DRC : Kinshasa Ta Rufe Sararin Samaniyarta Ga Jiragen Rwanda
Published: 13th, February 2025 GMT
Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango ta yanke shawarar rufe sararin samaniyarta ga “dukkan jiragen sama na farar hula ko na gwamnati masu rijista dake zaune a Rwanda”.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Kwango, matakin ya “hana shawagi da sauka a cikin kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, saboda dalilai na rashin tsaro da ke da nasaba da rikicin masu dauke da makamai.
A taswirorin zirga-zirgar jiragen sama na duniya, jiragen sama daga Kigali na kasar Rwanda, yanzu haka na kaucewa shiga sararin samaniyar Kongo.
Bayanai sun ce wani jirgin da ya tashi daga babban birnin kasar Rwanda zuwa birnin Landan na kasar Birtaniyaa ranar Talata, an tilas ya sauya hanyarsa don yin aiki da dokar, wanda a yanzu ya shafi “dukkan jiragen da suka yi rajista ko kuma suna zaune a Rwanda.”
A ranar Laraba, ma wasu jiragen Rwandair daga Kigali zuwa Libreville, Gabon, ko Lagos, Nigeria, suma sun yi zagaye don gujewa sararin samaniyar Kongo, lamarin daya shafi matafiya zuwa Libreville, da Najeriya wadanda suka samu karin sa’o’i uku na tafiya.
Ga kamfanonin da abin ya shafa, kuwa dokar zata tilasta musu karin kudin man fetur.
DR Kwango da Rwanda dai na takun tsaka game da rikin ‘yan tawayen M23 da Kinshassa ke zargin Kigali da goyan baya a rikicin gabashin kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Bukaci A Kara Inganta Aikin Titin Gabasawa
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar a soke ko kara inganta aikin titin gina hanya mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Gabasawa.
Wannan mataki ya biyo bayan karɓar rahoton da Kwamitin Majalisar kan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci ya gabatar dangane da ambaliyar da ta afku a Zakirai, cikin karamar hukumar ta Gabasawa.
Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin, Alhaji Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana wasu muhimman shawarwari da suka hada da: Umurtar kamfanin da ke aikin gina hanyar da ya faɗaɗa magudanar ruwa a yankin da abin ya shafa da kuma gaggauta kai agajin gaggawa ga waɗanda ambaliyar ta shafa.
Sauran shawarwarin sun haɗa da tura tawagar ƙwararru daga ma’aikatun ayyuka da muhalli na jihar don gudanar da bincike da bayar da shawarwarin fasaha.
Bayan nazari da tattaunawa mai zurfi, majalisar ta amince da rahoton baki ɗaya tare da kiran gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar mataki domin rage tasirin ambaliya a Zakirai.
A wani sabon lamari kuma, majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta sake gina hanyar da ke haɗa Kwanar ‘Yan Mota zuwa Kwanar Bakin Zuwo zuwa Jakara, zuwa Kwanar Gabari a cikin karamar hukumar birnin Kano.
Wanda ya gabatar da kudirin, Honarabul Aliyu Yusuf Daneji, mai wakiltar mazabar Kano Municipal, ya jaddada cewa hanyar, musamman a kusa da kasuwar Kurmi, tana cikin matsanancin hali wanda ke kawo cikas ga zirga-zirga da kuma lalata harkokin kasuwanci.
Haka kuma, Alhaji Abdullahi Yahaya, mai wakiltar mazabar Gezawa, ya gabatar da kudiri na buƙatar gina titin kwalta daga Jogana zuwa Matallawa, Yamadi Charo da Daraudau.
Ya ce hanyar ba ta dadin bi a lokacin damina, inda al’ummar yankin ke ɗaukar matakin kansu ta hanyar cike ramuka da yashi da itace.
Kudirin ya samu goyon bayan Jagoran Masu Rinji a Majalisar, Alhaji Zakariyya Abdullahi Nuhu, tare da cikakken goyon bayan ‘yan majalisar baki ɗaya.
Sauran kudirori da aka amince da su a zaman sun haɗa da: Gina titi daga Dalawada zuwa Gazobi a karamar hukumar Tudun Wada da kuma sake gina hanyar Fanisau a Ungogo.
Daga Khadijah Aliyu