Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Yi Murabus

Daga Bello Wakili

Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take.

Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa.

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon.

Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har sau biyu daga 2015 zuwa 2023. An kuma naɗa shi minista ne a ranar 21 ga watan Agustan 2023.

Murabus ɗinsa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaron  ƙasa, kuma ana sa ran zai fayyace cikakkun matakan da za a ɗauka a nan gaba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Pizishkiyan:  Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufar
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Janar Chiristopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
  • Shugaba Tinubu Ya Nada Janar Christopher Musa Sabon Ministan Tsaro
  • Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya
  • Kungiyar Hamasa Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji  A Yankin Gaza
  • Shugaban Kungiyar ECOWAS  Ya Gana Da Shugaban Mulki Soji Na Kasar Guinea Bissau
  • Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Yi Murabus
  • Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi
  • Shugaban venuzuwela Ya Gargadi Amurka Game Da Kokarin Da Take yi Na Karbe Ikon Kula Da Rijiyoyin Mai Na Kasar
  •  Kasar Ireland Ta Sauya Sunan Shugaban  “Isra’ila” Da Na Shahidiyar Falasdinu