Gwamnatin Sakkwato na biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 – NLC
Published: 10th, April 2025 GMT
Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Sakkwato (NLC), ta musanta iƙirarin da shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), Ali Kankara, ya yi cewa gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba.
Shugaban NLC na jihar, Kwamared Aliyu Abdullahi, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa Gwamnatin Sakkwato ta fara biyan sabon albashin tun a watan Janairu ga dukkanin ma’aikatan jihar, ciki har da na ƙananan hukumomi.
Ya ce: “Sakkwato ce jiha ta farko da ta fara biyan sabon albashi na dubu 70, kuma ma’aikatan gwamnati da na ƙananan hukumomi na amfana da shi.
“Maganar shugaban NULGE na ƙasa ba gaskiya ba ce.”
Ya ƙara da cewa bai kamata shugaban NULGE ya faɗi irin wannan magana ba tare da ya bincika gaskiyar al’amari ba.
Kwamared Aliyu, ya yaba wa Gwamna Ahmad Aliyu bisa ƙoƙarinsa na biyan ma’aikata haƙƙoƙinsu da kuma dawo da kuɗin tafiyar da ofisoshi, biyan bashin fansho da sauran haƙƙoƙin ma’aikata.
Sai dai wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa ba dukkanin ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar ne ke karɓar albashin dubu 70 ba.
Wani ma’aikaci ya ce: “Wasu daga cikinmu da muke karɓar dubu 18 a da, yanzu muna karɓar dubu 30, yayin da waɗanda ke karbar dubu takwas a baya, yanzu gwamnati na biyansu dubu 20.”
Wannan ya nuna cewa duk da gwamnati na ƙoƙarin biyan sabon albashi, har yanzu ba a kai ga kowa ya samu dubu 70 ba a matakin ƙananan hukumomi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Mafi karancin albashi Sakkwato biyan sabon
এছাড়াও পড়ুন:
Portugal ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 a karon farko
Kasar Portugal ta kafa tarihi a birnin Doha na Qatar bayan da ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 (U-17) a karon farko, inda ta doke Austria da ci 1-0 a wasan ƙarshe.
An jefa ƙwallon da ta bai wa Portugal nasara ne ta hannun Anisio Cabral, wanda ya ci a minti na 32 da fara buga wasan a filin wasa na Khalifa.
Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru BauchiA hanyarta ta kaiwa wasan ƙarshen, Portugal ta doke Brazil a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Austria ta fitar da Italiya bayan lallasa ta da ci 2-0.
Wannan nasara ita ce ta farko a tarihin Portugal tun da aka fara gasar, wanda hakan ya sanya sunanta cikin jerin ƙasashen da suka taɓa ɗaga kofin.
Nijeriya ce ƙasa mafi nasara a gasar U-17, inda ta lashe ta sau biyar. Sai Brazil wacce ta lashe sau uku, Ghana da Mexico wadanda suka lashe sau biyu-biyu.
Akwa kuma Jamus, Ingila, Switzerland, Faransa da Saudiyya kuwa kowacce ta lashe sau daya.