Hukumar Kula Da Taswira Ta Jihar Kebbi Tasha Wani Alwashi A Shekarar 2025
Published: 26th, January 2025 GMT
Hukumar Kula Da Taswira Ta Jihar Kebbi (KEBGIS), ta tsara wani gagarumin shiri na samar da kudaden shiga na sama da Naira biliyan daya a shekarar 2025.
Babban Manajan Hukumar, Bashiru Saidu Bakuwai, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan tabbatar da nadinsa a matsayin babban Manaja, ya ce hakan ya nuna kwazon hukumar a karkashin ma’aikatar filaye da gidaje na tallafa wa tattalin arzikin jihar.
Malam Saidu Bakuwai, ya ba da karin haske kan ayyukan hukumar da suka hada da alhakin duk wasu takardu da suka shafi filaye, tsarawa da bayar da takaddun kowane gida, sake tantancewa, daidaitawa, da kuma tsarin rajistar kadarorin.
Sauran su ne Gudanarwa da Rajista na ma’amalar filaye, gami da Ayyuka, jinginar gida, Canjin manufa (amfani da ƙasa), haɗaka da rabe-rabe tare da tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da filaye daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya.
Da yake mika godiyarsa ga Kwamared Nasir Idris da ya jagoranci gwamnatin bisa yadda take tantance daidaikun mutane bisa cancanta da kwazo, don basu mukamai, Saidu Bakuwai, ya ba da tabbacin hukumarsa za ta himmatu wajen rubanya kokari wajen bayar da gudunmawar ci gaban manufofin gwamnatin na inganta shugabanci nagari, da inganta ayyuka. da haɓaka kudaden shiga na cikin gida a jihar.
Sai dai ya yi kira ga takwarorinsa da aka tabbatar da su a sassa daban-daban da su ba da goyon bayansu ga gwamnatin Kwamared Nasir Idris domin su hada kai wajen ba da damar gudanar da ayyukansu na daidaiku da na gamayya don tabbatar da samun nasarar jagoranci.
COV/Abdullahi Tukur/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp