Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasanta
Published: 17th, April 2025 GMT
Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da gwamnatin Najeriya.
Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar.
Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya ba ne, abu ne na Allah.
Takwaransa na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa nan gaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su gana da shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, a matsayin ci gaban wannan daidaitawa.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka sanya hannu a kai, ta zama, “darasi ga duk wasu ƙasashen duniya, domin yanzu an shiga wani lokaci da ake fama da tashe tashen hankali. To yanzu mu abin da a muka a tsakaninmu ya zama abin koyi.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnatin sojin Nijar Najeriya Nijar Tuggar Yamai
এছাড়াও পড়ুন:
ASUU Ta Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Albashin Watan Yuni
Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta.
ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya.
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun.
Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba.
“Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen mutanen da ke da alhakin sakin kuɗin ne,” in ji Piwuna.
Ya ƙara da cewa sauyi tsarin biyan albashi daga IPPIS zuwa GIFMIS ya ƙara jefa malamai cikin wahala.
ASUU ta ce duk wata Jami’a da ba a biya malamanta albashin Yuni kafin 7 ga Yuli ba, to, ya kamata su fara yajin aiki nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp