Guteress Ya Damu Game Da Matakin Trump Na Dakatar Da Taimakon Kasashen Waje Daga Amurka
Published: 28th, January 2025 GMT
Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya bayyana damuwarsa game da matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na dakatar da taimakon kasashen waje daga Amurka yayin da sabuwar gwamnatin Amurka ke aiwatar da sabbin manufofinta na ketare, kamar yadda mai magana da yawun Guterres ya bayyana.
“Ya yi kira da a yi la’akari da halin da ake ciki don tabbatar da ci gaba da samar da muhimman ayyukan ci gaba da na jin kai ga al’ummomin da ke da rauni a duniya,” in ji Stephane Dujarric ga manema labarai.
” Ya ce akwai al’umomin da suka dogara da wannan tallafin,” inda ya kara da cewa Amurka na “daya daga cikin manyan masu ba da agaji” a duniya.
Kwanaki kadan bayan rantsar da shi, shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka, inda ya umurci dukkan hukumomin gwamnatin tarayya da su sanya dokar ta baci na tsawon kwanaki 90 kan taimakon ci gaban kasashen waje da kuma duba shirye-shiryen da ake da su.
“Manufar Amurka ita ce ba za a sake ba da wani taimakon kasashen waje ba ta hanyar da ba ta dace da manufofin ketare na sabon shugaban Amurka ba,”.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce an dakatar da duk wani tallafin kudade na shirye-shiryen ba da agajin kasashen waje ban da na manyan kawayenta a Gabas ta Tsakiya, wato Isra’ila da Masar.
Amma umurnin na ranar Juma’a ya kebance tallafin abinci na gaggawa da kuma abubuwan da ke da alaka.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen waje
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya.
Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan AmurkaDon haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa.
“Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne ga ƙasarmu,” in ji Gumi.
Sheikh Gumi, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kira Jakadan Amurka domin neman bayani da kuma a janye wannan barazanar, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi haka ba, to Najeriya ta yanke hulɗa da Amurka.
“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira Jakadan Amurka idan ba su janye barazanar ba, to mu yanke hulɗa da wannan gwamnati mara mutunci,” in ji shi.
Gumi, ya kuma jaddada cewa Najeriya tana da damar bunƙasa tattalin arziƙinta ba tare da dogaro da Amurka ba.
“Akwai hanyoyi da dama da za mu iya faɗaɗa tattalin arziƙinmu da ƙarfafa haɗin kan soji ba tare da dogaro da su ba,” in ji Gumi.