Sojojin Isra’ila Sun Kai Hari A Kan Masallatan Nablus A Ranar Juma’ar Farko Ta Watan Ramadan
Published: 8th, March 2025 GMT
Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan wasu masallatai a birnin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan a ranar Juma’a ta farko ta watan Ramadan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, a safiyar ranar Juma’a sojojin gwamnatin Isra’ila sun kutsa kai cikin wasu masallatai shida na birnin Nablus, inda suka hana gudanar da salla.
Har ila yau, sun kame wasu Falasdinawa uku a lokacin da suke kutsawa cikin Nablus.
Rahotanni sun ce sojojin na Isra’ila sun harba harsasai masu rai, da gurneti da bama-bamai masu guba a yayin da dakarunsu suka mamaye wasu unguwanni a birnin.
Ko a ranar Alhamis din da ta gabata hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ci gaba da cin zarafi da gwamnatin Isra’ila ke yi kan yankin yammacin kogin Jordan na daga cikin shirin gwamnatin kasar na mamaye yankin.
A watan Yulin 2024, Kotun Duniya (ICJ) ta yanke hukuncin mamayar da Isra’ila ta dade tana yi a yankunan Falasdinawa ba bisa ka’ida ba, inda ta bukaci a kwashe duk wasu haramtattun matsugunan da ke Yammacin Kogin Jordan da gabashin Quds.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila sun
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
Rahotanni da muka samu sun nuna cew wasu yan ta’adda sun kashe wasu dakarun sa kai guda biyu a kudu masu gabashin iran a yankin sisitan Baluchistan.
Jami’In huda da jama’a na dakarun kare juyi yayi karin harke game da harin da aka kai, yace an kashe mutane ne yayin da suke kokarin ketare da jami’an tsaro suna tafiya akan babbar hanyar da ta hada birnin kashsh dake lardin da kuma babban birnin zahidan
An bayyana cewa wanda abin ya shafa sun hada da Esma’il shavarzi da kuma mukhtar shahouze da kuma wadanda suka samu mummuan rauni a lokacin kai harin
Lardin sistan baluchestan na da iyaka da kasar Pakistan da ya dade yana fuskantar tashe tashen hankula kan fararen hula da kuma jami’an tsaro
Hukumomin yankin sun sha bin asalin tushen irin wadannan hare-hare zuwa cibiyoyin leken asirin na kasashen waje dake nuna goyon bayan yan’ taa’dda dake irin wadannan ayyukan a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci