Hakimin Ketare kuma Kanwan Katsina, Alhaji Usman Bello Kankara, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina bisa karɓar jakadun ƙasashe goma daga sassa daban-daban na duniya a lokacin bukukuwan Sallah na bana.

A cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa irin wannan haɗin gwiwar diflomasiyya ba wai kawai zai bai wa duniya damar ganin al’adun gargajiya masu ɗimbin tarihi na jihar ba, har ila yau zai buɗe ƙofofin zuba jari da haɗin gwiwar ƙasashen waje.

Alhaji Usman Bello Kankara ya kuma jinjinawa gwamnati bisa jajircewarta wajen farfado da tsohuwar al’adar Sallah Durbar da ke da tarihin fiye da shekaru ɗari a Jihar Katsina.

“Gwamnatin Jihar Katsina ta cancanci yabo bisa irin ƙoƙarinta na farfado da tsohuwar al’adar Sallah Durbar da ke da dogon tarihi a jihar.” In ji shi.

A cewarsa, gyaran kujerun masu kallo a fadar sarkin Katsina da ta Daura, da kuma tsohon gidan gwamnati, ya taimaka sosai wajen ƙara jin daɗin baƙi da suka halarci jerin gwanon Sallah.

Kanwan Katsina na daga cikin Hakimai da masu rike da sarautun gargajiya da suka raka Mai Martaba Sarkin Katsina, Dr. Abdulmumini Kabir Usman, wajen gudanar da bukukuwan Sallah Durbar na bana a birnin Katsina.

Ranar farko ta jerin gwanon Durbar ta gudana ne a ranar Sallah, inda Musulmi daga sassa daban-daban na jihar suka halarta tare da iyalansu da dangi.

Ranar ta biyu ta kasance ranar kai gaisuwar Sallah zuwa gidan gwamnati, wanda Sarkin Katsina ya jagoranta tare da rakiyar hakimai da masu sarauta, inda suka kai gaisuwa ga Gwamna Malam Dikko Umar Radda a tsohon gidan gwamnati na Katsina.

An gudanar da jerin gwanon Durbar cikin kyan gani, inda aka ga sarakuna da fadawansu cikin kayan gargajiya, da dawakan da aka kawata cikin kyau, tare da dimbin jama’a da suka shaida bukukuwan.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarta har da Jakadan ƙasar Bulgaria a Najeriya, Yanko Yordanov, da wasu jakadu tara daga ƙasashe daban-daban tare da iyalansu, waɗanda Gwamnatin Jihar Katsina ta karɓa domin halartar wannan biki mai tarihi.

Wakilan Kanwan Katsina a wannan jerin gwanon sun haɗa da dukkanin dagatai a gundumar Ketare, mambobin majalisar gundumar Ketare da kuma dangin Kanwan Katsina.

Shekarar bana ta nuna zagayowar karo na 25 da Kanwan Katsina ke halartar bukukuwan Sallah Durbar tun bayan naɗinsa da aka yi a shekarar 2000 daga marigayi Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Muhammadu Kabir Usman.

Release/Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Al adar Durbar Farfado Gwamnatin Hawan Kanwan Yabi

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina

Wasu mazauna Jihar Katsina sun yi zaman sulhu da wasu shugabannin ’yan daban daji da suka addabe su.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an yi taron sasanci da ’yan bindigar daji ne a Ƙaramar Hukumar Danmusa, wanda rundunar sojoji ke shiryawa, inda Adamu Aliero ya jagoranci sashen ’yan bindigar.

BBC ya ruwaito Kwamishinan Tsaro da Harkokin Ciki Gida na Katsina na cewa al’ummar garin Bicci da ke yankin Ƙaramar Hukumar Danmusa sun zauna tare da Ado Aliero da sauran wasu shugabannin ’yan bindigar aƙalla goma.

“An zauna da Ado Aliero da Kamilu Buzaru da Dogo Nahali da Wada Jargaba da Dahiru Buzu haka ma da Nagoggo,” in ji shi.

Hotuna daga Ahmed Kabiru S/Kuka

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina
  • Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai
  • Dimokuradiyya A Shekara 26: Ba Yabo Ba Fallasa
  • Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA
  • Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi
  • Gwamnatin Tarayya Ta Dukufa Wajen Karya Farashin Kayan Abinci – Minista
  • Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da Sarakuna Da Gundumomi
  • Ƴansanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 2, Sun Ceto Mutane 11 A Delta Da Katsina
  • Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6
  • Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna