Iraki Ce Zata Amfana Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka: Inji Sayyed Ammar Hakim
Published: 17th, April 2025 GMT
Sayyid Ammar Hakim shugaban jam’iyyar ‘ تيار الحكمة الوطني’ na kasar Iraki ya bayyana cewa kasar Iraki ce kasa ta farko wacce zata amfani da tattaunawa tsakanin Iran da kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sayyid hakim yana fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa kasashen Iran da Iraki suna da gangantaka da musulunci makobtaka da kuma al-adu masu yawa.
A wani waje a cikin jawabinsa Hakim ya amince da ruwan da gwamnatin kasar Amurka ta taka wajen kauda tsohuwar gwamnatin kama karya na sadam Husaini. Da kuma kawo tsarin democradiyya wanda ya bawa mutanen kasar Iraki sararawa daga musibun sadam Husain a kan mutanen kasar.
Ya kuma kammala da cewa ‘amminsa shahid Bakir Hakim’ ya taba fadar cewa akwai bukatar mutanen kasar Iran su tattaunawa tsakaninsu da kasar Amurka don tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya ta kudu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
Kamfanin dillancin labarun “Reutres” ya bayyana cewa; Cibiyar da take tafiyar da ayyukan agaji a Gaza, wacce Amurka ta kafa ta, ta bayar da wata shawarar da take cewa; a kafa wa mutanen Gaza hemomi na wucin gadi da za su zama masomin yin hijirarsu zuwa wani wuri daban, a cikin yankin ko a wejensa.
Rahoton kamfanin dillancin labarun na Reuters ya ambato wata majiya mai karfi tana cewa; An gabatarwa da shugaban kasar Amurka shawarar tilastawa mutanen Gaza yin hijira, kuma a cikin kwanakin nan an tatauna wannan batu a fadar mulkin Amurka ta “White House.”
Har ila yau rahoton ya kunshi cewa,tun daga watan Febrairu cibiyar ta fara kokarin tara kudaden da za su kai dalar Amurka biliyan 1 domin aiwatar da Shirin hijirar mutanen Gaza a cikin yankin ko kuma zuwa wajensa, da kuma kwace makaman da suke a hannun ‘yan gwagwarmaya.
A karkashin wannan Shirin da akwai matakai guda uku; Na farko shi ne bayar da kayan agaji. Na biyu shi ne gina hemomi na tsugunar da Falasdinawa a cikinsu. Na uku shi ne fitar da mutanen Gaza zuwa hijira ta dole, wacce babu dadowa.
A fili yake cewa a cikin matakin farko da har yanzu ake cikinsa, wurin da aka kira na raba kayan agaji, ba komai ba ne,sai tarko na kashe Faladinawa. Duk wanda ya je domin ya karbi kayan agaji, to ya zama abin farautar ‘yan sahayoniya.
Masu kula da wadannan cibiyoyin na agaji da aka kafa kuwa su ne; HKI da wata rundunar sojojin ‘yan ina da yaki ta Amurka.