Leadership News Hausa:
2025-09-17@22:36:06 GMT

Fabio Na Brazil Ya Kafa Sabon Tarihi A Kwallon Kafa

Published: 24th, August 2025 GMT

Fabio Na Brazil Ya Kafa Sabon Tarihi A Kwallon Kafa

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Fluminense Fabio a ranar Talata ya zama mutum na farko a tarihin wasan kwallon kafa na maza da ya buga yawan wasanni a tarihi, lokacin da dan Brazil din ya buga wasa karo na 1,391. Dan wasan mai shekaru 44 a ranar Asabar ya yi daidai da tarihin da tsohon dan wasan Ingila Peter Shilton ya rike na wannan adadin ya samu wannan nasarar a wasan da suka doke America de Cali da ci 2-0 a filin Maracana dake Rio de Janeiro.

Kafofin yada labaran Fluminense da na Brazil sun ce a yanzu Fabio ya kasance shi kadai a tarihin kwallon kafa, duk da cewa FIFA ko hukumar CONMEBOL ba ta bayyana hakan a matsayin tarihi ba, Fabio, wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a Brazil, ya ce “Wani lokaci ba ma fahimtar muhimmancin irin wannan gagarumar nasara ta karya tarihi ba,” in ji Fabio, wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a Brazil.

Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah Yadda Ake Alale

Magoya bayan Fluminense sun yi ta rera cewa, “Fabio shine mafi kyawun mai tsaron gida a Brazil,” kuma ya sun daga allunan dake dauke da hotunansa, kocin Fluminense Renato Gaucho ya ce “Babu wanda ke buga wasanni da yawa ba tare da matakin kwarewa kamar nasa ba, kuma babu shakka zai ci gaba da taka leda na dogon lokaci”

“Zai yi wahala wani dan wasa ya wuce tarihinsa,” in ji kocin, Fabio ya lashe kofin Copa Libertadores tare da Fluminense a shekarar 2023 kuma yana cikin tawagar da ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya na kungiyoyi a Amurka a bana, ya buga wa Cruzeiro wasanni 976 tsakanin 2005 zuwa 2022, bayan ya buga wa Uniao Bandeirante wasanni sau 30 da kuma wasu wasanni 150 tare da Basco da Gama, hakan ya sa jimillar wasannin da ya buga suka kai 1,387, amma hukumar kididdiga ta Guinness World Records ta ce adadin ya kai 1,390.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza
  • Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
  • Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
  • Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff