Sojoji sun tarwatsa maɓoyar Bello Turjia Zamfara
Published: 10th, February 2025 GMT
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara.
Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro.
Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato.
Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska.
’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a KanoSojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan da ke ƙauyen Dakai.
Sojojin sun kona sansanin tare da ceto mata da ƙananan yara da ’yan bindigar suka tsere suka bari.
Sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK47 da bama-bamai da gurneti da ’yan bindigar suka tsere suka bari.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan
Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar.
A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai 6 sannan wasu 22 suka ji rauni.
Yankin Sistan Baluchistan dai ya dade yana fama da hare-hare na wannan kungiyar, kuma tana da sansani a cikin kasar Pakistan wacce take makobtaka da kasar a kudu maso gabacin kasar.