An Bukaci Ma’aikatun Gwamnati Su Rika Yin Kasafin Da Zai Amfani ‘Yan Nijeriya
Published: 28th, January 2025 GMT
Kungiyar masu ruwa da tsakin masana’antu a fannin mai ta Najeriya NEITI da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, na kokarin kwato kusan dala biliyan shida da kuma wani naira biliyan 66 da gwamnatin tarayya ke bin gwamnatin tarayya bashin.
Sakataren zartarwa na hukumar Mista Orji Ogbonnaya Orji, wanda ya bayyana haka a lokacin kare kasafin kudin 2025 a gaban kwamitin majalisar kan albarkatun man fetur.
Mista Orji Ogbonnaya, ya bayyana cewa tuni hukumar ta gabatar da dukkan rahotannin da ta ke a masana’antar hako mai ga majalisar a wani bangare na matakan tabbatar da samun nasarar kwato kudade daga hukumomin gwamnati.
Ya ce wasu daga cikin abubuwan da hukumar ta sa a gaba a shekarar 2025 sun hada da gudanar da rahoton masana’antu na fannin iskar gas da ma’adinai, da tantance kudaden da doka ta tanada, bincike kan ainihin adadin gidaje mai da ake amfani da su a Najeriya, da kuma aiwatar da binciken ra’ayi jama’a na kasa.
Sakataren zartarwa, ya bayyana cewa NEITI a matsayin hukumar da aka kafa domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkar man fetur da iskar gas a Najeriya ciki har da bangaren ma’adinai, ta sami kasafin kudin shekarar 2025 na Naira biliyan 6.5.
A nasa jawabin shugaban kwamitin kula da albarkatun man fetur na majalisar Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ya jaddada muhimmiyar rawar da hukumar ta ke takawa a fannin man fetur, ya kuma ba da tabbacin cewa kwamitin a shirye yake na mara masa baya wajen gudanar da ayyukansa.
Alhaji Alhassan Doguwa, ya shawarci shugabannin hukumar da su ci gaba da sa kaimi ga jin dadin ‘yan Nijeriya a duk lokacin da suke shirya kasafin kudin shekara bisa la’akari da yanayin tattalin arzikin da talakawa ke fuskanta daga sassa daban-daban na kasar nan.
COV: TSIBIRI/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Majalisar Kasa tattalin arziki
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar.
Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar.
“Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.”
“Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da haƙuri yayin aikin Hajji. Da fatan za ku halarci dukkan tarukan bita da kai da aka shirya, domin muhimmanci su Alhazai” In ji shi.
Labbo, wanda ya sa ido a kan shirin rigakafin tare da bai wa wani mahajjaci daga Hadejia allurar farko, ya bayyana cewa aikin rigakafin zai ci gaba har zuwa lokacin tafiyar su zuwa ƙasa mai tsarki.
Haka kuma, Shugaban cibiyar lafiya a matakin farko, Dr. Bala Ismaila, ya bayyana muhimmancin allurar rigakafin da ake bayarwa, wanda ya haɗa da rigakafin cutar sankarau, cutar shan inna, da kuma cutar zazzabin cizon sauro (yellow fever).
Ya kuma yi bayani kan yiwuwar fuskantar rashin lafiya bayan rigakafin, inda ya shawarci mahajjata da su nemi kulawar likita cikin gaggawa idan suka fuskanci hakan ko wata matsala da ta wuce kima.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana gudanar da aikin rigakafin a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.
Usman Muhammad Zaria