Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba ni muƙamin Minista — El-Rufai
Published: 25th, February 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta batun cewa Majalisar Tarayya ce ta ƙi tabbatar da shi domin zama Minista a shekarar 2023.
El-Rufai ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba shi muƙamin duk da sun ƙulla yarjejeniya a kan hakan.
Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke KatsinaAna iya tuna cewa, a watan Agustan 2023 ne Majalisar Dattawa ta ƙi tabbatar da El-Rufai a matsayin Minista, inda ta bayyana dalilai da suka shafi tsaron ƙasa da Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta ba da shawara.
Sai dai a hirarsa da gidan Talabijin na Arise a ranar Litinin, El-Rufai ya ce duk ba wannan ba ne face Shugaba Tinubu ne ya sauya shawara kan ba shi muƙamin.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ne ya sauya masa akalar ƙudirinsa bayan shafe shekaru takwas a matsayin Gwamnan Kaduna.
“Bayan shafe shekaru takwas a matsayin Gwamnan Kaduna, ina da wasu burace-burace da na ƙudirta amma Tinubu ya nemi na bayar da gudunmawa a gwamnatinsa.
“Bayan haka ne muka ƙulla yarjejeniyar da sharaɗin cewa zai ba ni muƙamin Minista, amma daga bisani ya sauya shawara.
“Saboda haka a daina yarda da cewa Majalisar Tarayya ce ta ƙi tabbatar da ni saboda ba haka abun yake ba.
“Shugaban ƙasar ne kawai ba ya buƙata ta a gwamnatinsa saboda ya sauya shawara amma ko ma dai mene ne ba abin da ya dame ni ba ne,” in ji El-Rufai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tinubu ne ya sauya
এছাড়াও পড়ুন:
Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura IsaTrump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.
“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”
Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.
“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.