Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa
Published: 8th, March 2025 GMT
Majaliar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar.
A cewarsa, dakatar da Sanata Natasha, mataki ne da duka majalisar ta ɗauka, saboda saɓa dokokinta da ta yi kamar yadda kwamitin ɗa’a da ladabtarwa ya tabbatar.
“An dakatar da ita ne saboda yadda take keta dokoki da ƙa’dojin majalisa, da nuna rashin ɗa’a a majalisar, wannan shi ne laifinta babu daɗi babu ragi.”
Sanarwar ta ce da a ce Sanata Natasha ta yi aiki da dokoki da ƙa’idojin majalisar, da majalisar za ta karɓi ƙorafinta, kamar yadda doka ta tanada.
“Amma ba ta bi ƙa’ida da dokokin da suka kafa majalisar da take aiki a cikinta ba.”
Sanata Bamidele ya ce majalisar ta ɗauki matakin dakatar da Sanata Natasha ne bisa shawarar kwamitin ɗa’a, wanda ya same ta da laifin saɓa wa sashe na 6.1 da sashe na 6.2 na dokokin majalisar.
Sanarwar ta kuma zayyano wasu laifuka biyar da ta ce Sanata Natasha ta aikata, ciki har da ƙin zama a kujerar da aka sauya mata a lokacin zaman majalisar na ranar 25 ga watan Fabrairu, da yin magana ba tare da amincewar jagoran zaman majalisar ba, da yin kalaman zagi da rashin girmamawa da shugabancin majalisar.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan har na tsawon wattani shida a kan laifin saɓa wa dokokin majalisar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dattawa dakatar da Sanata Natasha majalisar da a majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas
Wata tsohuwa mai shekara 80 a kasar Turkiyya za ta shafe sama da shekara 4 a gidan yari, saboda ta daki jikarta ’yar shekara 18 da silifa a lokacin da suke takaddama.
Asiye Kaytan na zaune tare da jikarta Vural a unguwar Topraklık da ke Denizli a Kudu maso Yammacin Turkiyya.
Tuntuni dai iyayen yarinyar suka rabu, inda tsohuwar mai shekara 80 take kulawa da ita fiye da kanta.
A ranar 9 ga Agustan bara, bayan Vural ta dawo daga aiki, ta fada wa kakarta cewa, za ta fita waje tare da wasu abokanta.
Tsohuwar ta ji tsoron fitar don kare lafiyarta, ta ce ba za ta yarda ba, har ma ta kulle kofa don tabbatar da cewa Vural ba ta iya fita ba.
Zuwa wani lokaci, sai budurwar ta yi kokarin bude kofar, inda Kaytan ta dauko takalmi silifas, ta dake ta.
Vural ta rama dukan da kakarta ta yi mata a ka da wayarta. Kaytan ta fara zubar da jini, inda yarinyar ta kira motar asibiti.
“Jikata ta so fita da yamma, amma na hana ta, na kulle kofa,”
Kaytan ta shaida wa jaridar Sabah News. “Na buge ta a hannu da silifas, sai ta buge ni da wayarta a ka. Lokacin da na fara zubar da jini, sai ta tsorata ta kira motar daukar marasa lafiya.”
Kaytan da jikarta ba su kai kara a kan junansu ba, amma sun bayyana wa wadanda suka amsa da farko yadda tsohuwar ta samu rauni a ka, inda suka kai rahoto a asibitin Jihar Denizli, wanda daga baya aka mika wa ’yan sandan yankin.
An gayyaci matan biyu domin amsa tambayoyi, kuma duk da bayyana cewa sun sasanta rikicin nasu kuma sun yi sulhu, sai aka buɗe ƙofar ƙarar jama’a, kuma ofishin mai shigar da kara na gwamnati ya shigar da karar kakar mai shekara 80.
A shari’ar tasu, masu gabatar da kara sun yi zargin cewa, silifas da Kaytan ta yi amfani da shi wajen dukan jikarta makami ne, kuma yarinyar ’yar shekara 18 ta yi kokarin kare kanta ne a lokacin da ta bugi kakarta da wayarta.
An kuma tuhumi kakar da tauye ’yancin dan-adam saboda ta kulle Vural a cikin gidanta tare da hana ta fita, zargin da zai iya kai ga hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari.
A ranar 25 ga watan Fabrairu ne kotun hukunta manyan laifuka ta 12 ta kasar ta yanke wa Asiye Kaytan hukuncin daurin shekaru 2 da wata 6 a gidan yari saboda laifin ‘tauye ’yancin dan-adam ta hanyar amfani da karfi ko barazana ko yaudara da kuma ƙarin shekaru 2 da watanni 6 kan amfani da “makami” wajen aikata laifin da ta yi wa jikarta.
Daga ƙarshe an rage hukuncin zuwa shekaru 4 da watanni 2, amma lauyan Kaytan ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Idan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke mata, za ta je gidan yari.
“Zan shiga kurkuku ina da shekara 80? Ta yaya zan zauna a can? An yi mini tiyata, kuma ina tafiya da kyar, za su saka ni a kurkuku saboda silifas,” tsohuwar ta yi kuka.
‘‘Babu wanda ya isa ya daki yaronsa da silifas saboda ana daukar sa a matsayin makami. Ba ni da masaniyan cewa silifas ya zama makami’’, in ji ta. “
An yi wa kakata hukuncin zaman gidan yari ne saboda ta doke ni da silifas, ta hana ni fita daga gidan. Ban so haka ta kasance ba, ban kai karar ta ba, amma an bude karar jama’a,” in ji Asiye Vural.