Kwamitin Zaman Lafiya Da Tsaro Na AU Yai Yi Zaman Gaggawa Kan Halin Da Ake Ciki A Gabashin DRC
Published: 28th, January 2025 GMT
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC).
Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da ake yi tsakanin dakarun Kongo da mayakan M23″ in ji Paschal Chem-Langhee, mai magana da yawun kwamitin, yayin da al’amura ke kazanta a Goma, babban birnin gabashin DRC.
Kafin nan daruruwan ma’aikatan MDD da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sun tsere zuwa makociyar kasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo din suka “mika wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan tawayen M23 sun kwace iko da birnin na Goma mai muhimmanci a Kongo.
‘Yan tawayen na M23, waɗanda ake zargin suna samun goyon bayan Rwanda, sun zafafa hare-hare a gabashin Kongo a makon jiya, inda suka kwace muhimman birane, Sai dai Shugaban Rwanda Paul Kagame ya sha musanta zargin cewa yana goyon bayan ‘yan tawayen.
Shugaban Kenya William Ruto, wanda yake shugabancin kasashen Gabashin Afirka ya sanar a ranar Lahadi cewa, kungiyar za ta gudanar da wani taro na musamman a cikin sa’o’i 48 don tunkarar rikicin da yake yaduwa a Jamhuriyar Dimukuradiyar Kongo.
Ruto ya tabbatar da cewa tun da farko ya tattauna da Shugaban DRC Kongo Felix Tshisekedi da Shugaban Rwanda Paul Kagame, wadanda dukkansu suka amince za su halarci taron.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta shiga tsakani don sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO).
Rikicin ya samo asali ne daga katse wutar lantarki da asibitin ya zargi KEDCO da yi, inda ya ce hakan ya kawo cikas ga ayyukan lafiya masu muhimmanci a asibitin, ciki har da zargin mutuwar marasa lafiya.
Sasantawar da Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya jagoranta ta biyo bayan zarge-zargen cewa katsewar wutar ta haddasa mutuwar wasu marasa lafiya da ke kan na’urar taimakon numfashi a asibitin.
Sai dai KEDCO ya musanta zargin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, yana mai cewa asibitin na kokarin bata sunansa ne kawai.
A cewar mai magana da yawun ‘yan sanda na Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, an gudanar da taron sasancin ne a hedikwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai, inda aka zauna da Shugaban asibitin, Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe, da Shugaban KEDCO, Abubakar Shuaibu Jimeta.
Taron ya mayar da hankali ne kan warware tankiyar da kuma dawo da wutar lantarki ga asibitin, wanda ke ya fuskanci matsaloli sakamakon katse wutar.
Sanarwar ta ce, “Bangarorin biyu sun nuna godiya ga matakin gaggawa da ‘yan sanda suka dauka. KEDCO ya amince da dawo da wutar lantarki nan take, alamar cewa rikicin ya zo karshe.”
Kiyawa ya kara da cewa, “Rundunar ‘Yan Sanda ta jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da ci gaba da aiki ba tare da tangarda ba a bangaren kiwon lafiya.”
Sanarwar ta kuma ce kwamishinan ‘yan sanda ya yaba wa AKTH da KEDCO bisa hadin kai, tare da alkawarin ci gaba da goyon baya don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.