Rahotanni da suke fitowa daga Bukavu sun ambaci cewa ‘yan tawayen kungiyoyin M 23 da kuma AFC sun kwace iko da filin sauran jiragen sama na Kavumu wanda yake da tazarar kilo mita 45 daga birnin.

mutanen sun kauracewa zirga-zirga akan titunan birninna  Bukavu saboda rashin tabbacin abinda zai biyo baya.

Mafi yawancin ‘yan siyasa a birnin sun buya,saboda karatowar ‘yan tawayen cikin birnin.

 Wasu rahotannin suna nuni da cewa, ‘yan tawayen sun shiga cikin birnin na  Bkavu, a jiya Lahadi.

Bukavu dai shi ne birni na biyu da ‘yan tawayen su ka kama daga farkon watan Janairu zuwa yanzu, bayan da su ka shiga cikin birnin Goma.

 An Shiga Rudani A Birnin Bukavu .

Sojojin DRC da kawayensu na kasar Burundi sun janye daga cikin barikokin birnin tun a ranar Juma’a da ita ce ranar da ‘yan tawayen su ka kwace iko da filin saukar jiragen sama.

An rika jin karar bindiga da ake harbe-harbe a cikin birnin da kuma wawason da ake yi a dakunan ajiya na hukumar abinci ta duniya ( WFP).

Kustawar da kungiyoyin ‘yan tawayen suke yi a cikin biranen DRC, yana haddasa fargaba akan yiyuwar barkewar yaki a cikin yakin. Kungiyar M 23 dai tana samun goyon bayan ne daga kasar Rwanda yayin da ita gwamnatin kasar DRC take da nata kawayen a cikin yankin da su ka hada da Brundi. MDD dai ta sha yin kira da a tsagaita wutar yaki da kawo karshe fadace-fadacen da ake yi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyaku sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa.

Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono.

Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure

Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su.

Hakan dai ya haifar da kauracewa ƙauyukan ga mazaunansu da suke da sauran numfashi inda a yanzu haka ake da ’yan gudun hijira sama da 3,500 da ke neman mafaka a cikin garin Bakori.

Kazalika, rahotanni sun kuma ce akwai wasu sama da 2,500 da ke garin Guga don neman mafaka.

’Yan gudun hijirar wadanda akasarinsu mata ne da ƙananan yara sun watsu a wurare daban daban.

Aminiya ta zagaya unguwan Kafaɗi da unguwar Ma’aru da ke Sabuwar Abuja a cikin garin na Bakori, inda wakilinmu ya tarar da cincirindon mata da ƙananan yara a rakuɓe, a gidajen ’yan uwa, wasu kuma a makarantun firamaren gwamnati da ke karamar hukumar ta Bakori.

A tattaunawar Wakilinmu da wasu daga cikin ’yan gudun hijira wadanda suka fito daga kauyaku daban-daban na jihar, sun nuna alhininsu game da yadda ’yan bindigar ke cin karensu ba babbaka a yankin.

Imrana Shafi’u wanda ’yan bindigar suka harbe shi a ƙafa har wuri biyu, wanda shi ya yi hijira ne daga kauyan Ɗan Marka, ya ce lamarin na da ban tsoro matuƙa.

A cewarsa, “Ni ma Allah ne ya sa zan rayu domin ’yan bindigan sun zaci na mutu ne.

“Domin da suka zo kanmu harbin kan mai uwa da wabi, suka yi ta yi, inda suka kashe mutane da dama.

“Ni ma dai Allah ne ya tsirar dani, domin duk wadanda nake tare da su duk an kashe su, ni kadai na tsira cikin ikon Allah,” in ji shi.

Ita kuwa Malama Marawiya wacce ta yi gudun hijira daga kauyan ’Yar Dabaru ta ce da rana tsaka ’yan bindiga suka keto cikin kauyan nasu, suka tarwatsasu sa’ilin da suka tasa ƙeyar mata sama da 10 kuma duk yawancinsu suna ɗauke da goyo suka yi cikin daji da su.

Marawiya ta kara da cewa kusan kwanakin matan 10 ke nan a hannun su kuma sun ce sai an biya kudin fansa har Naira miliyan daya da rabi kan kowanne mutum daya kafin a sake su.

Ta Kara da cewa “A da in suka dauki mutum bai wuce su ce a ba su Naira dubu ɗari biyar ba amma a wannan karon sai suka ce sai an biya har sama da naira miliyan daya da rabi ga kowanne mutum,” in ji ta.

Yusuf Usman, wanda suka yi sansani a wata makarantar Firamare ta Nadabo da ke cikin garin Bakori, ya ce kusan su ɗari uku ne suka yi gudun hijira daga kauyan Doma, cikinsu har da tsofaffi.

Ya kuma ce, “A haka muka tako da ƙafa muka yini muna tafiya tare da mata da yaran kanana har Allah ya kawo mu garin Bakori,” in ji shi.

Ya kara da cewa kusan shekara biyar kenan suna fama da wannan matsalar ta tsaro, kuma ba dare ba rana bare damina ko rani, haka ake shigowa kauyakun su ana kashe su sannan kuma a tasa ƙeyar su a tafi da su daji domin karɓan kuɗin fansa.

Shugaban kwamitin da ƙaramar hukumar Bakori ta kafa domin kula da ’yan gudun hijirar, Mallam Mamman Yaro Bakori, ya ce adadin ’yan gudun hijirar sun kai 3,500 a garin Bakori.

Ya Kara da cewa a garin Guga Kuma akwai akalla kimanin mutane 2,500 da suke gudun hijira a can.

Shugaban ya ce kuma kusan a kullum yawan su ƙaruwa yake yi, sannan suna warwatse ne a wurare daban daban a inda wasu suke zaune a gidajen ‘yan uwansu wasu kuma suna zaune ne a makarantar firamare ta Nadabo a cikin garin Bakori.

Sai dai ya ce tuni Shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Abubakar Barde ya bayar da umurnin kai masu tallafin kayan abinci sau uku a rana tare da kudin cefane don saukaka masu rayuwar da suke ciki.

Wasu na bayyana cewa a ‘yan kwanakinnan ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka kafa sansaninsu a dajin Guga da Kandarawa da Kakumi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Shirya Taron Bita Ga Kansiloli
  • Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawul
  • Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Lod Da Ke Jaffa Da Makami Mai Linzami
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa
  • An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa