Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo.

Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere.

Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka.

An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni a shekarar 2024, matakin da ya bayyana cewa, al’adun bikin na kara yaduwa zuwa duk fadin duniya zuwa wani sabon matsayi.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jagora Ya Bada Umurnin A Gudanar Bincike Mai Zurfi A Fashewar Tashar Jiragen Ruwa Na Shaheed Rajae

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana bada umurni ga ma’aikatar shari’aa a kasar ta gudanar da cikekken bincike don sanin abinda ya faru saboda daukar matakan da suka dace don hana irin wannan sake faruwa nan gaba, sannan idan akwai wadanda suka yi kuskure a hukunta su.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gobarar da ta taso a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajae, daya daga cikin tashoshin jirage masu muhimmanci  a tattalin arzikin kasar, don haka dole ne a kara daukar matakan tsaro da amincin tashar don hana irin wannan sake faruwa.

Sanadiyyar wannan hatsarin majalisar dokokin kasar ta shelanta makoki a duk fadin kasar a yau Litinin. Sannan shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan ya ziyarci tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae don ganewa idanunsa abubuwan da suka faru da kuma barnan da aka tabka.

Ya zuwa yanzun wadanda suka rasa rayukansu sun kai 40 sannan wadanda suka rasa rayukansu sun kai dubu guda.  

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis
  • Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
  • Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka
  • Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
  • Katafaren Jirgin Daukar Jiragen Yaki Na Kasar Amurka Harry Truman Zai Fice Daga Tekun Maliya
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
  • Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine
  • Jagora Ya Bada Umurnin A Gudanar Bincike Mai Zurfi A Fashewar Tashar Jiragen Ruwa Na Shaheed Rajae