Yadda Za Ku Magance Kaikayin Gaba
Published: 8th, February 2025 GMT
Yadda ake amfani da shi:
Za ku dinga shafa zumar a gabanku, ku barta na tsawon mintuna 30, sai ku wanke da ruwan dumi, sannan ku shafa Man Zaitun. Za ku dinga yin haka safe da yamma kafin kwanciya.
Sannan ku dinga dafa ‘ya’yan hulba na tsawon mintuna 10 da ruwan da bai wuce kofi daya ba, sai ku dora shi a wuta ya dan tafasa bayan kun sauke shi sai ku tsiyaye shi sai ku sa masa zuma cokali uku, za ki yi wannan hadin shima safe da yamma.
Sai kuma maganin kurajen da kaikayin gaba:
Kai tsaye ana cewa sanyin mara shi ne yake jawo wannan matsala, amma abin da ya kamata mu sani shi ne ba iya shi kadai yake jawowa ba akwai abubuwa da dama.
Akwai abubuwa da yawa da ke haifar da wannan matsala, bayan kamuwa da cuta da akan ce yana haifar da wannan matsalar, akwai wasu abubuwa a bayansa.
Wani lokacin sanya kaya ko ‘Underwear’ wanda ya matse ka yana jawo kaikai wani kuma motsa jiki ko tafiya mai nisa a kafa ko gudu suna jawo masa wannan.
Akwai karancin tsafta, mutum ya rika sanya ‘Underwear’ kusan mako guda ba tare da an canza shi ba, wasu kuma ba sa barinsu su bushe bayan sun yi wanka sannan su sanya tufafi, duk suna haifar da wannan matsala.
Koda gaban dadewa yake yana saba yana wari in sha Allah idan akai wannan za’a samu waraka
Abubuwan da ake bukata:
Man Darbejiya, Man tafarnuwa, Man zogale, Man kwakwa:
Yadda ake hadawa:
Da farko za ku samu kowanne daga cikinsu, amma ku tabbata kun samu na asali masu kyau saboda biyan bukata, kuma kowanne yana samuwa a Islamic chemist.
Idan kuka saya kowanne, ku auna shi da murfin kwalbar.
Sai a hada su waje daya a shafa a wurin da kurajen ya bayyana ga namiji, idan ya takura sai a bar shi, sai a yi wanka a bar shi ya bushe, sai a shafa wannan maganin a wurin sannan a sa tufafi, sai a yi kokarin canza rigar a kowane kwana 2.
Idan mace tana da kuraje ko kamuwa da cuta na dogon lokaci ko kamuwa da cuta, sai ta samu auduga ta shafa mai a jikinta idan ta kwanta ta danna gabanta kuma a sha ruwan dumi, a guji shan ruwan sanyi. Allah ya sa mu dace.
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar.
A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta IAEA kamar yadda yarjeniyar NPT take bukata da kuma dokokin kasa da kasa.
Abbas ya fada masa inda aka kai ya zuwa yanzu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, a biranen Mascat na kasar Omman da kuma Roma na kasar Italiya.
Ya zuwa yanzu dai kasashen biyu sun gudanar da taro har sau uku dangane da shirin Nukliyar kasar ta Iran, kuma bangarorin biyu sun bayyana amincewarsu da yadda tattaunawar take tafiya.