Abincin karnuka ya fi namu —Fursunonin Najeriya
Published: 14th, April 2025 GMT
Fursunoni a gidajen yarin daban-daban a sassan Najeriya sun koka game da munin irin abincin da ake ba su, wanda suka ce na karnuka ya fi shi.
Da dama daga cikin fursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa.
Wannan zargi na zuwa ne bayan da Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya tare da wani kwamitin bincike mai zaman kansa sun ƙaryata zarge-zargen fursunonin kan yunwa a gidajen yari.
A watan Satumban 2024 ne Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa a kwamitin domin gudanar da bincike kan zargin jami’an gidajen yari da cin hanci da kuma cin zarafin fursunonin.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar BornoDuk da cewa kwamitin ya tabbatar da zargin yunwa da fursunonin suka yi, Muƙaddashin Shugaban Hukumar Gidajen Yari ta Kasa, ya ce an zuzuta lamarin, saboda a cewarsa, babu alƙaluman da ke tabbatar da hakan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gidajen yari yunwa
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine
Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu.
Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai shekaru 29 a yankin Zaporizhzhia bayan shafe watanni biyar yana yaƙi a cikin mayaƙan Rasha.
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPPOluwagbemileke ya shafe shekaru huɗu yana zaune a ƙasar Rasha kafin a kama shi akan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi.
An ruwaito cewa matashin ya amince ya shiga wannnan yaƙi ne domin a rage masa yawan shekarun da zai shafe a gidan yari sakamakon laifin da aka kama shi da shi.
Gbemileke yana daga cikin dubban sojojin haya daga ƙasashe masu tasowa da ke taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine.