Jigilar Fasinjoji Da Jiragen Kasa Masu Zirga Zirga Cikin Biranen Sin Suka Yi Ta Karu Da Kaso 9.5 A 2024
Published: 30th, January 2025 GMT
Adadin jigilar fasinjoji da jiragen kasa masu zirga zirga cikin biranen kasar Sin suka yi a shekarar 2024, ya karu da kimanin biliyan 2.8 ko kuma kaso 9.5 a kan na shekarar 2023.
A cewar ma’aikatar kula da sufuri ta kasar, a baran, jimilar jigilar fasinjoji da jiragen suka yi ya kai biliyan 32.24.
Zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2024, tsawon tafiyar da jirage 325 suka yi a fadin birane 54 na kasar Sin, ya kai kilomita 10,945.
এছাড়াও পড়ুন:
Mutanen Sweida Na Kasar Siriya Suna Fama da Rashin Abinci da Ruwa
A yankin sweida na kudancin kasar Siriya mazauna wurin sun bayyana cewa abinci da ruwa da kuma kayakin bukatu nay au da kullum sun fara karanci sosai a yankin saboda yakin makonni uku da suke fafatawa da sojojin sabuwar gwamnati a Damascus.
Jaridar The National ta Amurka ta bayyana cewa yankin sweida na kudancin kasar Siriya wanda kuma HKI ta dade tana shigowa yankin ta fita a halin nyanzu yana fama da karancin abinci da ruwansha. Sannan da alamun har yanzun sojojin sabuwar gwamnatin kasar Siriya tana ci gaba da hana shigowar abinci da ruwa yankin duk tare da shelanta tsagaita wuta da aka yi.
Labarin ya kara da cewa. an kashe daruruwan mutane a fafatawar da mayakan hTI suka yi da drsawa da suka fi rinjaye a yankin da kuma wasu kananan kabilu a yankin.
Tun lokacinda HKI tare da taimakin kasashen turkiya da sauran kasashen yamma suka kifar da gwamnatin Bashar al-asad, kasar Siriya take fama da karin kashe-kashe na kabilanci da na addini a kasar.