Aminiya:
2025-05-25@15:06:24 GMT

’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato

Published: 9th, April 2025 GMT

Wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne sun kashe masunta uku a wani hari da suka kai ƙauyen Sanyinna da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.

Wata majiyar a ƙauyen ta ce ’yan bindigar sun kashe mutanen ne a lokacin da suka kawo hari da safiyar Talata yayin da mutanen suka fita sana’arsu ta su.

Kazalika, majiyar ta ce ko a ranar Litinin da ta gabata ’yan bindigar sun kai hari garin Sutti da Takkau duk a karamar hukumar inda sun jikkata mutum biyu.

Mataimaki na musamman ga shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza kan tsaro, Alhaji Gazali Raka ya tabbatar da faruwar lamarin.

Alhaji Raka ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace dabbobi da suka haɗa da Shanu da Rakuma da Tumaki da Awaki.

Hadimin shugaban karamar hukumar ya jinjina wa jami’an tsaro kan gaggauta ɗaukar matakin da suka yi na fatattakar ’yan bindigar tare da ƙwato dabbobi da suka yi awon gaba da su.

Aminiya ta ruwaito cewa mutum biyu da suka samu raunin harbin bindiga suna karɓar magani a babban asibitin Tangaza.

Raka ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-haren ’yan bindiga ke ƙaruwa a garuruwansu musamman da tsakar rana.

Ya yi kira ga mahukunta da su ƙara ƙaimi don ganin an dawo da zaman lafiya a yankin don samar da ci gaba mai ɗorewa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Lakurawa Sakkwato yan bindigar yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

SojojinHKI Sun Kashe Akalla Mutane 75 A Gaza A Ranar Jumma’a Kadai

Sojojin HKI sun sabonta hare-hare a ranar Jumma’a kan fararen hula a kan Falasdinawa a Gaza, inda suka kashe akalla mutane 76 ajiya jumma’a kadai sannan wasu dadama suka ji rauni.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa sojojin HKI sun kai hare-hare a kan wani gida a Khan Yunus inda suka kashe akalla mutane. A wani  harin da sojojin yahudawan suka kai khan yunus har’ila yau ya kashe falasdinawa akalla 8.

Alaa Al-Najjar, likita a asbitin Nasir ya bayyana cewa ta rasa yayanta har 9 a cikin asbitin sanadiyyar hare-haren HKI a kan shi.

Harin da yahudawan suka kai kan gidan Annajjar dai ya rusa gidan daga sama har kasa sannan wutan da ya taso daga gidan sai da ya watsu zuwa gidajen da suke makobtaka da gidan nata.

Dr Annajjar ta sami labarin hari a kan gidanta ne a lokacinda take aiki a kan wasu kananan yara. Yayanta sun kama daga shekara 2-16. Sannan mijinta na daga cikin wadanda suka ji rauni.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ya Kubuta A Hannun ‘Yan Bindiga Bayan shafe Kwanaki 8 Yana Gudu A Dajin Sokoto Da Neja
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 5 A Katsina
  • Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 5 a Borno
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Mazauna Kauyuka 4 A Taraba Bayan Taron Zuba Jari
  • SojojinHKI Sun Kashe Akalla Mutane 75 A Gaza A Ranar Jumma’a Kadai
  • Donal Trump Ya Kori Gomomi Daga Cikin Ma’aikata A Majalisar Tsaro Ta Kasar Amurka
  • Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Borno
  • Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Bormo
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram 16 A Borno Bayan Sun Kawo Hari Barikinsu
  • Jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda 13,000 daga 2023 zuwa yanzu —Ribadu