HausaTv:
2025-12-04@00:38:59 GMT

Masu Zanga-zanga Sun Farmawa Ofisoshin Jakadancin Amurka Da Na Faransa A DR Congo

Published: 29th, January 2025 GMT

Masu zanga-zanga sun kai hari kan ofisoshin jakadancin kasashen waje da dama hari a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC).

An bayar da rahoton cewa, fusatattun masu zanga-zangar sun kai wa ofisoshin jakadancin Amurka, Faransa, Belgium, Rwanda, Uganda, Kenya da Afirka ta Kudu hari.

Masu zanga-zangar dai na neman hadin kan kasashen waje da yunkurin kasa da kasa na shiga tsakani na soji da kuma dakatar da ‘yan tawayen M23 da ke ci gaba da mamaye wasu sassan yankin gabashi.

‘Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa amma masu zanga-zangar sun samu damar shiga sassan harabar, inda suka yi banka wuta.

Rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana yi da kungiyar ta M23 ya yi Kamari a baya bayan nan, inda suka kwace iko da Goma babban birnin gabashin Congo, ko da yake rundunar sojin Congon ta ce har yanzu tana iko da kashi 80 na birnin.

Masu zanga-zangar a Kinshasa sun bukaci kasashen duniya su matsa lamba kan kasar Rwanda kan ci gaban da dakarun ‘yan tawayen suka yi.

Tashin hankali a yankin da ake fama da rikicin kabilanci ya haifar da daya daga cikin manyan matsalolin jin kai a duniya.

A shekara ta 2012, ‘yan tawayen M23 sun mamaye birnin na Goma na wani dan lokaci kafin a tilasta musu janye dakarunsu a karkashin matsin lamba daga kasashen duniya.

A shekara ta 2021, dakarun ‘yan tawayen sun sake haduwa bisa tallafin da suke samu daga kasar Rwanda, a cewar gwamnatin Kinshasa da kwararrun MDD, saidai gwamnatin Kigali na mai musanta hakan.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Masu zanga zangar

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu

Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci.

Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara ba.

Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja

Sanata Bamidele, ya ce ƙudirin ya yi daidai da yunƙurin gwamnati da majalisa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.

Yayin gabatar da ƙudirin, ya ce garkuwa da mutane na ƙara yawaita, kuma ƙungiyoyin miyagu na amfani da shi wajen tara k6udi, abin da ke jefa jama’a cikin tsoro da kuma daƙile karatun yara a jihohi da dama.

Sanatoci da dama sun goyi bayan hukuncin kisa, inda suka bayyana cewa hakan zai zama gargaɗi ga masu aikata wannan mummunan laifi.

Wasu kuma sun nemi a hukunta bankunan da ke taimakawa wajen aikewa ko karɓar kuɗaɗen fansa, yayin da wasu suka ce ya kamata a daina yi wa ’yan ta’adda afuwa.

Majalisar ta tura ƙudirin zuwa kwamitoci na musamman domin bincike, tare da umarnin su kawo rahoto cikin makonni biyu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu
  • MDD Ta Amince Da Kudurori Biyu Masu Yin Tir Da HKI
  • Kamfanonin jiragen Sama Na Kasashen Yamma Na Neman Izinin Amurka Don Komawa Iran
  • Nijar ta maka kamfanin hakar uranium na Faransa Orano kotu
  • Amurka ta soke bada mafaka ga ‘yan kasashen Afirka 10
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 
  • Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran
  • Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi
  • Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa