Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi
Published: 12th, February 2025 GMT
Tsohon Hadimin Shugaban Ƙasa a fannin Ƙimar Ƙasa da Zamantakewa, Fela Durotoye, ya bayyana yadda ya ƙi karɓar tayin cin hancin Naira biliyan biyar yayin da yake aiki a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Yayin da yake jawabi a wani taro a Abuja, Durotoye ya ce wani jami’i da ya ce shi limamin coci ne, ya matsa masa lamba domin ya ƙara farashin wani shirin horo da gwamnati ta shirya.
Ya bayyana cewa tawagarsa ta ƙiyasta kuɗin aikin zuwa Naira biliyan 1.3, amma bayan kwana uku, aka ce masa ya gabatar da takardar lissafi zuwa Naira biliyan biyar.
“Sun ce kuɗin da na nema ya yi kaɗan, sun ce za su ƙara shi zuwa Naira biliyan biyu.
“Daga nan ne suka buƙaci na ƙara lissafin zuwa Naira biliyan biyar,” in ji shi.
Lokacin da ya tambayi dalilin ƙarin kuɗin, sai jami’in ya ce masa kada ya damu.
“Ya ce min, ‘Ba wani laifi a ciki. Ka yi wa Najeriya hidima sosai, yanzu lokaci ya yi da Najeriya za ta saka maka da alheri,’” in ji Durotoye.
Ya ce ya ƙi yarda da tayin, kuma don guje wa damunsa, sai ya kashe wayarsa.
Watanni kaɗan bayan haka, ya samu labarin cewa an kama wasu jami’an gwamnati da suka wawure Naira miliyan 426 daga kuɗin wani shirin horo da aka shirya.
Durotoye, ya jaddada cewa gaskiya da ɗa’a ne kaɗai za su taimaka wa mutum gujewa cin hanci a Najeriya.
“Idan muna da kyawawan halaye, ba za a samu cin hanci da rashawa a ƙasarmu ba,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnatin zuwa Naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara
Ɗan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, a wani zagayen ganawa da manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027.
Obi, wanda ke ƙoƙarin ƙara yauƙaƙa zumunci da manyan shugabanni a fadin ƙasar, ya bayyana cewa ziyarar na da alaƙa da burinsa na ganin an samu shugabanci na gaskiya da riƙon amana a Najeriya.
An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wutaA wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana cewa ziyararsa ta musamman zuwa Ibadan na da nufin girmama Rashidi Ladoja, wanda aka naɗa a matsayin Olubadan, da kuma jaddada muhimmancin Ibadan a siyasa, zamantakewa, da tattalin arzikin ƙasar.
“Na kai ziyara don girmama sabon Olubadan, Rashidi Ladoja, wanda ƙwarewarsa a matsayin tsohon sanata, gwamna, kuma attajiri za ta taimaka wajen ɗaga martabar Ibadan,” in ji Obi.
Ya ƙara da cewa tattaunawarsa da Obasanjo da Ladoja na da nasaba da ci gaban Najeriya da kuma shugabanci da ke da burin sauya al’umma ta fuskar gaskiya da adalci.
Ziyarar Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda ake hasashen zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.