HausaTv:
2025-07-31@17:54:28 GMT

‘Yan Tawayen M23 Sun Kara Shimfida Ikonsu A Garin Goma

Published: 29th, January 2025 GMT

Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake  gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar.

A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a tsagaita wutar yaki.

Da safiyar yau Laraba an sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Goma bayan da a jiya mazaunansa fiye da miliyan biyu su ka kasance a cikin zullumi da fargaba.

Mazauna birnin na Goma sun fadawa kamfanin dillancin Labarun (AP) cewa ‘yan tawayen kungiyar ta M 23 ne suke rike da mafi yawancin birnin.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai kungiyar ta M 23 ta sanar da cewa ta kame wannan birnin na Goma bayan mayakanta suka dauki kusan mako daya suna matsawa kusa da shi.

Kungiyar M 23 daya ce daga cikin kungiyoyin tawaye 100 da ake da su a cikin kasar ta jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kowace daya daga cikinsu take son shimfida iko a cikin yankunan da ake da ma’adanai.

Ita dai kasar DRC tana da dimbin arzikin ma’adanai da suke kwance a karkashin kasarta, da ya sa kasashen makwabta da kuma na nesa suke taimakawa  wasu daga cikin kungiyoyin ‘yan tawaye saboda su yi kaso mu raba da arzikin wannan kasar.

Tun da kasar ta Sami ‘yanci daga kasar Belgium, ba ta sami zaman lafiya ba har zuwa yanzu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 

Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya.

Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji.

Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma ne ma’auratan, waɗanda makwabta ne ga mamacin, suka fara faɗa ne bayan wata rashin fahimta, shi kuma Ayuba, bayan jin hayaniyar, ya fito daga ɗakinsa don shiga tsakani.

A cewarsa, mamacin ya dawo ne daga gonarsa kuma yana shirin yin wanka lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana dukan matarsa.

Ya ce, Ayuba nan take ya ajiye soso da gugar ruwansa ya ruga don shiga tsakani amma ya faɗi sumamme a yayin.

Ayuba, wanda aka yi imanin yana cikin koshin lafiya kafin faruwar lamarin, an garzaya da shi asibiti a garin Gawu, inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwarsa.

Sarkin yankin, bayan samun labarin lamarin, ya sanar da ’yan banga tare da ba da umarnin kama ma’auratan, waɗanda daga baya aka mika su ga jami’an tsaro a Gawu.

Ibrahim, daya daga cikin ’yan bangan, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, “Mun fahimci cewa ƙaramar rashin fahimta ce kawai ta kai ga faɗan tsakanin makwabcin mamacin da matarsa.”

Ya ƙara da cewa an kai gawar mamacin kauyensa na Paiko a Jihar Neja don binnewa.

’Yan sanda a yankin Gawu sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce har yanzu ana ci gaba da bincike.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilan Da Suka Sa Canada Ta Goyi Bayan Kafa Kasar Falasɗinu
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa
  • Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 
  • Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran
  • Hamas: HKI Da Amurka Sun Janye Daga Tattaunawa Ne Don Sake Damarar Yaki
  • Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan