Rundunar Sojin Najeriya Za Ta Fara Atisayen Koyon Harbi A ‘Yar Gaba Da Ke Dutse
Published: 16th, March 2025 GMT
Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta fara atisayen tantance gwanintar harbi na shekarar 2025 daga ranar Litinin 17 zuwa 19 ga watan Maris a Barikin Yar Gaba da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya ta 26 Armoured Brigade, Laftanar Uzoma Egwu-Ukpai, ya sanyawa hannu aka kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse.
Sanarwar ta bayyana cewa, atisayen tantance gwanintar harbi ana yi ne domin auna ƙwarewar jami’an soji wajen sarrafa makamai da ingancin harbinsu.
Laftanar Uzoma Ukpai ya shawarci al’umma da kada su firgita yayin atisayen idan suka ga sojoji suna kai-komo ko suka ji karar harbi, musamman mutanen da ke zaune a yankin Yargaba.
Haka kuma, Mataimakin Daraktan ya umarci manoma da mafarauta da ke kusa da wurin atisayen da su guji yankunansu na noma da farauta a lokacin atisayen.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Harbi Jigawa Rundunar Soji
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya
Kalli yadda aka karɓi ’yan Najeriya guda 203 da aka dawo da su daga ƙasar Libya.
(Hoto: Onyekachukwu Obi).