NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya
Published: 11th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da ɗaukar salo iri-iri yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasaƙe suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ɗiga mata ɗanba.
A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da rade-radi a kana bin da wasu jiga-jigan ’yan siyasar ƙasar nan, musamman ’yan adawa da ’ya’yan jam’iyya mai mulki waɗanda suke takun saƙa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suke ƙullawa
Yanzu ta fara wari, an ji Malam Nasiru ya bayar da sanarwar ficewarsa daga jam’iyyar APC da tsallakawa zuwa SDP.
Shin ko me zai biyo bayan wannan girgiza da tsallen baɗaken Malam Nasiru da dirarsa suka haifar?
Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai duba.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Siyasar Nijeriya Zaɓen 2027
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
A ƙoƙarinta na ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa.
Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin
A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa.
Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa garkuwar jiki.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Muhammad Abdullahi, ya yi wa mahalarta horon bayani kan muhimmancin tsafta yayin al’ada domin gujewa kamuwa da cututtuka.
Shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun Gabas, ya shawarci mahalarta da su mai da hankali ga sashen aikace-aikace na yadda ake sarrafa audugar mata a gida yayin horon.
Usman Muhammad Zaria