Takunkumi kan Musulmi masu ibada a Indiya
Published: 11th, March 2025 GMT
Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta Indiya ya bukaci musulmi da su yi sallar Juma’a a gida.
A cewar radiyon gwamnatin Pakistan, Firimiyan Jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath ya kare kalaman jami’in ‘yan sandan game da musulmi, inda ya ce, “A yayin da ake gudanar da bukukuwan Holi sau daya a shekara, ana gudanar da sallar Juma’a a duk mako.
Ya bayyana jami’in a matsayin gwarzo jarumi, tare da bayyana cewa wannan ra’ayi nasa daidai ko da kuwa hakan ya bakantawa wasu.
Ya kara da cewa: “Bikin Holi ya fi sallar Juma’a muhimmanci, amma ana gudanar da shi sau daya ne kawai a shekara, don haka gudanar da shi yana da fifiko a kan Jum’a.”
Jami’in ‘yan sandan da ake magana a kai ya fada a wata hira da manema labarai cewa: “Idan musulmi suna son fita to babu matsala, kuma idan aka watsa musu musu kaloli to kada su yi korafi kan hakan, ko kuma su zauna a gida.
Firimiyan Uttar Pradesh ya bayar da hujjar cewa ana iya jinkirta Sallar Juma’a har zuwa lokacin da ‘yan Hindus za su kammala bukukuwansu, ko kuma kowane musulmi ya yi sallar Juma’a a gida.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da malamin addinin musulinci Maulana Khalid Rashid Faranji ya bayyana cewa za a gudanar da sallar Juma’a kamar yadda aka saba a ranar 14 ga watan Maris, ranar da ‘yan addinin Hindus suke gudanar da wasu bukukuwansu na addini.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sallar Juma a a gudanar da
এছাড়াও পড়ুন:
An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa
An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare da kafa wuraren bincike domin magance matsalar rashin tsaro da ta biyo bayan kisan wata amarya mai shekaru 22, Zainab Ibrahim.
An yanke wannan shawara ne a taron da aka gudanar a Hadejia, wanda ya haɗa jami’an majalisar masarautar da hukumomin ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma.
Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalmaManufar taron ita ce samo mafita ga matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin.
Da yake jawabi a madadin majalisar masarauta, Galadiman Hadejia, Usman Abdul’aziz, ya nuna damuwa matuƙa game da yawaitar hare-haren da ake kai wa jama’a.
Ya buƙaci shugabannin yankin da su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
An tsinci gawar Zainab Ibrahim, wacce aka ɗaura mata aure a baya-bayan nan, kwance cikin jini a gidanta da ke unguwar Warware.
Lamarin ya tayar da hankalin al’umma, lamarin da ya tilasta hukumomi ɗaukar matakan tsaro cikin gaggawa.
Bayan tattaunawa, an amince da sanya dokar hana fita daga ƙarfe 12 na dare zuwa 4 na Asuba, tare da kafa wuraren binciken tsaro.
Shugaban kwamitin tsaro na Ƙaramar Hukumar Hadejia, Ahmed Ari, ya bayyana cewa dokar hana fitar za ta taimaka wajen rage aikata laifuka da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma roƙi al’ummar yankin su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da nasarar waɗannan matakai.