Trump Ya Bayyana Ra’ayin Tura Falasdinawan Gaza Zuwa Masar Ko Jordan
Published: 26th, January 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza.
Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya.
Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Amnesty International Ta Kafa Hujja Kan Ta’asar’Yan Sahayoniyya A Gaza
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya take aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, kai tsaye duniya na gani ta hanyar tauraron dan Adama.
A yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty kan kare hakkin bil’adama a duniya Agnes Callamard, sakatariyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, duniya ke kallon yadda ake aiwatar da kisan kare dangi kai tsaye a tauraron dan Adam a Zirin Gaza.
Ta kara da cewa, “Sun ga kasashe kamar babu abin da zasu iya saboda da rauni” tare da nuna cewa “gwamnatin mamayar Isra’ila na kashe dubban Falasdinawa maza da mata, ta hanyar kisan kiyashi kan dukkanin iyalai da suka hada da kananan yara, da lalata gidaje, rusa cibiyoyin tsare rayuka, rusa asibitoci da cibiyoyin ilimi.