Ɗan Abacha ya kare mahaifinsa bayan ƙaddamar da littafin IBB
Published: 22nd, February 2025 GMT
Sadiq S. Abacha, ɗan Tsohon Shugaban Mulkin Soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana mahaifinsa s matsayin mutum mai nagarta duk da sukar da ake yi masa har yanzu.
A wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Sadiq, ya ce an jima ana cin amanar mahaifinsa, amma tarihi zai yanke masa hukunci ta hanyar yin adalci.
“Mutumin nan Abacha—kullum sukarsa da cin amanarsa kuke yi a asirce. Tarihi zai tuna ka a matsayin shugaba nagari, ko da kuwa sun ci gaba da ƙoƙarin rage maka ƙima.
“A matsayina na ɗanka, yau na fi alfahari da kai. Lallai kai ne mutumin da suke so sun zama ko da rabinka ne kuwa,” in ji shi.
Ya kammala rubutunsa da karin maganar Hausawa: “Duk wanda ya yi jifa a kasuwa…”
Rubutun nasa ya zo ne kwanaki kaɗan bayan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya ƙaddamar da littafinsa.
Littafin ya jawo cece-kuce sosai, musamman kan soke zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993.
A cikin littafin, Babangida ya tabbatar da cewar MKO Abiola ne ya lashe zaɓen, amma ya ce wasu a cikin gwamnatinsa, musamman Abacha, suka tilasta masa soke sakamakon zaɓen.
Janar Sani Abacha ya mulki Najeriya daga 1993 zuwa lokacin rasuwarsa a 1998.
Wasu na yaba wa mulkinsa saboda gyaran tattalin arziƙi da tsaro, yayin da wasu ke sukarsa bisa cin hanci da take hakkin ɗan Adam.
A gefe guda kuma, Gumsu Abacha, ɗaya daga cikin ’ya’yan marigayin, ta mayar martani game da littafin da IBB ya ƙaddamar.
A wani saƙo gajere da ta wallafa a shafin X (Twitter), wanda ke kama da habaici.
Haka kuma, ta sake wallafa wasu rubuce-rubuce da ke cewa Babangida ya zargi Abacha da laifuka ne domin ba shi da ikon kare kansa.
Ga hotunan a ƙasa:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ya ya Kare Mahaifi
এছাড়াও পড়ুন:
Kare Ya Ciji Tsohon Ɗan Wasan Barcelona A Mazakuta
Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata.
Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya ji ciwo mai tsanani a wajen. An garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa a Panorama inda aka ɗinke masa raunin da ƙwayoyin da suka kai guda shida.
Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro Diaz Ba Na Sayarwa Bane – Liverpool Ta Fadawa BarcelonaƘungiyar ƙwallon ƙafa ta Aris FC, wacce ta karɓi Perez aro daga Celta Vigo, ta tabbatar da cewa ya samu “cizon da ya haddasa kumburin naman wajen,” kuma hakan ya sa ba zai buga wasan UEFA Conference League da za su kara da Araz-Nakhchivan ranar Alhamis ba.
Kocin ƙungiyar, Marinos Ouzounidis, ya bayyana cewa an tsara Perez zai fara wasan kafin lamarin ya faru. “Carles zai kasance cikin ƴan wasa 11 na farko da zasu fara fafatawa” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp