Gidauniyar Marayu Riyadissalihin ta Funtua Ta Raba Kayayyakin Ramadan
Published: 11th, March 2025 GMT
Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu.
Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a wani bangare na kokarinsa na yada albarkar watan Ramadan.
A cewarsa, kula da marayu ba kawai nauyin zamantakewa ba ne, amma wata gagarumar ibada ce da ke karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma.
Da yake jawabi yayin taron rabon kayan, sakataren gidauniyar, Bashir Muhammad King, ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace.
Ya kuma mika godiya ga duk wadanda suka bayar da gudunmawa domin nasarar shirin, yana mai jaddada cewa irin wannan karamci yana da matukar tasiri wajen kawo fata da sauki ga rayuwar mabukata.
Taron rabon kayan ya kasance mai cike da farin ciki da godiya daga marayu da masu kula da su, wanda hakan ya kara nuna muhimmancin hadin kan al’umma wajen daga darajar rayuwar marayu da marasa galihu.
COV/Magaji Yakawada
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gidauniya Kayayyaki Marayu Rabo Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Nada Kwamishina
Majalisar dokokin jihar Kano ta wanke Arc. Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jiha.
A yayin aikin tantance kwamishinonin, ya jaddada mahimmancin kiyaye babban tsarin ga birane da yankunan karkara.
Ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmowarsa wajen sauke nauyin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora masa.
Adamu wanda a baya ya taba rike mukamin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tsare-Tsare Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), ya bayyana jin dadinsa ga majalisar a yayin zaman majalisar.
Shugaban majalisar Jibril Ismail Falgore ya bukaci Adamu da ya kara samun nasarori a KNUPDA tare da yi masa fatan Alheri a sabon mukaminsa.
Nadin Adamu ya yi daidai da ikon da tsarin mulki na Gwamna Yusuf ya ba shi na nada ‘yan majalisar zartarwa ta jiha.
KHADIJAH ALIYU