Tsohon Minista Ya Zargi Isra’ila Da Kasashen Yammacin Turai Da Kitsa Kashe-kashen Rayuka A Nijeriya
Published: 17th, April 2025 GMT
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP Yan bindiga Fani Kayode
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani gidan yarin da aka kebewa yan Afrika, kuma yawansu ya kai 115, amma har yanzun ba’a san yawan wadanda suka rasa rayukansu a gidan yari.
Labarin ya kara da cewa har yanzun ma’aikatan agaji suna aikin ceto a wurin, sannan hotunan da suka fara bayyana sun nuna gawaki da dama. Amma Al-Masirah ta bayyana cewa akalla mutane 68 sun rasa rayukansu.