Aminiya:
2025-09-18@05:40:54 GMT

Sojoji sun ƙwato tarin makamai a Zamfara

Published: 28th, January 2025 GMT

Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun ce sun ƙwato tarin makamai a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda na Jihar Zamfara.

Dakarun tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (DSS), sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya.

Tankar mai ta sake fashewa a Neja Jadawalin Gasar AFCON 2025 da za a fafata a Morocco

Wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce sun ƙaddamar da farmaki ranar 27 ga watan Janairun 2025, abin da ya kai ga ƙwato makaman kan hanyar Namoda zuwa Zurmi.

Ya ce waɗanda ake zargin sun tsere zuwa cikin daji tare da barin motarsu bayan artabu da sojoji.

Kanal Abubakar ya ce bayan binciken da suka yi a cikin motar, sun gano makamai da dama da suka haɗa da bindigar AK-47 guda tara da harsasai daban-daban.

A ɗaya gefen, dakarun sun ce sun baza koma domin cafke ƙasurgumin ɗan bindigar nan Bello Turji wanda ake nema ruwa a-jallo.

Bayanai sun ce Turji na ci gaba da guje-guje da sojoji daga maɓoya zuwa maɓoya.

Dakarun sun tabbatar da cewa suna aiki tuƙuru domin kama Turji da zummar dawo da zaman lafiya a al’ummomin da suka addaba da hare-hare.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: dakaru Jihar Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m
  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff