Aminiya:
2025-07-31@13:51:26 GMT

Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu

Published: 25th, February 2025 GMT

Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ƙaryata zargin da tsohon abokinsa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi masa na neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2031.

A wata hira da aka yi da El-Rufai cikin dare ne tsohon gwamnan Kadunan ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu yana da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.

A yayin hirar da aka yi da shi a cikin dare a kafar Arise TV ranar Litinin, El-Rufai ya bayyana cewa sun raba jiha da tsohon abokin nasa Nuhu Ribadu da kuma Gwamnan Kaduna mai ci kuma magajinsa, Sanata Uba Sani, yanzu duk  ba abokansa ba ne.

Amma martaninsa, a cikin sakon da ya fitar jim kaɗan da ta tsohon gwamnan, Nuhu Ribadu ya ce, ƙarya El-Rufai yake yi cewa ya taɓa yin maganar tsayawarsa takarar 2031 da tsohon gwamnan ko da wani.

NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba ni muƙamin Minista — El-Rufai

“Ba don kada in yi shiru a ɗauka maganar El-Rufai gaskiya ba ce, da na yi watsi da shi. Ni tulin aikin da ke gabana a yanzu ma kaɗai ya ishe ni, balle in tsaya ɓata lokaci ina cacar baka da El-Rufai ko waninsa a kafofin watsa labarai.

Martanin Nuhu Ribadu ga El-Rufai

“Duk da cewa ya sha takala ta da caccaka ta, amma saboda mutunta tsohuwar abotarmu, ban taɓa fitowa na aibata shi ba, kun ba zan fara ba.

“Amma ina roƙon jama’a su yi watsi da maganganun da El-Rufai ya yi a kaina.

“Domin kawar da shakku, babu mahalukin da na taɓa magana da shi cewa zan nemi takarar shugaban ƙasa a 2031. Abun da na sa a gaba shi ne ganin Najeriya ta bunƙasa da kuma nasarar Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

“Saboda haka ina roƙon El-Rufai ya ƙyale Ni in fuskanci aikin yi wa kasa hidima da ke gabana, kamar yadda ni ma ban shiga masa harkokinsa ba.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: takarar shugaban ƙasa zaɓen 2031 El Rufai ya

এছাড়াও পড়ুন:

Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi

Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya kammala rahoton aikinsa na wucin gadi.

 

Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin da ke Karaye.

 

Ya ce rahoton ya ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi aikin Hajji tun daga lokacin da aka ƙaddamar da kwamitin a birnin Makkah, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf.

 

“Rahoton ya kunshi cikakken bayani kan ayyukan da kwamitin ya gudanar zuwa yanzu, kuma zai kasance muhimmin ɓangare na rahoton ƙarshe da za a miƙa ga Gwamna,” In ji shi.

 

Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta rigaya ta tattara nata cikakken rahoton, wanda za a mika wa Gwamnan nan ba da daɗewa ba.

 

A nasa jawabin, Sarkin Karaye ya nuna godiya ƙwarai ga Gwamnan Jihar bisa amincewa da baiwa kwamitin damar gudanar da wannan aiki mai muhimmanci.

 

Shugaban Hukumar gudanarwa na hukumar  Alhaji Yusif Lawan, ya bayyana godiya ga Sarkin Karaye bisa sadaukarwa da haɗin kai da ya bayar, wanda ya taimaka wajen samun nasarar aikin kwamitin.

 

Abdullahi Jalaluddeen

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yanke Wa Mai Gadi Da Mai Dafa Abinci Hukuncin Kisa Kan Kashe Tsohon Kwamishina A Katsina
  • Majalisar Kasa Na Duba yiwuwar Dawo Da Gwamnan Jihar Rivers Fabura Kafin Cikar Wa’adin Watanni Shida.
  • Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila
  • Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Bayyana Shirinsa Na Sake Tsayawa Takarar Shugabanci Karo Na Hudu
  • Gwamnan Kaduna Ya Sauke Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ya Maye Gurbinsa Da Maiyaki
  • Ku Daina Kashe Mutane Ko Ku Miƙa Wuya – Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Bindiga
  • Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi
  • Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Abdulkadir Ibrahim A Matsayin Sabon Sarkin Katsinan Gusau Na 16
  • Tsohon Ɗan Takarar Mataimakin Gwamnan Kaduna Na PDP Ya Koma ADC
  • SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa