DRC: ‘Yan Tawayen M 23 Sun Sha Alwashin Tunkarar Babban Birnin Kasar Kinshasha
Published: 1st, February 2025 GMT
Bayan da su ka kwace iko da birnin Goma dke gabashin kasar DRC, kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta sha alwashin kama hanyar shiga babban birnin kasar Kinsasha.
Wani daga shugabannin kungiyar ta M 23, Corneilla Nangaa ya furta cewa,: manufarmu ita ce, muna yin yaki ne saboda kishin Congo, ba muna yaki ne saboda samun ma’adanai ba, babu wani dalili na daban da ya sa muke yaki.
Da akwai wasu rahotanni da suke nuni da cewa, ‘yan tawayen na M 23 sun kama hanyar zuwa Bukavu, wanda shi ne birni mafi girma na biyu a yankin.
Nangaa ya ce babu wata gwamnati tsayayya a kasar Congo, domin Tshikedi ya riga ya rusa sojoji, ‘yansanda, kuma tsarin tafiyar da mulki, haka nan kuma ma’aikatar shari’a.”
Sai dai kuma ‘yan tawayen sun ce a shriye suke a bude tattaunawa domin a dama da su a cikin sha’anin tafiyar da kasar.
Kungiyoyin kasa da kasa suna yin kira da a tsagaita wutar yaki a kasar ta DRC.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan kasuwa na duniya da su shiga harkokin tattalin arziki da zuba hannun jari a Iran.
A yayin bikin bude baje koli karo na bakwai na baje kolin kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa kasashen ketare (Iran Expo 2025) a safiyar yau Litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi maraba da baki na kasashen waje da suka halarci wannan baje kolin, yana mai cewa, “Ko da yake ana gabatar musu da wani hoto na daban da ya yi hannun riga da hakikanin Iran da al’ummar kasarta a ketare, amma Iran kasa ce mai karbar baki, kuma al’ummarta masu tausayi da nuna jin kai.”
Yana mai jaddada cewa: Iran wata kafa ce da ta dace da zuba hannun jarin kasuwanci da yawon bude ido na ketare, Pezeshkian ya bayyana cewa da wannan karfin, kuma ta hanyar ciniki, zuba hannun jari, da hadin gwiwa, za a iya samar da makoma mai haske ga duniya, mai cike da tsaro da zaman lafiya.
Ya kuma yi nuni da cewa: Yake-yaken da suka gani a duniya sun samo asali ne sakamakon rashin mutunta hakkokin bil’adama da na kasashe, Pezeshkian ya jaddada mutunta yankin kasar Iran da hakkokin kasashe, yana mai bayyana Shirin Iran na gudanar da duk wani hadin gwiwa a fannin kimiyya, tattalin arziki, siyasa, da zamantakewa da duniya, da kuma mika ilimi ga sauran kasashe ba tare da iyakancewa ba.