Zaɓe, Tsari Ne Kawai Na Ci Gaba Da Riƙe Madafun Iko Ba Dimokuraɗiyya Ba – Jega
Published: 26th, February 2025 GMT
Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa tasirin dimokuradiyya a Afirka ta Yamma na raguwa saboda rashin shugabanci nagari. Da yake jawabi a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a wani taro mai taken, “Mahanga kan makomar zabe a Afirka ta yamma”, wanda wata kungiyar al’umma ta ‘Yiaga Africa’ ta shirya, ya danganta komowar juyin mulkin soji a yankin da rashin shugabanci nagari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga
Bayo Onanuga, Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu ne kawai saboda ya fito daga Kudancin Najeriya.
Yayin wata hira da Trust Radio, Onanuga ya ce maganar cewa ana yi wa Arewacin Najeriya wariya ba gaskiya ba ce, face tsantsar siyasa kawai.
Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin TarayyaYa ce ƙorafin da Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta yi na cewa an yi watsi da Arewa wajen naɗe-naɗen muƙaman gwamnati da ayyukan ci gaba, wata dabara ce kawai don rage ƙimar shugabancin wanda ya fito daga Kudu.
Ya shawarci ’yan siyasar Arewa da su yi haƙuri, kamar yadda ɓangare Kudu ya yi lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya shugabanci ƙasar har na tsawon shekaru takwas.
“Shugaba Tinubu ɗan Najeriya ne kamar kowa. Ya cancanci yin shekaru takwas a kan mulki kamar yadda Buhari ya yi. Ka da mu lalata ƙasa saboda son zuciya,” in ji Onanuga.
Dangane da zargin cewa an fi bai wa ’yan Kudu muƙamai, Onanuga ya ce masu sukar Tinubu su kawo hujjoji da ƙididdiga maimakon su ci gaba da yin zargin da ba shi da tushe.
Ya ƙara da cewa babu wani yanki da ba shi da matsalar hanyoyi ko ayyukan da ba a kammala gama ba, amma ya ce gwamnatin yanzu na ƙoƙarin gyara abubuwan da ta gada.
“Kafin ku zargi gwamnati, sai ku binciki gaskiyar lamarin. Wannan duk siyasa ce kawai don a raina Shugaban Ƙasa,” in ji shi.
Onanuga, ya kuma kare matakin da Tinubu ke ɗauka wajen inganta tsaro.
Ya ce an samu ci gaba sosai, inda ya kafa misalin cewar dukkanin shugabannin tsaro daga yankin Arewa suka fito.
Ya ce yanzu yana iya yin tafiya daga Kaduna zuwa Abuja cikin kwanciyar hankali, tafiyar da a da ta ke da hatsari sosai.