2025-11-03@07:12:29 GMT
إجمالي نتائج البحث: 391

«ya sayi kwafi»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kebbi, NUJ, ta taya gwamnatin jihar da al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar ranar Sallah.   Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar da Sakatare, Ismail Adebayo, ta yi murna da al’ummar musulmin jihar kan kammala azumin kwanaki 29 na watan Ramadan da kuma bikin Eid-Fitr.   Ta yi kira da a zauna lafiya da juna a tsakanin al’ummar jihar bisa koyarwar addinin Musulunci da manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da la’akari da muhimmancin watan Ramadan da Idi-El-Fitr.   Majalisar ta yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Nasir Idris kan kayayyakin abinci da aka rabawa musulmi a...
    A shekarar 2009 ne Cristiano Ronaldo ya saka hannu akan kwantiragin da ya sa ya zama sabon dan wasan Real Madrid, tun daga wancan lokacin Ronaldo ya jefa kwallaye 311 a wasanni 292 da ya bugawa Madrid, hakazalika ya lashe kofuna 15 a shekaru 9 da ya kwashe a Santiago, to amma yanzu Fionrentina Perez ya dauko wani Bafaranshe daga PSG, wanda yanzu haka ya dauko hanyar doke tarihin Ronaldo a Real Madrid. Kylian Mbappe ne ya jefa kwallaye 2 a wasan da Real Madrid ta doke Leganes, wanda hakan ya sa ta samu maki daya da abokiyar hamayyarta Barcelona dake saman teburin La Liga, kwallaye biyun da Mbappe ya ci ya sa kwallayen da Mbappe ya ci a kakar...
    Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira gudun tayar da hargitsi a Jihar Kano. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Gabanin yanzu dai, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da shi kansa Sarki Aminu sun ɗaura azama ta gudanar da haye-hayen sallah bana. Sai dai da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Kurawa...
    Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin He Yadong, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa, da doka da kuma mizanin kasa da kasa. He Yadong ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum, inda ya ce, a wannan lokaci da ake ciki, wasu manyan jami’an kamfanonin kasa da kasa na kawo ziyara kasar Sin. Kuma kamfanonin sun yi nuni da cewa, babbar kasuwa, da cikakken tsarin masana’antun samar da kayayyaki, da kuma karfin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Sin, dukkansu babbar dama ce a gare su, kuma zuba jari a Sin yana nufin cin gajiyar wannan dama. Bugu da kari,...
    Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bukukuwan Sallah na bana, saboda bukatar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar. A wata sanarwa da aka fitar, Sarkin ya bayyana takaicinsa kan matakin amma ya jaddada cewa, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne babban abin da ya sa a gaba. Sarkin ya ce, “Bisa umarnin da jama’a suka ba mu da kuma jajircewar da muka yi na ba su kariya, mun ga ya dace mu janye duk wani shiri da aka yi na bukukuwan Sallah bisa la’akari da halin da ake ciki.” Ya kara da cewa, tuntubar da aka yi da manyan malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki sun yi tasiri a...
    Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin  raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi...
    Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke arewaci da kuma kudancin yankin ruwan Iran yau Alhamis gabanin ranar Qudus ta duniya. Kwamandan rundunar sojojin ruwa na IRGC Rear Admiral Alireza Tangsiri ya ce jiragen ruwa masu nauyi da marasa nauyi 3,000 ne ke halartar faretin. Ya kara da cewa, faretin na da nufin nuna karfin ruwa na bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma isar da sako ga miyagu da azzalumar gwamnatin Isra’ila. A...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen duniya suka bai wa matatar. Duba daga  rahoton ma’aikatar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta Kpler, ta ce jiragen ruwa shida dauke da kusan ganga miliyan 1.7 na man jiragen sama daga matatar Dangote sun isa tashoshin jiragen ruwa na Amurka a wannan watan na Maris. Wani jirgin ruwa, Hafnia Andromeda, ana kyautata tsammanin zai isa tashar Everglades a ranar 29 ga Maris tare...
    A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa. Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya. Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Naɗinsa yana cikin ƙoƙarin gwamnatin Jihar Ribas na amfani da ƙwararru ‘yan jihar domin samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro. Farfesa Worika ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Okrika a Jihar Ribas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki  domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa ​​Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar jirgin kasa. Da yake yiwa magoya bayansa jawabi, Rasool ya ce, Abin da ya faru yana a matsayin wulakanta ku ne ku al’ummar Afirka ta kudu, amma kuma idan kuka tsaya tsayin daka kan manufofinku na ‘yancin kai to za ku ci gaba da rayuwa a cikin mutunci da daukaka. Ya ce ba laifi muka yi ba, ammam kuma mun dawo gida ba tare da...
    Wata mata mai suna Krystena Murray ’yar Amurka, wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne, ta fara ɗaukar matakin shari’a a kan wani asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IBF). Matar tana zargin asibitin da yi mata dashen ɗantayin da ba nata ba, bayan an tilasta ta, ta mayar wa asalin iyayen jaririn ɗansu. NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Krystena Murray, mazauniyar Jihar Georgia, ta ɗauki cikin ne bayan dashen ɗantayi na (IBF) da aka yi mata a asibitin masu neman haihuwa da ake kira Coastal Fertility Clinic,...
    A jiya Asabar 22 ga watan nan, jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng, ya amsa gayyatar halartar taro na 2 na tattaunawar sassan Sin da na Amurka game da batun tattalin arziki karkashin cibiyar Jimmy Carter, inda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.  A cikin jawabinsa, jakada Xie Feng ya ce ko kadan, hadin gwiwar Sin da Amurka bai taba zama na wani fanni ya ci riba dayan ya yi asara ba. Maimakon haka, kaso 41 bisa dari na kamfanonin Amurka dake kasar Sin na daukar Sin a matsayin kasa ta biyu a duniya, wajen samun ribar hada hadar kasuwanci. Dole Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Daina Barazana Ga Masu Sukar Ta – Amnesty An Kashe Askarawa 6 da...
    “Saboda haka, za a soke sunayen kadarorin da suka shafe sama da shekara goma ba a biya musu haraji ba nan take, Bugu da kari kuma, ana bayar da wa’adin kwanaki 21 ga masu rike da gidajen da ake rike da bashin kudin haraji na tsawon shekara daya zuwa goma, sannan kuma za a soke sunayensu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ‘Yar kasar ta Zimbabwe Kiristy Coventry ta zama mace ta farko daga fito daga nahiyar Afirka,kuma mace da za ta rike shugabannin hukumar wasannin Olympic. An zabi Kirsty  ‘yan shekaru 41 ne a yayin kada kuri’a ta sirri da aka yi da ‘yan takara 7 su ka yi gogayya. An yi zaben ne ne a yayin taron hukumar ta Olympic karo na 144, a birnin Costa, Navarino a kasar Greece a jiya 20 ga watan nan na Maris. Gabanin zabenta dai , Kirsty ta kasance wacce ta zama gwarzuwa ta iyo har sau biyu a wasannin Olympic. Za ta fara aikin nata ne na shugabancin hukumar wasannin Olympic  a ranar 23 ga watan Yuni, da za ta gaji Thomas Bach...
    Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a gudanar da bincike don gano abinda ya hadda hatsarin day a faru a kan gadar Karuk an titin Abuja Keffi a daren Labaran da ta gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da kuma jikatan wasu. Jaridar Premium Times ta nakalto shugaban kasar yana fadar haka tabakin mai bashi shawara kan al-amuran watsa labarai Bayo Onanuga a jiya Alhamis. Shugaban ya bayyana alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan murmurewar wadanda suka ji rauni. Ya kuma bukaci a gaggauta gudanar da bincike don sanin abinda ya haddasa hatsarin day a kai da wannan asarar, don daukar matakan hana aukuwar irinsa nan gaba.
    Shugaba Kaïs Saïed na Tunisiya ya kori firaministan kasar Kamel Madouri,  da aka nada a watan Agustan da ya gabata yayin wani gagarumin garanbawul a majalisar ministocin kasar a daren jiya Alhamis. Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce an maye gurbin firaministan kasar Madouri nan take inda aka maye gurbinsa da Sarra Zaafrani Zenzri, ministar kayan aiki. Sanarwar ta ce sauren mambobin gwamnatin zasu ci gaba da aikinsu. Garan bawul na shugaban kasar ta Tunisia a baya baya nan shi ne na ranar 6 ga watan Fabrairu inda ya sallami ministan kudinsa Sihem Boughdiri Nemsia da tsakar dare, tare da maye gurbinsa da alkalin kotun Michket Slama Khaldi.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma. Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan Ɗaya daga cikin matsalolin da masana suka gano shi ne sare itatuwa ba tare da dasa sabbi ba, wanda ke illa ga muhalli. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazarin illar sare itatuwa ba tare da...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kakaba haraji da sauran shingayen kasuwanci ba za su amfani kowa ba, kuma suna matukar haifar da illa ga samar da wadatar tattalin arzikin duniya, da tafiyar da shi cikin kwanciyar hankali.  Jami’ar wacce ta bayyana haka a yau Alhamis yayin wani taron manema labarai, ta ce kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga kasashen waje, da nuna goyon baya ga ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, da tsarin kasuwanci a tsakanin bangarori daban-daban, da karfafa samun moriyar kasa da kasa ta fuskar tattalin arzikin da ya hade kowa da kowa, da neman bunkasa ta bai-daya, tare da samar da moriyar juna da dukkan...
    Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙwace wani fili mallakar sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja. Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen kula da filaye na Abuja, Chijioke Nwankwoeze. Nwankwoeze ya ce an yanke hukuncin ƙwace filin ne sakamakon gazawar babbar jam’iyyar adawar na biyan kudin gini na shekara shekara. Wasiƙar ta ce PDP ta gaza biyan kuɗin tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2006 zuwa 1 ga watan Janairun 2025, duk da sanarwar da hukumar gudanarwar babban birni (FCTA) ta wallafa a jaridu da dama tun daga shekarar 2023 kan buƙatar biyan kuɗaɗen. Aminiya ta ruwaito cewa filin na Jamiyyar PDP na daga cikin filaye 4,700 da Ministan ya ƙwace a...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Litinin cewa, atisayen da sojojin kasar Sin suka yi a mashigin tekun Taiwan wani muhimmin martani ne ga goyon bayan da kasashen waje ke nunawa kan yunkurin neman “’yancin kan Taiwan,” kuma babban gargadi ne ga ‘yan awaren Taiwan. Kakakin ta ce, matakin soja da kasar Sin ta dauka ya wajaba, kuma yana bisa doka, ya kuma dace don kare ikon mallakar kasa, da tsaro da kuma cikakkun yankunanta. Mao ta bayyana hakan ne a lokacin da take ba da amsa ga tambayoyi a taron manema labarai na yau, inda ta ce, rahotanni sun nuna cewa, sojojin kasar Sin sun gudanar da atisayen soji a mashigin tekun Taiwan...
    Wasu manyan jami’an kasar Habasha sun bayyana cewa, layin dogon da ya sada tsakanin kasar Habasha da Djibouti da kasar Sin ta gina, yana kara inganta bangaren hada-hadar kayayyaki na kasar Habasha, kana ya zama wani muhimmin ginshiki da ke taimaka wa cinikayyar shigo da kaya da fitar da su zuwa kasashen waje a kasar. Jami’an sun bayyana hakan ne a wata ganawa da suka yi tare da masu ruwa da tsaki a harkar sufuri da shigo da kayayyaki da fitar da su waje na kasar Habasha, a ranar Asabar da ta gabata. Da yake jawabi a wajen taron, ministan sufuri da hada-hadar kayayyaki na kasar Habasha, Alemu Sime ya bayyana cewa, kasar da ke gabashin Afirka tana aiki tukuru...
    Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta fara atisayen tantance gwanintar harbi na shekarar 2025 daga ranar Litinin 17 zuwa 19 ga watan Maris a Barikin Yar Gaba da ke Dutse, Jihar Jigawa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya ta 26 Armoured Brigade, Laftanar Uzoma Egwu-Ukpai, ya sanyawa hannu aka kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse. Sanarwar ta bayyana cewa, atisayen tantance gwanintar harbi ana yi ne domin auna ƙwarewar jami’an soji wajen sarrafa makamai da ingancin harbinsu. Laftanar Uzoma Ukpai ya shawarci al’umma da kada su firgita yayin atisayen idan suka ga sojoji suna kai-komo ko suka ji karar harbi, musamman mutanen da ke zaune...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci. Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai domin tabbatar da kyakkyawan makoma ga ƙasar. Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu “Tsawon shekaru 50, Najeriya na kashe kuɗin ’ya’yanmu wajen samar da man fetur ga maƙwabtan ƙasashe. Dole ce ta sa muka tsara makomar yaranmu,” in ji shi. Shugaban ya amince da cewa ana fuskantar ƙalubale...
    Cikin kasa da wata guda, an yi asarar hannayen jari da darajarsu ta kai dala triliyan 4, inda damuwar da duniya ke da shi kan manufofin haraji na Amurka ke haifar da fargaba a kasuwar hannayen jari ta kasar. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin jama’ar duniya masu amfani da intanet ya nuna cewa, mutane na bayyana shakku kan manufofin haraji na sabuwar gwamnatin Amurka, kuma sun damu ainun da mummunan tasirinta kan kasuwar hannayen jari ta kasar dake tafiyar hawainiya. Wani mai bayar da amsa cikin nazarin ya kuma bayyana cewa, sanya haraji kan dukkan kayayyakin kasashen wajen, bai taba haifar da da mai ido ba. A baya bayan nan, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa,...
    Minisyan yaki na HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sojojin HKI za su ci gaba da zama a kasar Siriya har zuwa illa masha allah, don kare yahudawan da suke zaunwa a tuddan Golan na kasar Siriya da suka mamaye a yakin kwanaki 6 a shekara ta 1967. Tashar talabijin ta Presstv TV ta nakalto ministan yakin ya na fadar haka a jiya Talata, a lokacinda ya kai ziyara kan ‘Jabal Sheikh’ wani tsauni mai muhimmanci a fagen tsaro, wanda sojojin HKI suka mamaye bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad da yan kwanaki. Da kuma bayan da Abu Mohammed al-Julani  shuga kungiyar Deash ya shiga fadar gwamnati a Damascus. Jabal sheikh dai yana da tsawo sosai ta yadda ana iya kallon...
    Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka. Sai dai shugaban bai san sauye-sauyen da kasashen Afirka suka samu ba, wadanda tun tuni suka daina dogaro da kasashen yammacin duniya. A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da...
    Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki huɗu. Wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Litinin a Abuja, ta ce mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3. Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar. Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Neja da Kwara da...
    Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan gagarumin atisayen sojojin ruwa tsakanin manya-manyan kasashen guda uku zai sami halattan wasu kasashe da dama a matsayin masu kallo. Labarin ya kara da cewa manya-manyan jami’an sojojin ruwa na sojojin Iran da kuma na dakarun IRGC ne suka tarbi jiragen ruwan yaki na wadannan kasashe. Sannan ana saran wakilai daga kasashen Azerbaijan, Iraki, Kazakhstan, Oman, Pakistan, Qatar, Afirka ta Kudu, Sri Lanka da Haddiyar...
    Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da fara atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran, wanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar  ta kasar Iran. Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa, kasashen Sin, Rasha da Iran sun fara atisayen jiragen ruwa na hadin gwiwa daga tashar ruwan Chabahar ta Iran ne domin karfafa hadin gwiwa na tsaro tsakanin wadannan kasashe guda uku. Kwanaki biyu da suka gabata, Beijing ta mayar da martani ga kalaman sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth na cewa kasarsa a shirye take domin shiga kowane irin yaki, kuma idan muna son dakile Sinawa ko wasu, dole ne...
    A yammacin ranar Alhamis da ta gabata ce sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka aukawa Falasdinawa masu ibada bayan sun gudanar da sallar tarawihi a masallacin Al-aqsa, inda suka kore su daga masallacin da karfi, tare da hana su yin I’itikafi a cikin masallacin. Da yake tsokaci a cibiyar yada labaran Falasdinu, Ziad Abhais, mai bincike kan al’amuran birnin Kudus, ya jaddada cewa, matakin da gwamnatin sahyoniyawa ta dauka na hana masu ibadar I’itikafi a cikin masallacin Al-Aqsa wani mataki ne na cin zarafi da kuma muzgunawa hakkokinsu na addini. Ya kara da cewa: Sojojin yahudawan sahyoniya suna amfani da hakan ne don shimfida ikonsu a kan masallacin Al-Aqsa, domin kuwa a shekara ta 2015 an ba da izinin yin I’itikafi...
    Rikicin ya fara ne tun bayan tsige Obasa a ranar 13 ga Janairu, 2025, a matsayin shugaban majalisar. ‘Yan majalisa 33 a zaman da aka yi a wannan rana suka tsige Obasa tare da ayyana tsohowar mataimakiyar shugaban majalisar, Merand a matsayin shugaban majalisar dokokin Jihar Legas. Ko da yake ’yan majalisar sun yi nuni da cewa yana cin zarafin mukami da karkatar da kudade da kuma rashin da’a a matsayin wani bangare na dalilan tsige Obasa, matakin ya nuna asalin rikicin da ya barke a majalisar ta 10 a jihar. ‘Yan majalisar dai sun tsige Obasa ne a lokacin da yake kasar Amurka. Bayan dawowarsa Legas a ranar 25 ga Janairu, 2025, ya kalubalanci cire shi. Duk da tsoma...
    A cikin abubuwan da aka tattauna a taron, a cikin kananan hukumomi 774, Jihar Delta ce kadai mai kananan hukumomi 25, suka mika bayanan asusunsu domin biyansu kai tsaye. “Kawo yanzu kananan hukumomin Jihar Delta ne kawai suka bayar da bayanan asusunsu. “Duk da haka, ana ci gaba da tuntubar babban lauyan gwamnatin tarayya game da yadda ake gabatar da asusun.” Da take maida jawabi kan kalubalen, Madein ta ce an tsara tsarin da za a aiwatar, amma kalubalen farko shi ne na tantance shugabannin kananan hukumomin da tsarin mulki ya zaba. Ta bayyana cewa wannan matakin ya kasance mara tabbas. “Bugu da kari, ga wadanda ke da zababben shugabanci, akwai alaman tambaya cewa wasu hanyoyin za a bi don...
    A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...
    A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...
    “A kan batun kafafen yada labarai, muna son mu yi taka-tsan-tsan don kada mu wuce gona da iri. Al’amari ne da ke cikin Majalisar Dattawa, kuma yin hakan ta hanyar kafafen yada labarai na iya daukar mana hankali. Zauren kwamitin zai iya ɗaukar mutane da yawa, kwamitin yana da mambobi kusan 23 ko 24. Muna son mu mai da hankali kan lamarin da ke gabanmu, kada wani lamari ya dauke mana hankali.”   Ya ba da tabbacin cewa za a yi wa Sanata Akpoti-Uduaghan adalci, inda ya ce: “Mai girma Sanata Natasha na da gata kamar kowane Sanata, kuma za a kare gatanta. Za ta samu adalci a wannan al’amari matukar ina wannan mukami. Kawata ce, kuma ba wanda zai...
    Sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar, ta bayyana cewa saɓani ne ya shiga tsakanin matashin da mahaifiyarsa, wanda ya haifar da tashin hankalin. Majiyoyi daga unguwar sun ce matashin yana shaye-shaye, kuma mahaifiyarsa ta faɗa masa ya daina, wanda hakan ne ya fusata shi. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    A ranar 28 ga watan Fabarairun da ya shude ne aka saki wani fim din kasar Sin mai lakabin “Creation of the Gods II: Demon Force”, a gidajen kallon sinima 39 dake sassan tarayyar Najeriya, da kuma wasu 2 dake kasar Ghana, da sinima 1 a Laberiya. Wannan ne dai karon farko da aka saki wani fim da aka shirya a kasar Sin kai tsaye, a allunan sinima na kasashen yammacin Afirka. Kuma a cewar wani manajan gidan sinima dake Abuja, fadar mulkin Najeriya, duk da kasancewar fim din shi ne na farko da ya shiga gidajen kallon na kasuwanci a birnin, jigon labarin ya samu karbuwa matuka tsakanin masu kallo. Ya ce shigar fina-finan Sin kasuwar gidajen kallo a...
    Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombia sun jaddada aniyarsu ta hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila amfani da tashar jiragen ruwansu, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi a zirin Gaza. “Za mu hana jiragen ruwa da ke dauke da kayan aikin soji zuwa Isra’ila amfani da tashoshin jiragen ruwanmu; kamar yadda,” Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, Firayim Ministan Malaysia Anwar Ibrahim da Shugaban Colombia Gustavo Petro suka rubuta a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da mujallar harkokin waje ta buga a wannan makon. Sun jaddada cewa yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ya fallasa gazawar tsarin kasa da kasa, tare da yin...
    “A karkashin Shugabancin Dantsoho, ya taimaka wajen ganin ana sauke sundukan kayan da aka yo jigilarsu a cikin sauki, musamman a Tashar Lekki wanda hakan ya taimaka, wajen rage cunkso a Tashar.” A cewar Mahukuntan Mullar. Mahukuntan Mullar sun kara da cewa, sun zabo Dantso ne, ganin cewa, shi ne, na farko da aka zaba a mukamin Shugaba na Kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya PMAWCA, inda zabarsa, ta kara daga kima da darajar Nijeriya, a fannin harkokin tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa, a yankin. A yayin da yake karbar babbar lambar yabon Mullar Dakta Dantsoho ya bayar da tabbacin cewa, zai kara zage damtse wajen shugabantar Hukumar, daidai da tsare-tsaren Miniatan bunkasa...
      Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsaya a matsayin wakilin na angwaye yayin da Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo Janar Muhammad Iliyasu Bashar murabus ne ya tsaya a matsayin wakilin na amaren.   Gwamna Nasir Idris, yayin da yake godewa uwargidansa Hajiya Nafisa Nasir Idris bisa wannan shiri a karkashin gidauniyarta ta “Asusun NANAS ”, ya yi alkawarin bayar da goyon baya da kuma ci gaba da gudanar da shirin na shekara-shekara domin amfanin al’ummar Kebbi, ya kuma shawarci ma’auratan da su kasance masu adalci da mutunta ra’ayin juna.   Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku-Bagudu, ya bayyana taron a matsayin tunatarwa ga daidaikun mutane...
    Gwamnatin Jihar Kano, ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗauki mataki na cire Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, daga Fadar Nassarawa, wanda ta ce zamansa na haddasa tashin hankali a jihar. Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne, ya yi wannan kira. Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Fadar Gwamnatin Kano yayin rabon kayan tallafi da ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tarauni, Hon. Kabiru Dahiru Sule, ya bayar. Ya zargi wasu mutane na amfani da zaman Aminu Ado a fadar Nasarawa don cimma muradun kansu da kuma haddasa rikici a Kano. “Muna kira ga...
    A kokarin da take yi na magance kalubalen muhalli da inganta ayyukan sarrafa sharar gida mai dorewa, gwamnatin jihar ta hana zubar da shara a filin titin kotu.   Wannan shawarar na da nufin hana yaduwar cututtuka da kuma kare lafiya da amincin mazauna da masu wucewa.   A yayin ziyarar da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Dr. Dahiru Muhammad Hashim ya kai wurin ya bayyana damuwarsa kan illar muhalli da kiwon lafiya daga zubar da shara.   Ya jaddada kudirin gwamnati na samar da ingantattun dabarun sarrafa shara don kare lafiyar jama’a da muhalli.   Dokta Hashim ya ba da umarnin kwashe sharar da suka taru a yankin, sannan ya shawarci mazauna yankin da su rika zubar...
      Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano irin muhimmiyar gudunmuwar da kungiyoyin hadaka ke takawa wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban al’umma, da kuma karfafa jama’a a kasar.   Karamin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin horo na musamman ga shugabanni, kwamitocin gudanarwa, da manajoji na kungiyoyin hadaka a Najeriya, wanda aka shirya a Kaduna.   A cewar Kungiyar Hadaka ta Duniya (International Cooperative Alliance), sama da kashi 12% na al’ummar duniya suna cikin daya daga cikin kungiyoyin hadaka miliyan 3 a duniya.   Kungiyoyin hadaka suna nada muhimmiyar gudunmuwa wajen bunkasa tattalin arziki mai dorewa, inda suke samar da ayyukan yi da damammaki ga mutane miliyan 280, wanda...
    Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta batun cewa Majalisar Tarayya ce ta ƙi tabbatar da shi domin zama Minista a shekarar 2023. El-Rufai ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba shi muƙamin duk da sun ƙulla yarjejeniya a kan hakan. Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina Ana iya tuna cewa, a watan Agustan 2023 ne Majalisar Dattawa ta ƙi tabbatar da El-Rufai a matsayin Minista, inda ta bayyana dalilai da suka shafi tsaron ƙasa da Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta ba da shawara. Sai dai a hirarsa da gidan Talabijin na Arise a ranar Litinin, El-Rufai ya ce...
    Ma’aikatar kula da muhallin halittu ta kasar Sin ta gudanar da taron manema labarai a yau Litinin 24 ga wata, inda wani jami’inta ya nuna cewa, ingancin iska da muhallin kasar sun kyautatu a shekarar da ta gabata, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin ta cimma burin magance gurbatar yanayi a shekara ta 2024. Jami’in ya kara da cewa, a shekara ta 2024, yawan kwanakin da aka samu kyakkyawan ingancin iska ya kai kaso 87.2%, adadin da ya karu da kaso 1.7% idan aka kwatanta da na shekara ta 2023. Kazalika, yawan kwanakin da aka samu mummunar gurbatar yanayi ko fiye da haka, ya kai kaso 0.9%, adadin da ya ragu da kaso 0.7%. A Beijing, wato fadar mulkin...
    Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi. A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya, sannan za a bai wa kwararren manomi guda hamsin wanda zai koyar da su dubarun kiwo. Tun da farko da take jawabi, kwaminisiyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta bayyana wannan tallafi a matsayin wata gagarumar gudummawa da gwamnati za ta bunkasa harkokin mata ta hanyar dogoro da kai. A cewarta, taimakon da Gwamna Radda ya bayar ko shakka babu zai amfani...
    “Jajircewar sa ga haɓaka ababen more rayuwa, noma da ƙarfafa matasa yana ci gaba da mayar da Jihar Neja abin koyi wajen cigaba da wadata.”   Ministan ya ce yana taya gwamnan na jihar su murna, yana mai bayyana shi a matsayin jagora mai kishin hidimta wa al’umma da cigaban ƙasa.   Idris ya ƙara da cewa, “Yayin da yake bikin wannan rana ta musamman, ina taya shi murna a matsayin jagora wanda jajircewar sa ga hidima da shugabanci ke nuna ainihin cigaba.   “Ina roƙon Allah ya ci gaba da ba shi lafiya, hikima da ƙarfi don ya ci gaba da tafiyar da Jihar Neja zuwa matakai mafi girma.”   Ya kammala da taya Gwamna Bago murna, inda ya...
    Mai martaba Mai Pataskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya jagoranci bikin buɗe sabon masallacin Juma’a da aka gina a Garin Danga a Ƙaramar Hukumar Potiskum da ke Jihar Yobe. Bikin kaddamar da sabon masallacin Juma’ar, wanda ya jawo shugabannin al’umma, malaman addini, da mazauna yankin ya nuna irin gagarumin ci gaba da aka samu a harkokin addinin musulunci a yankin. Mai Pataskum, wanda ya yi fice wajen bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin, ya yaba da kokarin da masu bayar da tallafi na kasar Malaysia suka yi na gina masallacin, tare da jaddada rawar da yake takawa wajen samar da haɗin kai da ci gaban yankinbmasarautar. Mai martaba Sarkin ya yi...
    Dauda ya kara da cewa, babu wata waka da zai yi ba tare da an bukaci ya yi ta don isar da wani sako ba. Haka zalika, Shugaba Tinubu, ba shi da wani buri na tara dukiya a halin yanzu; illa kawai dai fatan barin tarihi mai kyau a matsayinsa na Shugaban kasa, kamar yadda sauran mazan jiya; irin su Sir Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa suka bari. Dangane da abin da wasu ke dauka cewa, ana biyana makudan kudade; don yin wakokin da za su kawar da hankalin mutane, su sani cewa; na fi mayar da hankali a kan noma fiye da yadda nake yi wa harkar waka, dalili kuwa; ni manomi ne wanda a yanzu haka duk...
    Sojojin kasa na jumhuriyar Musulunci ta Iran sun hada guiwa da sojojin ruwa don atisayen hadin guiwa wanda suka sanyawa suna Zulfikar 1403. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakain atisayen Brigadier General Alireza Sheikh yqana cewa a cikin wannan atisayen suna son gwada aiki tare da sojojin masu aiki a sama da na ruwa don samar da yanayi irin na yanayi yaki da gaske don fahintar da harkokin yaki suke tafiya. General Alireza Sheikh yace a bangare na farko na wannan atisayen mun gwada yadda jiragen yakin masu saukar ungulu zasu sauka su tashi a dai dai lokacinda ake cikin budewa juna wuta da makiya. Sannan manufar atisayen gaba daya itace samar da yanayi ta yadda...
    A jiya Jumma’a ce aka kammala taron kungiyar kasashen G20 a birnin johanasboug na kasar Afrika ta Kudu, kuma inda batun yake-yake a yankunan daban-daban na duniya ne suka mamaye taron. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yakin Ukraine da Rasha Hamas da HKI, Congo da sauransu ne suka mamaye taron inda ministocin harkokin wajen kasashen na G20 suka tattauna a kansu. Ministan harkokin wajen na kasar Afrika ta Kudu Ronal Ramola ya bayyana cewa duk tare da cewa babu wani babban jami’an gwamnatin kasar Amurka a taron amma taron ya gudana kamar yadda ake saba. Kungiyar G20 Taron kasashe masu arziki a duniya, wadanda suke da kasha 85% na  tattalin arziki a duniya sannan suna...
    Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
    Arziƙin hamshakin attajirin nan ɗan jahar Kano Alhaji Aliko Dangote ya ninka na bara inda ya ƙaru zuwa dala biliyan 23.9, wanda hakan yasa ya cigaba da kasancewa mutumin da yafi kowa dukiya a nahiyar Afrika kuma ya koma matsayi na 86 a jadawalin masu kudin Duniya kamar yadda mujallar Forbes mai ƙididdiga akan masu kuɗin Duniya ta fitar, Forbes ta zaɓi Aliko Dangote a matsayin mutum na 144 mafi arziƙi a duniya a shekarar 2024 da dala biliyan 13.4. Forbes ta yi kiyasin cewa dukiyar Dangote ta kai dala biliyan 23.9, musamman saboda hannun jarin sa na kashi 92.3 na matatar man dangote, Aliko Dangote mai shekaru 67, ya sake zama ɗaya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya,...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran juyin juya halin musulunci ya fadar cewa a halin yanzu babu wani abunda HKI zata yi a gaza sai idan kungiyoyi masu gwagwarmaya suna sun abin ya faru, saboda kekkyawar riko da suka yiwa yankin. Imam Seyyed Ali Khamenei, ya yabawa kungiyoyin falasdinawa kan hadin kai da suka nuna a yankin da ya gabata. Ziyad al-Nakhalah, babban sakataren kungiyar Jihad Islami,   ya bayyana cewa sun...
    Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
    Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Zhang Xiaogang ya fitar da sanarwa kan batutuwan da suka shafi aikin soja a baya-bayan nan. Ya ce, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin. Kuma babu wata tsokana da sojojin Amurka za su yi da za ta iya canza wannan lamari, sabanin haka, za ta iya nuna munafuncin da Amurka ta dade ta na yi ga al’ummomin duniya, kuma za ta iya kara karfafa niyyar jama’ar kasar Sin ta kare ikon kasa da cimma cikakkiyar dunkulewar yankunan kasar baki daya. Game da zarge-zarge marasa tushe da sabon ministan tsaron Amurka ya yi kan Sin, Zhang Xiaogang ya ce, Sin na adawa sosai da hakan. Kuma jama’ar kasar Sin na son zaman lafiya....
    Yau Alhamis, ma’aikatar kula da kasuwanci ta Sin ta sanar cewa, tun bayan kaddamar da bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, manyan ayyukan da suka shafi bikin sun sa yawan kudin da aka kashe ta intanet da kuma a zahiri ya zarce yuan biliyan 1.6. An ba da rahoton cewa, bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, wanda ma’aikatar kula da kasuwanci, da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da kuma gwamnatin birnin Beijing suka shirya tare, tun daga ranar 7 ga watan Janairu, ya sa kananan hukumomi daban daban da kuma dandamalin kasuwanci ta intanet sun mayar da hankali kan lokacin bikin bazara, kuma sun kaddamar da ayyuka fiye da 100 don...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin lamba, yana mai jaddada cewa; Kasarsa ba ta neman yaki da wata kasa, sai dai tana kokarin karfafa dangantakar abokantaka da kasashen makwabta. Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai lardin Bushahar inda ya gana da al’umma tare da jinjinawa sadaukarwar shahidai musamman shahidan wannan lardin, a daidai lokacin da ake cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci,...
    Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
    Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Nijeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ‘ƴan ƙasa. Kamfanin sadarwa na MTN ya fara amfani da sabon tsarin ƙarin kudin awanni kaɗan bayan da majalisar wakilai ta kasa ta bukaci gwamnati da ta dakatar da ƙarin.
    Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga wayewar garin jiya Litinin ne, al’umma sun fito kan manyan hanyoyi kasa a jihohi kasar tamkar kwararan kogi don gudanar da murnar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, tare da tabbatar da aniyarsu ta yi riko da manufofin juyin juya halin na Musulunci da kuma sabunta mubaya’arsu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.
    Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar. Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin. Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku...
    Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da...
    Siyasar tsananata matsin lamba kan Iran ta gaza cimma buri kuma hana fitar da man da Iran ke fitarwa mafarki ne da ba zai tabbata ba Ministan mai na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana matsayar matsin lamba da Amurka ke yi kan fitar da man kasar Iran a matsayin siyasa ta nuna gazawa, yana mai cewa: Hana fitar da man fetur din Jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa wajen kasar, mafarki ne da ba zai taba wanzuwa ba. Ministan mai na Iran Mohsen Paknejad a matsayin mayar da martani ga furucin Trump ta sake dawo da tsananta siyasar matsin lamba da nufin gurgunta harkar tattalin arzikin Iran ta hanyar hana ta fitar da man fetur, a jiya Lahadi ya bayyana...
    Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai. Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988),...
    An bude atisayen soja kan teku bisa hadin gwiwar wasu kasashe a birnin Karachi na kasar Pakistan, a ranar 7 ga wata. Asitayen sojan da kasar Pakistan ta tsara ya samu halartar jiragen ruwan soja daga kasashe sama da guda 10, wadanda suka hada da Sin, da Indonesiya, da Japan, da Italiya, da Malasiya, da kuma Amurka da dai sauransu. Haka kuma, sauran kasashe sama da guda 40 sun tura masu sa ido wajen atisayen. An raba atisayen sojan zuwa matakai guda biyu. Mataki na farko shi ne tsakanin ranaku 7 zuwa 9 ga watan Fabrairu, inda za a yi atisayen soja kan tashar jiragen ruwa, da tattaunawa kan atisayen, da tattaunawa kan ayyukan musamman tsakanin bangarori daban daban da...
    Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
      Yadda ake amfani da shi: Za ku dinga shafa zumar a gabanku, ku barta na tsawon mintuna 30, sai ku wanke da ruwan dumi, sannan ku shafa Man Zaitun. Za ku dinga yin haka safe da  yamma kafin kwanciya. Sannan ku dinga dafa ‘ya’yan hulba na tsawon mintuna 10 da ruwan da bai wuce kofi daya ba, sai ku dora shi a wuta ya dan tafasa bayan kun sauke shi sai ku tsiyaye shi sai ku sa masa zuma cokali uku, za ki yi wannan hadin shima safe da yamma.   Sai kuma maganin kurajen da kaikayin gaba: Kai tsaye ana cewa sanyin mara shi ne yake jawo wannan matsala, amma abin da ya kamata mu sani shi ne...
    Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.” Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka...
    Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba. Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Yadda bom din Boko Haram ya kashe mutane a hanyar kasuwa a Adamawa Aƙalla masallata 10 da suka haɗa da Limamin ne aka ce an yi awan gaba da su a yayin harin. Jaridar Punch ta ruwaito DSP Ahmed Rufa’i, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a....
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama.   A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin iyalan mutanen uku da suka rasu.   Ya kuma ba da umarnin a gaggauta biyan kudaden jinya ga duk wadanda suka jikkata tare da samar da kayan abinci don tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa.   A cikin nuna jin kai, gwamnan ya bayyana shirin gina sabon masallacin Juma’a a Rimin Zakara a matsayin sadaqatu jariya (dauwamammiyar...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya rattaba hannu a kan doka wacce ta yi allawadai da kutun kasa da kasa ta ICC saboda laifin fidda sammacin kama abokiyar Amurka firai ministan HKI da ta yi, sanadiyyar kissan kiyashin da ya yi a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump ya na fadar haka a lokacinda yake rattaba hannu a kan dokar tasa a jiya Alhamis. Ya kuma kara da cewa kotun da ke birnin huqae ta wuce huruminta a lokacinda ta cutar kawar Amurka HKI tare da fidda sammacin kama shi. A ranar tarlatan da ta gabata ce Benyamin Natanyahu ya tattauna da shugaban Trump wanda yayi masa alkawula da dama, daga cikin har da  kwace...
    Biyo bayan nasarar da suka yi akan Alavés a ƙarshen mako, Barcelona za ta dawo taka leda a yau Alhamis don ƙarawa da Valencia a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey a filin wasa na Estádio de Mestalla dake Valencia. Barcelona na cigaba da jan zarenta a wannan shekarar ta 2025, inda ta buga wasanni da dama ba tare da tayi rashin nasara ba tun bayan shigowar sabuwar shekara, kuma daya daga cikin mafi kyawun sakamakon da ta samu ya zuwa yanzu a bana shi ne wanda ta doke Valencia da ci 7-1 kwanaki 10 da suka gabata. Har Yanzu Arsenal Ta Na Iya Lashe Gasar Firimiya Ta Bana – Alan Shearer Ba...
    Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a zaman lafiya da hakuri a tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara sakamakon rikicin filaye da ya barke tsakanin al’umma da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).   Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin hajji.   Da yake jawabi ga al’ummar yankin, Sarkin ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka jikkata cikin gaggawa.   “Dole ne mu yi wa wadanda suka rasu addu’a da kuma baiwa iyalansu ikon jure wannan rashi, Allah ya sa wannan ya zama na karshe a cikin irin wannan mummunan lamari a cikin al’ummarmu,” inji...
    Saka sunan Taye Taiwo a cikin jerin zakakuran yan wasan kungiyar ya nuna yadda dan wasan ya nuna bajinta da kuma yadda ita kanta kungiyar ta Marseille ta yaba da irin kokarin da ya yi a baya.
    Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 “Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan...
    A yayin da rikici ya kaure cikin dare tsakanin jami’an tsaro da masu gine-gine a unguwar Rimin Zakara, mutane sun cinna wa gidan mai garin wuta. Da farko dai an samu rikici tsakanin mahukunta da mutanen yankin, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane huɗu tare da ƙone gidan mai unguwar. NCDC ta tsaurara matakan shige da fice a Nijeriya saboda fargabar Ebola EU ta yaba wa Gwamna Zulum kan farfaɗo da Jihar Borno Aƙalla wasu mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon ƙazamin rikicin da ya hautsine tsakanin mahukunta da mazauna unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano. Bayanai sun ce an harbe mutanen huɗu ne yayin da suka fito tirjiya...
    Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta cafke wasu matasa a yankin Sheka bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, yana mai cewa rikicin ya fara ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Aminu, ɗan unguwar Sheka Babban Layi, wanda ake zargi da aikata fashi da sauran laifuka. Dabaru Irin Na Sin A Kan Daidaita Harkokin Duniya A 2024 An Yi Taro Don Tattauna Dabarar Aiwatar Da Shawarar Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya A MDD Rahotanni sun nuna cewa marigayin mamba ne na ƙungiyar ‘Yan Shida,’ wacce ta addabi yankin Sheka da aikata fashi da tashin hankali. Wasu mazauna unguwar sun kama shi, suka kakkarya masa ƙafa tare da...
    Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909.   Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14.   Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001).   Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56.   Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949).   Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960).   Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021).   Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
    Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance a matsayi na daya na wucin gadi a kasuwar fina-finan duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
    Wani uba a ƙasar Pakistan ya kashe ɗiyarsa matashiya bayan ta saka wasu faifan bidiyo da ya ɗauka a matsayin waɗanda ba su dace ba a manhajar sada zumunta ta TikTok, in ji ‘yan sanda a ranar Alhamis. Shugaban ‘yan sandan yankin, Babar Baloch, ya ce mutumin wanda aka ce yana da shekara 50 a duniya, ya dawo da iyalansa daga ƙasar Amurka kwanan nan, domin su zauna a birnin Ƙuetta da ke Kudu maso Yammacin Pakistan. Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Jirage sun yi karo a sararin samaniya a Amurka Mahaifin, wanda yanzu haka yake tsare, ya amsa laifin harbe ’yarsa a farkon wannan makon bayan ta ƙi sanya suturar da ta dace kuma ta daina...
    An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar. Tun a jiya Laraba ce, shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Ahmed al-Sharaa (al-Jolani) ya gabatar da jawabi na samun nasara bayan ganawa da shugabannin bangarorin soja a birnin Damascus fadar mulkin kasar, a gaban dandazon bangarori da dakarun Siriya. A yayin jawabinsa na nasara, Al-Sharaa ya ce: A yau kasar Siriya tana bukata abubuwa fiye da kowane lokaci, yana cewa, kamar yadda suka kuduri aniyar ‘yantar da kasar a baya, wajibi...
    Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron gaggawa game da batun Kongo(Kinshasa) da kwamitin sulhu ya kira jiya Talata cewa, a halin yanzu, yankin gabashin Kongo(Kinshasa) yana cikin yanayi mai hadari. Ya ce Sin na goyon bayan mambobin kwamitin sulhu su hada kai tare da daukar kwararan matakai, ta yadda za a samar da dabarun hana yanayin ya ci gaba da tsanani da kuma inganta warware batun a siyasance. Fu Cong ya bayyana cewa, kwanan nan, yanayin Kongo(Kinshasa) ya shiga matsanancin yanayi ciki sauri, inda kungiyar M23 ta kai hari birnin Goma, hedkwatar jihar Kivu ta arewa dake kasar, lamarin da ya sanya fararen hula da yawa barin gidajensu, inda kuma hadarin barkewar rikici...
    Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga  Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.  Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20  da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
    Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
    Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila. Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar. Hakan ya kai United matsayi na 13 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 26. Ga jerin rashin ƙoƙarin ƙungiyar a shekarun baya: Bayan da Brighton ta yi nasara a kan United a Old Trafford, karo na shida ke nan da aka doke ƙungiyar a gida a wasa na 12 tun bayan 1893/94. United ta ƙare a ƙarshen teburi, lamarin da ya kai ga ta bar buga gasar ta...
    Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka. An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
    Hukumar kula da gandun daji na Hadejia ta ce wuraren shakatawa na kasa suna taka rawar gani ta fuskar kiyaye halittu, da magance matsalolin sauyin yanayi, da inganta bincike, da ci gaba, gami da samar da ayyukan yi a Najeriya. Mukaddashin jami’in kula da gandun dajin, Mista Jonah Moses ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar neman shawarwari ofishin wayar da kan jama’a na kasa da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa. Ya nanata cewa al’umma za su kara fahimtar fa’idojin irin wadannan wurare ne kadai idan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa NOA, ta taimaka wajen fadakarwa ko ilmantar da jama’a. Jonah Moses ya bayyana cewa, sun kawo ziyarar ce domin ganawa da masu ruwa...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.