A Cikin Shekara Daya EFCC Ta Kwato Dalar Amurka Miliyan 500
Published: 11th, March 2025 GMT
Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da sauran dangoginsa da sun kai ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975.
A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin hukumar ta EFCC ta bayyana cewa, ta sa an hukunta masu laifi har su 4,000 wanda shi ne adadi mafi girma tun kafa ta.
Tuni an zuba wasu kudaden da aka kwato a cikin ayyukan gwamnati.
A karshen rahoton hukumar “Transparency International” ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 140, a jerin masu fama da cin hanci da rashawa, bayan da a baya ta kasance ta 180.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza
Amma yanzu, sabon tsarin ya rage wa’adin bizar zuwa wata uku kacal, kuma mutum zai iya shiga sau ɗaya ne kawai da ita.
Ma’aikatar ta ce wannan mataki yana daga cikin gyaran tsarin alaƙar diflomasiyya da tsaro da Amurka ke yi da sauran ƙasashe.
Sai dai ta bayyana cewa za a iya sauya wannan tsari a nan gaba, idan an samu canji a dangantakar diflomasiyya, tsaro ko dokokin shiga ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp