Hisbah ta kama mutane 62 a cibiyar Gwamnatin Tarayya a Kano
Published: 19th, August 2025 GMT
Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata haɗala a Cibiyar Fasahar Sufuri ta Kasa (NITT) da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Kano.
Mataimakin Kwamandan Hukumar, Mujahid Aminudeen, ya ce mutane — maza 27 da mata 35, “A ranar Lahadi, jami’anmu tare da haɗin gwiwar NDLEA suka su su 62 a cibiyar horarwa ta NITT da ke Dawakin Kudu, bayan samun bayanan sirri daga wasu masu kishin ƙasa.
Ya ce mutanen sun yi amfani da saukar ruwan sama da ake samu lokaci-lokaci a yankin don aikata baɗala.
“Muna amfani da wannan dama don gargaɗi ga matasa masu aikata abubuwan batsa da su daina, ko su fuskanci hukuncin doka. Hisbah ba za ta zauna ba tare da daukar mataki kan masu karya dokar Shari’a ba,” in ji Mujahid Aminudeen.
Yadda bom ya kashe yara 2 ya jikkata wasu 6 a Borno NAJERIYA A YAU: Halin Da Muke Ciki Bayan Rasa ‘Yan Uwanmu A Hadarin Kwale-Kwale A SakkwatoYa kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahoto kan duk wani abu da ya saba wa dokar Shari’a a jihar.
Aminudeen ya ƙara da cewa hukumar ta kai wani samame makamancin haka a Gadar Tamburawa, inda aka kama wasu mutane kan laifuka makamanta da haka.
Ya ce duk waɗanda aka kama za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Baɗala Dawakin Kudu Gadar Tamburawa
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA