaba ba ne, musamman duba da cewa; gonar ta kasance abin koyi ga sauran kungiyoyin da ke kiwon Tarwada a daukacin fadin wannan kasa. Bisa wannan nasarori da gonar ta samar, hakan ya nuna yadda take ci gaba da samun yabo daga kasashen duniya, cikin masu...
    Ya yabawa hukumar bisa yadda ta aiwatar da dokar da ta ba da damar, ‘Dokar Ci Gaban Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NOGICD) ta 2010. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamandan  sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Janar Amir Ali Haji Zadeh yana cikin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar harin da sojojin HKI su ka kawo wa  da asubahin yau Juma’a. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto majiyar juyin juya halin musulunci ta Iran tana tabbatar da shahadar Janar  Amir Ali Haji Zadeh.
    Yayin taron shekara-shekara na tattaunawar CBD na shekarar 2025 da aka rufe a yau Juma’a 13 ga wata, mashawarci kana kwararre a hukumar kasuwancin kasar Sin ta kasar Birtaniya, kuma shugaban cibiyar bunkasa kasuwanci tsakanin Birtaniya da Sin mista John Mclean, ya bayyana yayin da yake hira da wakilin CMG cewa, kasuwar kasar Sin tana cike da damammaki, don haka dole ne ya shiga a dama da shi a cikinta. A ganinsa, yayin da ake tinkarar tashe-tashen hankula da rashin tabbaci a duniya, babbar baiwar da Sin take da ita, da muhalli mai aminci da bude kofa ga kowa, sun samarwa kamfanonin Birtaniya da ma duniya baki daya damammaki. Tun bayan kafuwarsa a shekarar 2000 zuwa yanzu, taron ya kasance...
    Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan. Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar da shinkafa zuwa tan 58,000, lamarin da ya bai wa gwamnatin tarayya sanya tallafi a bangaren rabar da shinkafa ga jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa. Ministan ya ce akwai bukatar kare masu amfani da kuma kayan da ake nomawa, “kaso 80 cikin 100 na abincinmu manoman cikin gida ne suka samar da su.” A daidai gabar da ake hasashen adadin ‘yan Nijeriya zai kai...
    Lamarin ya ci gaba da raguwa har zuwa 2024, inda yawan kudaden da ake kashewa a yawon ketare ya fadi da kaso 14 a matakin shekara-shekara zuwa dala biliyan 2.66. Hakan na nuni da cewa ‘yan Nijeriya sun rage kashe kudaden da suke kashewa kan safarar jiragen sama da dala biliyan 1.12 ko kuma kashi 30 cikin dari a cikin shekaru biyun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya umurci jami’an tsaro su gaggauta kai dauki ba tare da bata lokaci ba don tabbatar da an gurfanar da masu laifin a gaban kuliya, yana mai jaddada cewa za a hukunta duk wanda aka samu dauke da muggan makamai ko kuma aka samu yana da hannu wajen aikata laifuka. “Ga iyalai da ‘yan uwa da masoyan marigayi Ahmed, ina mika sakon ta’aziyyata, da na gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, kuma muna jimami tare da ku, ina ba ku tabbacin za a yi adalci. “Ina kuma kira ga jami’an tsaro su kara kaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma sintiri kan tituna, musamman a wuraren da ke fuskantar irin wadannan laifuka. Jama’armu sun cancanci tafiya cikin walwala ba tare da...
    A cewar Bawa, gwamnatocin da a karkashinsu aka wawashe dukiyar kasa, su ne na Mulkin Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2006), sai Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua (daga 2007 zuwa 2009), kazalika a mulkin Shugaba Goodluck Jonathan daga (2010 zuwa 2014), sai kuma mulkin Muhammadu Buhari (daga 2015 zuwa 2023). Wadannan bayanai na kunshe cikin littafin, ‘The Shadow Of Loot and Loss – Uncobering Nigeria’s Petrol Subsidy Fraud,’ wanda tsohon sarkin yaki da cin hanci da rashawa ya rubuta. Alkaluman da Bawa ya bayyana daga cikin gwamnatocin hudu, shugaba Buhari ne ke kan gaba wajen biyan tallafin da ake ta cece-kuce akai na Naira tiriliyan 11, sai kuma na Jonathan wanda ya kashe Naira tiriliyan 3.9. Gwamnatin...
    Da yake nasa jawabin, Sangare ya ce, Nijar na bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma tana ba da fifiko ga hadin gwiwarta da kasar Sin, da mayar da hankali sosai kan harkokin tsaro, kana tana son kara amincewa da juna, da ci gaba da yin shawarwari bisa mutunta juna a tsakaninsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wannan lokaci da wasu sassa ke kafa shingaye, GCI na gina gadoji. Manufar na kuma karfafa gwiwar tattaunawa, da gudanar da shawarwari tsakanin sassan duniya masu bambance-bambance, ta yadda za a kafa managarcin tsarin hadin kan bil’adama mai dorewa. GCI da ranar tattaunawa tsakanin wayewar kan kasa da kasa ta MDD, za su kara zamewa duniya muhimman manufofi na “tafiya tare a tsira tare”!(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Baya ga haka, Sojojin sun kashe ƙarin ‘yan ta’adda goma da suka taru kusa da wani gidan mai a Danjibga, waɗanda ake zargin sun kasance cikin wata tawagar da Dogo Sule ya tara domin kitsa hari. Manjo Janar Kangye ya jaddada cewa rundunar Soji za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana da yaki, sannan ya tabbatar da cewa a shirye suke su fuskanci duk abinda zai faru. Manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi ga taron dakarun sa-kai na “Basiji a nan Tehran ya kuma kara da cewa;  Babu wani wuri komai zurfi da nisansa a HKI da ba mu tsinkayowa, idan kuwa aka ba mu umarni to za su yi nasara, mu Sanya abokin gaba ya yi nadama. A gefe daya ministan tsaron Iran ya bayyana cewa; Duk wani hari da ake tunanin kawo wa Iran, to kuwa zai fuskanci mayar da martani mai...
    Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a yankin Cape ya fada a jiya Laraba  cewa; An sami karuwar wadanda su ka rasa rayukansu ya karu zuwa 49. Shugaban tafiyar da sha’anin Mulki a yankin na garin Cape, Oscar Mobyan  ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru,kamar yadda kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto. Wasu yankuna na kasar ta Afirka Ta Kudu sun fuskanci saukar ruwa kamar da bakin kwarya, haka nan kuma saukar kankara, da hakan ya sa aka shiga cikin yanayin sanyi mai tsanani da kuma yankewar wutar lantarki a wasu yankunan. Ambaliyar ruwan da aka samu a kusa da wata makaranta ya ja motar da take dauke da dalibai 13, da hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsu. Tuni...
    A cewarsa, gobarar na iya kasancewa ta samo asali ne daga wani gini da ke bayan gidan man. Rahotanni sun nuna cewa gobarar na iya tashi ne daga tankunan mai da ke ƙasa, kafin ta bazu zuwa cikin gidan man gaba ɗaya. Hukumar kashe gobara ta jihar ta yi gaggawar killace wajen domin hana cunkoso da tabbatar da tsaron jama’a yayin aikin kashe gobarar. Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar, Shakiru Amodu, ya tabbatar da cewa an samu nasarar kashe gobarar kafin ta bazu zuwa gidajen da ke kusa. Kafin ƙarfe 6 na yamma, jami’an agajin gaggawa sun shawo kan lamarin gaba ɗaya, tare da killace yankin da abin ya shafa domin kaucewa wata barazana. Daga kanmu, magana...