Yadda Bankin Stanbic IBTC Ke Bunkasa Tattalin Arzikin Abokan Huldarsa
Published: 11th, April 2025 GMT
Idan masu ajiya a Bnkin suka ajiye akalla Naira 10,000 a Asusun ajiya na Bankin ko kuma a cikin Lalitar ajiyarsu ta Bankin a kalla a cikin kwanuka 30, hakan ya nuna cewa, sun tsallake zamowa Zakarun samun damar lashe kyaututuka a wata daya, inda kuma za su shiga gasar zagaye ta karashe.
Kazalika, a cikin kowanne wata daya, mai ajiyar zai iya zamaowa a cikin rukunin Zakaru 70, inda kowanne mai ajiya daya a Bankin, zai iya karbar Naira 100,000.
Har ila yau, a cikin watanni uku kuma, kowanne mai ajiya daya a Bankin na Stanbic IBTC, da ya fito daga yanki bakwai da ake yin kasuwanci, zai lashe Naira miliyan daya, inda kuma a zagayen gasar na karashe ta zango, wanda ya samu nasara, zai iya lashe Naira miliyan biyu.
Bugu da kari, a zagayen karshe da za a karkare, wanda suka zamo Zakaru. Kowannen su, zai samu Naira miliyan biyar.
Bankin na Stanbic IBTC, ya shafe sama da shekaru uku, yana yana sakawa masu ajiya da Bankin, inda ya zuwa yanzu, sama da masu ajiya da Bankin miliyan 1,900 suka samu nasaraa karkashin tsarin sa na, Reward4Sabing Promo 4.0.
Kazalika, Bankin ya rabarwa da wadanda suka samu nasara jimlar kyututukan kudade, da suka kai miliyan 318.
A saboda da irin wannan garabasar ta Bankin, yana da kyau daga yau ka fara tunanin fara yin ajiya a Bankin na Stanbic IBTC Bank.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
China Na Neman Ƙasashe Su Haɗe Wa Amurka Kai Sakamakon Ƙarin Haraji
“Amfani da haraji a matsayin makami don matsin lamba da son rai yana nuni da tsarin siyasa na rashin haɗin kai da kare tattalin arziƙi da kuma zambar tattalin arziƙi. Wannan ba abu ne na adalci ba ko mai kyau – yana nufin zaman ‘Amurka da tafi kowa’ da kuma ƙaruwar ƙarfin Amurka,” in ji shi.
Jakadan ya kuma yi gargadi cewa ƙasashe masu tasowa za su fi shan wahala daga wannan tsarin haraji, kuma hakan zai fi cutar da ƙasashen Afrika, ciki har da Nijeriya.
Ya bayyana cewa, “Amurka ta ɗauki mataki mara son Rai, na cewa ‘ samun ribar kasuwanci sai an yi zamba’ wanda ya kai ga kai wa ƙasashen Afrika haraji mai yawa, wanda ya saɓa wa ƙa’idojin WTO na bayar da kulawa ta musamman ga ƙasashen masu tasowa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp